Sashe 8
Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin gidan gwamna". **** Washegari Amina da kwarin gwiwarta ta doshi ofishin (consultant) dinta Dr. Usman Turaki. Sai dai kash! Ofishin Turaki a kulle. Wani masinja ke gaya mata ai Dr. Turaki an ba shi kwamishinan lafiya ya bar asibitin, shi da asibiti sai nan da shekaru hudu. Allah ya so tana da lambar wayarsa, a lokacin waya ta fara cika duniya. Duk wani babban ma'aikaci yana da ita. Ta kira shi akan ya kwatanta mata sabon ofishinsa sai ya ce zai turo direba ya kai ta yanzun nan. A wata ni'imtacciyar mota da Amina ba ta taba shiga irinta ba aka kai ta (Ministry of health) inda ofis din kwamishina Turaki yake. Amina ba ta bi dogon layin da ake bi wajen ganin kwamishinan ba, kai tsaye aka sadar da ita gare shi. Amina ta shiga da sallama cikin nutsuwarta ta halitta, Dr. Turaki ya amsa, tareda nuna mata wajen zama. Ta gaishe shi, ta kuma yi masa murnar sabuwar kujerarsa. Ya yi godiya sannan ya tambaye ta ta yi shawarar? Iyayenta sun amince? Amina ta ce, "Goggo ta amince, amma a bisa sharadin in miji ya zo kafin lokacin kwangilar ya cika zan bar aikin in yi aure". Dr. Turaki ya yi murmushi mai kama da dariya, yadda tayi maganar ne ya bashi dariya kamar auta kamar kuma yar fari, "That's good". Yace da ita. Wani tunani ya darsu a zuciyarsa a kan Ma'arouf da Amina, amma da ya tuna halin mutumin nasa sai ya yi gaggawar goge tunanin daga zuciyarsa ya janyo na abin da ya tara su. "Ki yi parking yau, duk da mai girma gwamna ya gaya min ba kya bukatar daukar komai, amma mutum ba ya rasa abin amfaninsa. Kayan sanyawa ne ba kya bukatarsu, yau za a maido takwararki gidan daga kauyen Ji-kas. Don Allah Amina ki kula da ita yadda ya kamata. As a doctor na san ba kya bukatar a tuna miki yadda za ki yi da (patient) dinki. But wannan patient din need extra more....saboda marainiya ce. Sannan lafiyarta matters a lot to her Dad. Zai nutsu ne kadai wajen aikin al'ummarsa in ya tabbatar Amina tana a kyakkyawan hannu kuma tana cikin koshin lafiya koda bata taka kasa da kafafuwanta. Daga yau zan bar zama jakada a tsakaninku, kai tsaye za ki dinga magana da His Excellency in kuna bukatar wani abu ko sanar da shi wani abu na ci gaba ko akasin haka da ya danganci lafiyar diyarsa. Be the best doctor and best physiotherapist as we know. Kawo wayarki in sanya miki lambar tasa... Amina ta miqa masa, ya sanya ta yi 'saving'. A ranta ta san ta karba ne kawai amma ba za ta taba iya kiran Ma'arouf Ji-kas ba! Wani kwayan mutum guda daya da ko sunansa bata taba kwatanta fada ko da a zuciyarta ba, shi din dai, (Turakin), za ta ci gaba da baiwa jakadancin ko yana so ko ba ya so. A sanyaye ta ce, "Sunan yarinyar AMINA?" Dr. Usman ya amsa, "Eh, AMINA 'yar AMINA koh?" Duk suka yi murmushi, "Allah ya ba ta lafiya". Ya amsa, "Ameen alfarmar Annabi. Allah kuma ya sa ta hannunki za ta samu lafiyar. Ina addu'ar tukwicin hakan ya zamo naki ne Dr. Amina". Ta yi murmushi. Har gida direban ya kawo ta, ya kuma ce in ta gama shiryawa gobe ta kira shi, shi zai zo ya shigar da ita gidan Gwamnati. **** Amina ta shiga gida da sallama, ta tadda Goggo da Ilya suna aikin nasu na kirga ciniki. Talatu mai aikin Goggo ta karbi katuwar jakar hannunta, wadda duka littattafai ne a ciki da farar rigarta ta likitoci sakale a hannunta na hagu. Ilya ya yi mata sannu da zuwa cikin karramawa don shi fa yanzu Amina ta zama uwardakinsa, tunda albarkacinta ya tabbata watarana sai ya ga Ji-kas ido da ido, sai ya taka kafarsa cikin gidansa ko da sunan kai wa Dr. Amina sako ne. Yana rokon Allah ya cika masa wannan burin. Ta zauna ta na fadin "Wash, na gaji wallahi". Goggo ta ce, "Ai shi aikin sa-kai haka yake". Ilya ya yi magana cikin muryar rashin jin dadi. "Goggo, yaushe za ki daina yabawa Amina magana mara dadi ne a duk sanda ta fada miki wani abu da ya shafi aikinta? Mijin nan fa ba ita ta hana kanta ba, Allah ne bai kawo ba. Shi auren ina ce lokaci ne? Koda a da Amina ta hana kanta aure ni shaida ne akan cewa banda yanzu. Mazan ne suka ga bazasu iya da ita ba, Allah zai kawo mata daidai ita ki daina ganin laifinta. Don Allah Goggo ki dinga tausasa kalamanki gare ta". Goggo tana mamakin soyayyar da Ilya ke yi wa Ma'arouf Habibou Ji-kas, alhalin shi bai sanshi ba, shi ma bai sanshi ba. Bai san yana yi ba. Ga shi har ta shafi Amina. Ta lura tun ranar da aka yi zancen aikin Amina a gidan Ji-kas ta fahimci Ilya wani girma da kulawa yake baiwa Amina na musamman, a da kuwa ai kusan kullum sai an raba su fada, ta kuma san ba don ya ba shi komai ba ne, fisabilillahi yake kaunarsa, irin kauna ta talaka ga wasu tsirarun shuwagabanninsu nagari. Ta nisa, ta dubi Aminar da idon rahma. "Sannu, ki je ki kwanta ki huta, akwai farfesun kaza da gurasa da muka yi na zuba miki cikin flask dinki in kin tashi ci". Amina ta ce, "To Goggo". Ta wuce su, Ilya ya ji dadi har ransa. Da daddare Amina na tsitstsince abubuwan amfaninta, ta gaya wa Goggo gobe ne tafiyar, direba zai zo ya dauke ta. Goggo Hauwa ta ji wata irin kewar Amina tazo ta lullube ta kamar garin za su raba bakidaya, koko shekara za ta yi ba ta ganta ba. Amma ta daure ba ta bari Amina ta gane ba, don ta san halinta sai ta ce ta fasa. Ta taya ta harhada wasu abubuwan nata, ta zuge a jaka. Amina ke ba ta labari suna aikin wai an ce kada ta dauki kayan sanyawa. Goggo ta ce, "Dauki abinki, idan kuma wando da yar riga zasu baki fa? Kwashi zannuwanki kinji na gaya miki Amina ta yi dariya, tana nunke zannuwan tana jerawa a jaka ta ce, "Goben da Ilya za mu tafi ya ga waje, ko ya ji dadi". Goggo bata ko amsa ba, ita kadai tasan me take ji a zuciyar nan tata mai cike taf! Da kewar Amina. **** GOVERNMENT HOUSE BAUCHI Tun yammacin jiya Akilu direban Ma'arouf na Bauchi ya dauko Hajiya Saude da jikanyarta Amina daga kauyen Ji-kas zuwa gidan gwamnati. Zuwan Hajiya na farko kenan tun bayan tarewarsu. Tun daga bakin gate ganin irin tsaron da gidan ke da shi da irin rundunar sojojin da suke wucewa kafin su shiga ciki, Hajiya Saude ta rika tasbihi a zuciyarta tsigar jikinta na tashi, in ta tuna wai duka don kare lafiyar danta kwaya daya suke wannan zaman. Da aka shiga da su falo na farko, wanda daga shi za su bi har su tadda sassan masu gidan Hajiya Saude kasa daure farin cikinta ta yi sai da ta yi hawaye, ta share da habar zaninta. Tana ganin gidan Ma'arouf na Fati Mu'azu karshen daular duniya, ashe gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta. Tafiya kamar ba za ta kare ba, har dai suka iso bangaren Laila. Tana hakimce cikin kujerar kasaita tana waya. Ta ci ado har ta gaji, ta dace kwarai da a kira ta matar gwamna, don ko can baya ita kyakkyawa ce ma abociyar ado, balle yanzu da ta ke kan kololuwar ni'imar rayuwa. Shigowar Hajiya da Amina, Akilu na turo ta cikin wheel chair dinta bai sa ta katse hirar da ta ke yi a waya ba, ci gaba ta yi har tana kyakyala dariya, ta dai yi wa Hajiya nuni da kujerar zama da hannunta, nufinta ta zauna, ita kuma ta ci gaba da hira da kawarta, tana gaya mata at last ya yarda ya amince da kafa 'Family Support Programme' din, sauransu fidda tsare-tsare su wawaso miliyoyi na tashin hankali. Hajiya ba ta sa wa hirarta kunne ba, sai dan tabuwa da zuciyarta ta yi ganin irin karbar wasarere da Laila ta yi musu. Ko kallon Amina ba ta yi ba har Hajiya ta fiddo ta daga wheel chair, tayi kici-kici ta kwantar da ita a kujera bacci ya dauke ta. Ta zauna ta yi tagumi tana jiranta ta gama. Sai da Laila ta kwashe minti talatin tana hira, sannan suka yi sallama ta ajiye wayarta a gefe. Ta dubi Hajiya tana dariya. "A'ah mutanen Ji-kas ne, sai yau? Har mun so mu yi fushi tunda muka tare ba ku zo ba". Hajiya ta yi murmushi fuskarta ta dan canza, da gani zuciyarta an taba ta. "To ga mu nan dai sai yau Allah ya nufa. Masha Allahu da sabon muhalli, Allah ya sanya albarka". "Amin-amin Hajiya, bari a kawo muku abinci, wanne iri ku ke so?" Mamaki yana kara shigar Hajiya, ta ce, "Kin ganmu nan a koshe muke. Har a cikin mota mun yo guzurin abinci. Nuna min bayan gida dai in yi alwala, in yi wa Aminatu wanka". Laila ko a jikinta, ta danna kararrawa wani ma'aikaci ya shigo sanye da (uniform) dinsu na ma'aikata, ya tsuguna gaban Laila. "Mukullin dakin saukar baki na farko yana hannunka ne?" "A'ah, yana hannun Amos shi ke kula da bangaren saukar baki". "To ku je da Hajiya da shi Amos din ya bude muku ka shigar da kayansu". Laila na kallon Hajiya tana ciccibar Amina da ke bacci, tana kici-kicin sanya ta a wheel chair kamar za ta fadi sabida jikin girma da nauyin yarinyar. Amma ko ta motsa daga inda ta ke zaune balle ta taimaka mata. Ma'aikacin ya kama 'wheel chair' din zai tura, Hajiya ta dakatar da shi. "Barshi ni zan tura". Sai ya dauko mata jakar kayanta ya shiga gaba suka bi shi a baya. Bangaren saukar bakin daga can wajen ginin da Laila ta ke ne. Tsararrunapartments ne iri daya sun fi guda hamsin. Amma in aka kwatanta shi da ginin da Laila ta ke ciki kamar gida ne da baskwatansa. Ma'aikacin ya yi wa Hajiya sallama ta fita, bayan