Sashe 15
Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yau bata gama iyakance su ba. Da murya irin ta wanda yayi laifi ya kuma yarda daga baya yayi laifin ya amshi laifin nasa, yana so yayi repenting in za a bashi dama tace. Ga tattabarun Amina na kawo as promised . Ta nuna kejin dake kan mudubi da dan alinta. Sai ya manta da fushin nasa kuma sosai ta bashi dariya amma ya dake. Ya karasa ga kejin da sauri ya durkusa yana kallon kyawawan tantabarun yana murmushi with admiration, sai kuma ya bude kejin ya fito da aure daya farare kal da dabbare dabbaren baki kadan a jikin su ya dora a cinyar sa yana shafa bayan su a hankali, abun mamaki basu tashi ba, Amina ta cire fukafikin tashin kafin ta dauko su. Yace. Beautiful, Amina ta gode. Amma ba a tukunya ake kiwon su ba? Eh, a tukunya ne, na sa a kejin ne don inji saukin daukowa, sai a nemi tukunyar a sanya su . Ya maida su kejin ya dauka ya fita, yana fadin. Yau dinnan kuwa. Mu wuni lafiya. Little Ameena stay blessed! Daddy luv you much! Ameena karama tayi murmushi ta daga masa hannunta mai lafiyar. Bata yi magana ba. Don dama maganar jefi-jefi take yinta. Amma tana jin komai tana kuma fahimta. **** Haka Dr. Amina ta ci gaba da aiki a gidan gwamnati har tsayin watanni biyar. Ba ta taba karbar albashinta ba, saboda bai kara yi mata zancen account number ba. Ita kuma bata taba damuwa ba, a yadda zuciyarta ke son Amina Ma arouf ji takeyi kamar kyauta take yi mata wannan aikin sadakatul jariya ta manta da wani abu wai . Mu amalarsu itada Ubangidanta mai wuyar fassarawa ce saboda kowannensu halinsa mai tsauri ne. Abinda za a iya cewa shine, tsakanin Ma arouf da Amina babu shakuwa babu sakewa da juna amma kuma babu gaba ko daurewa juna fuska. Wato mu amalar ta tsaya a iya ginshikin ta (lafiyar Amina) bayan wannan babu wata, sai ganin mutuncin juna da girmama juna. Saboda kowannensu ya tsaya matsayin sa ya kuma rike mutuncin nasa. Wata rana da daddare bayan sun ci abincin dare, Amina tace Aunty kunna min T.V . Amina ta tashi ta jona talbijin din, ta murdo mata cartoon din da kullum shi take kallo (Tom&Jerry). Amma sai little Ameena ta girgiza kai aunty yau mutane masu rai zaki budo min . Amina tayi dariya Tom da Jerry ba masu rai bane yau ta dauki remote ta murdo mata (Bauchi State Television). Cikin sa a a lokacin an nuno Baban ta, inda ake nuna sababbin ayyukan sa na wannan watan dana watan da ya gabata. Na farko purifying ruwan sha da yayi a jihar, da kara habaka hanyoyin gudun sa ta yadda ya isa ga kowanne sako da kowanne lungu na cikin birnin Bauchi (capital city), sai sabunta tourist attractions na jihar musamman Yankari Game Reserve , anyi sababbin motels da suits a cikinta, an sabunta ko ina an kara kula da dabbobin ciki, abincinsu da lafiyarsu, an karawa ma aikatan na Yankari albashi. A cikin gari kuma, gashi an nuno shi yana bude sababbin shatale-tale (round-abouts) da gadoji (flyovers) na sama dana kasa da ya gina don rage cunkoson motoci da ababen hawa a cikin gari, an kara wa asibitocin gwamnati albashi, an samar da magunguna masu kyau kyauta ga marasa lafiya al ummar jihar ta Bauchi. Amina tayi dan yi gajeren tsaki mtsw! Ta dora kafarta daya kan daya ta cigaba da kallo. Haka kawai taji ayyukan ko daya basu yi mata ba, basu burge ta ba! A ganinta akwai gyara a cikin ayyukan da administration din ke aiwatarwa. Amina karama na ta murna tana gaya mata. Daddy na ne, Aunty Daddy na ne fa ko baki gane shi bane? Amina ta tura baki gaba kafin tace na gane shi mana Amina tace to ban ga kina murna ba tayi dariya tace to ina murna Ameena gashi nayi dariya...... Suna haka yayi sallama tareda knocking ya dakata yana jiran su bashi umarnin shigowa. Lokacin sa ne na yin sallamar dare da little dinsa. Saida Amina ta bada izni ta hanyar cewa sannan ya murdo kofar ya shigo. Yau cikin wata irin shiga yake da Amina bata taba ganinsa da ita ba, wato shudin wandon jeans da yar top ja mai farin rubutun hilfiger. Kullum cikin babban riga da yar ciki da wando yake, wani lokacin kufta da wando na shadda ko yadi mai laushi da tsada (kaftan), bata taba ganin shi cikin wata shiga bayan wadannan ba sai yau. Sai ya zame mata yaro matashi dan shekaru talatin da daya ba magidanci Engnr. Ma arouf Ji-kas ba. Sai ta ga yayi mata wani irin kyau. Da ta kalle shi sai da ta sake maimaitawa abinda bata taba yi ba, amma tayi hanzarin dauke idonta kafin ya ankara da ta yi masa kallo na biyu. Ya zauna kusa da little, ya dauki kanta ya dora bisa cinyar sa. Yace Dear Ameena, kallo ake yi ne haka? Ta ce cikin yar siririyar muryarta Daddy kai muke kallo yace koh? Let me join you my princess, me ake yi a TVn? Ta ce an ce Yankari Game Reserve...... His Excellency Ma arouf Ji-kas.....! Ya kyalkyale da dariya ya rike hannunta cikin nashi sai kuma me? Ta yi dan tunani sannan tace Daddy na manta sauran yace Auntin ki ta tuna miki, kin ga ni ban gani ba gara ku bani labari Ta kai idonta ga Dr. Ameena aunty sai ma me aka yi? Ameena dake sauraron su amma idonta na kan TV, ba tareda ta juyo ba take magana. Aikin duk na cikin birni ne Ameena (maraya) wanda ake kira urbanization (raya maraya). Ki gayawa Daddyn ki inada gyara in zai bani minti goma cikin muhimmin lokacinsa Amina little ta maida kallonta ga mahaifinta. Daddy ka bata minti goma Ya nutsu sosai idonsa akan Dr. Ameena. Yace da little. Amina, Na bawa Doctor (100 minutes)! Dr. Amina taji dadin abinda yace. Ta juyo sosai daga fuskantar allon talbijin suka fuskanci juna, yana gefen gado ne da kan Amina akan cinyarsa, yayin da ita tana can gefe akan resting chair , kafarta daya bisa daya da remote control din talbijin a hannunta, sanye take da doguwar riga ruwan gwaiduwar kwai (beige colour) kirar Bahrain ta yi rolling da mayafin akanta da carbi a hannunta, da wuya ka ganta babu mayafi a wannan gidan sai ko a gidan Goggonta. Ganin irin nutsuwar da yayi yana sauraron ta itama ta zama serious ta soma magana cikin matsanancin ladabi. Da alama baka yi rayuwar karkara ba Mai girma Gwamna. Koko ince, Special Adviser for Rural Development din ka bashi da idea. Kauyukanmu sun fi maraya bukatu nesa ba kusa ba, amma kunfi mayar da hankali ga urbanization . Kananan hukumominmu tun daga Itass, Ganjuwa, Shira, Tafawa Balewa, Ningi, Toro, Katagum, Misau, Darazo, Jama are, Warji, Dass, Dambam da sauran wadanda ban ambata ba babu wadatar ruwan famfo sai na rijiyoyin burtsatse, babu tituna masu kyau, babu wadatar malaman makarantun firamare da sakandire sai a makarantun cikin birni, babu wadatar wutar lantarki, babu wadatar likitoci da malaman jinya a asibitocin su. Babu hannun gwamnati (tallafi) cikin sana in da sukeyi duk kokari ne na kai da kai kawai a tsakaninsu. Ba yau na fara bibiyar ayyukan administration dinka ba, sau tari ina budo (BATV) da Bauchi TV ina gani. Maganar gaskiya Your Excellency, gwamnatin ka tafi bada karfi ga raya maraya wai kara wa mai karfi karfi, kauyukanmu dake karkashin kananan hukumomi kuwa ko oho! Basu san ana yi ba wai kunu a makota! Da gama fadin hakan ta ja bakinta tayi shiru, ta maida duban ta ga talbijin, anyi sa a kuwa a daidai lokacin an nuno ya je bude wani estate da ya gina don bada haya ga ma aikata akan hanyar fita garin Bauchi. Amina ta juyo ta dube shi ta nuna t.vn da dan alinta ta ce you see.....? Ga mamakin ta har zuwa lokacin sauraron ta yake da attention da dan murmushi akan fuskarsa. Ko zantukunta sun masa ciwo fuskarsa bata nuna hakan ba. Da tace hakan, sai shima ya kai duban sa ga t.vn sannan ya dauke kai yana cigaba da murmushi. Sai a lokacin ya samu yin magana don kare kansa da yarda da wasu kalubalen nata. Sana i na kokarin taimakon kai da kai ko na gado a kauyuka dole ne Amina, ba dole saida taimakon gwamnati ba. Bazai yiwu ace gwamnati ta karade al ummar jihar ta bakidaya ta iya baiwa kowa dake jihar sana a ita kadai ba, dole sai da kokarin sana i na taimakon kai da kai al umma zatayi surviving. Don haka ki cire wannan daga lissafi. Sauran abubuwan da kika zano duk suna kan hanya kuma nagode da wannan kyakkyawan tunasarwa taki. Insha Allahu zaki ga chanji Ya mike ya nufi kofa yana fadin na barku lafiya, mu kwana lafiya, Allah ya tashe mu lafiya Amina tace Amin . Ta bi bayansa ta rufo kofar da mukulli kamar yadda ta saba ta dawo ta kashe wuta da kayan kallo suka kwanta. Sati biyu bayan wannan maganar da suka yi, Amina ta samu labari a bakin Ilya an sauke kwamishinan kananan hukumomi an nada sabo, an sauke mai bada shawara kan cigaban karkara an nada sabo. Idan ta murdo (BATV) ko (Bauchi TV) babu abinda take gani sai ayyukan cigaban karkara da kananan hukumomi sak! Wadanda ta ambata. Sosai taji dadi a ranta. She feel honoured! Jin dadin cewa ita mutum ce mai daraja da martabar data isa ta baiwa gwamna shawara ya dauka. Saidai bata ji dadin sauke wadannan masu mukaman ba, data yi masa maganar, yace da ita, ba akan abinda suka tattauna bane, ya kama su ne da almundahana, domin ya fidda wasu zunzurutun kudi ya basu domin inganta wutar lantarki da gyaran kwalbati a kananan hukumomi da kauyukan dake karkashinsu gabadaya ya bincika ya kuma je da kansa ya tarar ko daya basu yi ba. Kudi kuma babu su sama ko kasa. A sannan ne Ameena ta samu kwanciyar hankali domin bazata so ta zama sanadin hanyar abincin wani ba. ***** A karo na biyu, ya samu lokaci ya sake yin magana da likita Amina.