Sashe 2
Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zaren (silver) wanda ya kayatar da shaddar sosai. Da kafafunsu suke tafe suna hira har gidan Dagaci, wanda ya karbe su hannu bibbiyu, ya shigar da su turakar da yake saukar bakinsa. Ma arouf ya gaishe shi cike da ladabi ya amsa cike da kauna, ya rike hannunsa cikin nashi yana fadin, "Sai ka yi hakuri da ita fa, duk cikin 'ya'yana ita ce mai giggiwa". Abin ya ba wa Liman dariya, ya ya kai da aka zo neman auren 'yarka ka ke fadar halinta mara kyau? Shi kam maigari iyakar gaskiyarsa ya ke fadi, don kaunar da yake wa Ma arouf ba tun yau ba bazata bari ya yaudare shi ba. Engnr. Ma'aruf Ji-kas, yana so ya tambayi Maigari, "Giggiwa wace iri?" Amma ba zai iya ba, saboda karamcin dattijon. Ko dago kai ya kasa saboda tsabar girmama manya. Maigari da Liman suka fita kofar gida, suka dasa hira bayan Maigari ya shiga gida da kansa ya yi kiran Laila. Laila ta yi dauri ya kai sau goma tana warwarewa, ta sa kaya ya yi sau takwas tana canzawa. Ta fesa turare ya yi kala biyar, amma har yanzu ba ta ji tana kamshi ba. Uwarta na kara zuga ta. "Ta ina zai ganki ya ce ba ki yi ba? Ai karyarsa ta sha karya". A can falon bakin Maigari, Ma arouf ya fara kosawa. Har ya fara duban agogo. Ba ya son jira a rayuwarsa. Ko wanne minti daya mai amfani ne a wurinsa. Rayuwarshi a kayyade ta ke cikin tsara lokaci, minti goma sha biyar ya tsara zai yi tare da ita, ga shi ta ci minti talatin ba ta ma fito ba. Ya dan ja tsuka, ya murza zoben tsari na azurfa da ke hannunsa, wanda Baba Habibu ya sanya masa da jimawa, don a cewarsa rayuwa irin tashi sai da neman tsarin jiki. Yana son zoben don a kowanne lokaci yana tuna masa da Baban, ya kira shi a waya ya ji lafiyarsa, ko ya zo ya ganshi, ko ya aika a dauko masa shi a duk inda yake (kafin rasuwar Aisha). Sai lokacin ya ji takun takalmi kas-kas-kas, Laila tsayawa ta yi a soron gidansu hancinta na sirnano mata wani kamshi mai sanyaya zuciya da bata taba jin irinsa a rayuwarta ba. Sai ta ji turarukan da ta gumbudo sun hau mata kai kamar ta juya ta canza kaya. Wata zuciyar ta ce koma canza kaya ki dawo ki tarar ya yi tafiyarsa, duk lokacin da ki ka bata bai ishe ki ba?". Sai ta fasa komawar, ta yi sallama a dakin tare da daga labule ta shiga. Fitilar aci bal-bal ke ci a dakin, haskenta ya haska mata Ma arouf Ji-Kas wanda ya dago ido daga kan agogon (Rolex) da ke daure a fatar hannun hagunsa ya dube ta cikin hasken a ci bal-bal din, sai ta ga kamar idanun sun tara hawaye ne. Amma da ta kalle shi sosai, sai ta gane ba hawaye ba ne, halitta ce. Dogo, mara kauri, yana zaune bisa doguwar kujera kafafunsa a mike yana murza wayar hannunsa. Shaddar jikinsa sai maiko ta ke da alamun ba ta (squeezing) sam-sam. Tafin kafarsa fari sol kamar ba ya taka kasa. Laila ta tuno yadda kullum ta ke fama da goge kaushin tata kafar da dutsen kaushi. Kai Allah mai kyauta da kari, wannan sardidin miji Allah ya dauko ya ba ta har gida. Labban bakinsa jazur da su kamar yankan reza, fuskarshi (intact) cikakkiya, komai ya zauna daf a muhallinsa; wato ido, hanci, gira kowanne daidai yake a inda Allah ya halicce shi. Ba fari ba ne can, sannan ba za a kira shi baki ba. Kamar tsafta ce ta bayyanar da haskensa, amma ba shi da hasken fata sosai. Ga wani saje ya kwanta tun daga gefen fuskarsa sai sheki yake, da gani yana samun (extra) kulawa. Ta ga in ta tsaya kallon mijin nata zai dauke ta sakarai, dole ta kama kanta, ta zauna a kujerar da ke fuskantarsa, ashe ta manta kushin din kujerar a rarake yake sabida tsufan kujerun tana zama ta burma ciki. Tana kokarin fitowa ya ce, "Sorry". Da murya mai nuna kulawa. Ita dai kunyar duniya ta hana ta magana duk da ba ta ga alamun ya yi mata dariya ba. Ta bar kujerar ta koma wata duk suka yi shiru. Ya gaji da shirun ga dare yana yi, kuma cikin Jigawa za su kwana a hotel. Ya ce, "Ba ki iya gaisuwa ba?" A dan daburce ta dago domin ba ta zaci zai yi maganar ba kamar daga sama ta ji ta. "Iyee, na'am?" Ya maimaita, "Ba ki iya gaida na gaba da ke ba?" Da sauri ta ce, "Ka yi hakuri, ina wuni?" Ya basar, "Ya ya sunanki?" "Laila!" Ta amsa. Ya maimaita sunan cikin ransa. Ko ba komai sunan ya dace da ita, kyakkyawa ce da kuma alamun mai son ado ce, uwarta bafullatana ce don haka fara ce tas! "Ni sunana Ma arouf". Ya fadi a gajarce. "Na sani". Ta ba shi amsa. "Ya akai ki ka sani?" Ta dube shi da kyawawan idanunta kamar ta ce waye bai sanka ba a garin nan? Sai kuma ta kama kanta, ta ce, "Baba ne ya fada". Ya gyada kai. Cikin sakakkiyar murya ya soma magana sosai duk da ba ta fi layi biyu ba a ganinsa ya yi cikakken bayanin da ya dace. "To ni Laila na zo ne don mu ga juna, mu kuma fahimci juna kamar yadda iyayenmu suka yi umarni. Na ganki na karbe ki a matsayin matar aure na ta biyu. Na taba yin aure har ina da 'ya. Wannan shi ne". Jimlar nan 'kamar yadda iyayenmu suka yi umarni' bata yi mata dadi ba. Wato ba soyayya ta kawo shi ba, umarnin iyaye ne. Wata zuciyar ta ce, 'Ban da abinki Laila yaushe akayi daren har garin zai waye? Yaushe ya ganki har da zai yi zancen soyayya? Tunda ya riga ya zo a hankali za ki sa ya so ki, ki mallake shi ke kadai, ki mantar da shi tunanin kowace 'ya mace har matacciyar da aka ce yana masifar so'. Wannan tunanin ya sa ta yin murmushi, har ya zaci shi ta yi wa murmushin. "Sunana Laila, ta biyar wajen Baba, ta farko wajen Innarmu. Ina karatu a jami'ar Dutse ina karantar home-economics, yanzu ajina biyu. Na amince ni ma, Allah ya tabbatar mana da alkhairi". Ya gyara zama kamar ya gaji da zaman yana son mikewa ko jijiyoyin bayansa sa warware daga zaman jiran da ta sa shi. Bai yi shiru ba ya ce, "Me ya sa ki ka bar ni na yi ta jiranki? Ko kin san jira na daya daga cikin abubuwan da na tsana a rayuwa ta?" Da hanzari ta amsa laifinta, ta karyar da kai ta ce, "Ka yi hakuri". Ya ce, "Na yi. To ga shi kina karatu a Jigawa, ni kuma Bauchi zan ajiye ki. A can gidana yake, kuma can na fi zama, ko ya ya za a yi?" Laila ta kasa jan ajin a wannan lokacin cewa ta yi, "In za ka bar ni in yi business zan ajiye karatun". Ya dan dube ta na sakanni, "Business kuma? Karatun naki fa?" Ta girgiza kai, "Barinshi zan yi. Na fi so in yi kasuwanci". Cikin mamaki ya ce, "Bauchi ba a karatu?" "Ana yi, ban so ne kawai". Bai ja da yawa ba, ya zunkuda kafada irin ko ohon nan. "Za ki saida duk abin da ki ke son saidawa, in dai a gida ne. Ni zan tafi, Allah ya ba mu alkhairi. Sai gani na biyu". Kamar kada ta barshi ya tafi, ji ta yi in za su kwana suna hira ba za ta gaji ba. Mikewar nan da ya yi zai tafi kamar an soki zuciyarta. Babu yadda za ta yi tana ji tana gani ya bace a falon, ya bar mata sassanyan kamshinsa. Da kyar ta ja jiki zuwa cikin gida, tambayar duniya Innarta ta yi ta fada mata abin da suka tattauna, ta kasa gaya mata komai. Laila ta ce a zuciyarta, wannan ita ce soyayya? Duk da ba wanda zai ba ta amsa ta yarda ta amince ita ce. Ta kuma yi mata mummunan kamu. A bangaren Maaruf babu wani sauyi a zuciyarsa daga yadda ya zo, ya kuma tafi. Suka yi sallama da Hajiya da Baba Liman, motocinsu suka tashi. A cikin Jigawa suka kwana a hotel, da asuba suka kama hanyar Abuja. Karfe goma na safe itama Hajiya direbanta ya dauko ta, sai Bauchi. *** Amina na nan jiya-i-yau, sai ma baki da ya karkace. Ta samu Doctor da nosis suna yi mata gashin bakin. Hajiya ta daga hannunta sama, ta ce, "Ya Allah! Ka dubi wannan kankanuwar baiwa taKa, Ka ba ta lafiya. Lafiyarta kwanciyar hankalinmu ce nida mahaifinta da al'umma masu yawa, domin ubanta warkewarta kadai ce za ta sanya mishi nutsuwa ya ci gaba da ayyukan alherinsa ga al'umma". Bai kara tunawa da Laila ba yana Bauchi ya tare wajen Amina, in ka ga ya fita sallah ce da wanka da canza kaya ya fitar da shi. Don bacci kan kujera rike da hannun Amina ya riga ya saba da shi. Hajiya na gefe kan sallayarta tana lazimi tana tausaya musu su duka. Tana ganin in ya yi auren nan maraicin zai ragun musu, za su samu wadda za ta rungume su su duka biyun, ta rage musu maraicin da suke ciki. Don haka ta yi wa Liman magana a tsaida daurin auren cikin sati mai kamawa, ta kuma umarci Ma'aruf ya kara zuwa wajen Laila su kara fahimtar juna. Sai a lokacin ya tuna da ita. Bai yi musu ba, ya tsakuri lokaci cikin muhimman lokutansa ya je ya kara ganin Laila. Sai dai hirar ba ta yi armashi kamar wancan zuwan ba. A dalilin wasu tsare-tsare na shagulgulan biki da Laila ta lissafo masa har guda bakwai. Shi mamaki ma abin ya ba shi, tana kauyen kayau kamar Ji-Kas don ta je birni karatu shi ne ta samo wannan budadden idon haka? To ina ga ta shiga manyan birane irin Bauchi da Abuja? Shi ba abun ya ce zai janye ba, Hajiya ba za ta yarda ba. Sai ya ga bari