← Book details Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 20

Sashe 5

Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kallonsa, "Ka sani ba ni da ra'ayin aure-aure tun ina karami na. Ita wannan din, tunda yanzu na san halinta sai mu gangara a haka, a ba ni gishiri in ba ka manda. In ta yin taka tsan-tsan da ita. Beside, ban aureta don tazo ta yi min jinya ba. Kamar yadda bana son aure-aure, haka bana son saki, ko don ingancin rayuwar yaron da za a haifa da tarbiyyarsa, don ya faru a kaina ban ji da dadi ba. Haka na yi ta watangaririya sai dana girma na san 'yancin kaina. Duk da da babu haihuwa tsakaninmu auren bai jima ba, ban sani ba ko gaba kadan Allah zai kawo. Ga tsoron kada in tara su (mata) ya zamo cewa duk haka suke, in hakan ta faru Turaki ina zan sa raina? In yi ta saki kuma a ce min auri-saki, ko wanda ya kasa rike mace, to wanda ya kasa rike mace a cikin gidansa, yaya za ayi ya iya rike dubun dubatar al umma? Ka ga gara mu gangara da wannan din tunda yanzu nasan true colour dinta ta bayyana halayenta na fahimceta sosai, ita kuwa har gobe ba ta san waye Ma'arouf Habibu Ji-kas ba. Wallahi! Ko kwata na ba ta sani ba, suna na kawai take ji, ita kuwa tass! Na santa yanzu". Dr. Turaki ya nisa, dama Allah ba ya hada maka komai a rayuwa, idan ya baka wannan sai ya hana maka wancan, shi kuma Engnr. Ji-kas ga ta inda Allah ya jarrabe shi (mata), ban da ita, a ganinsa ba shi da sauran matsala a rayuwarsa. Multi-millonnaire ne da ko ya fadi zabensa (wanda da kyar in zai fadin) kuma ba fata yake ba, ba abinda zai girgiza shi. Juma'ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta. Duk da ance siyasa bata a inda ake tsammanin ta. "DR. AMINA MAS'UOD SHIRAH!". Ya furta masa a hankali da sauti mai dan kauri da ake kira (husky). Mai nuna muhimmancin wanda ya ambata a gareshi. Ma'arouf ya amsa, "Wace ce haka?" "Sunan likitar da ta siffantu da komai da ka ambata ne Ma arouf. Daliba ta ce, mu muka koyar dasu muka yaye su, Physiotherapist ce". "Ka yarda ta hada duk abubuwan da na lissafa a sama Turaki?" "Har ma ta zarta. Proffessional ce da ta san kan aikinta. Ta karbi (award) na Best Physiotherapist of Africa, sannan 'yar babban gida ce. Ba ina nufin 'yar masu kudi ba, a'ah ko kusa, gidan tarbiyya da mutunci. Ina fatan ka gane?" "Na gane, ka yi mata magana toh, cewa zan dauketa haya na tsawon shekara daya in ba ta da aure. Ta kula min da mai sunanta paralysed diya ta. Zan ninka mata albashinta sau hudu in iyayenta za su amince. Duk 'weekend' sai ta tafi gida, ta kwana biyu, ni kuma zan maida 'weekend' lokutan zamana a gida da Amina in ci gaba da kula da ita in ba ta nan har sai ta dawo, ina son mahaifiyata ta huta". Dr. Usman wata irin zuciya ta ciyo shi, "Me ye amfanin zama da matarka to idan har ba za ta iya jin kan abin da ka haifa ba, ko da na kwana biyu a sati?" Ma'arouf ya yi murmushi, zuciyarsa ta hango masa yadda karti biyu suka tube Amina a gaban Laila dake toshe hanci cike da kyankyami, idanunsa suka rine sukayi jajawur. "Idan har bayanin da na yi maka a sama bai gamsar da kai ba, ban san kuma wane bayani zan yi maka ba. Ban aureta don tazo tayi jinya ba". "Kana da sanyi da yawa Ma'arouf (she deserve punishment). Ba kuma na komai ba sai na karin aure". "Ba ni da ra'ayi Usman, wannan kadai na neman kashe ni da bakin cikinta ina ga na karo wasu su hadu su taru su haukata ni? Beside, ni fa ba ni da idon kallon mata har in ji sun yi min. Wannan din ma su Hajiya suka kallo min ita, ba su san kara da kiyashi ba ce daukar marar sani. Mu je a haka ni da Laila Turaki, na yankewa zuciyata irin zaman da zanyi da ita, aurena da ita bai da alaqa da diyata!". Cikin tausayi Dr. Turaki ya ce, "Ni ka ba ni kwangila in kallo maka. Na rantse ba duka suka taru suka zama daya ba". Dariya ya yi kasa-kasa. "Turaki, ka ki ka gane da gangan, mu bar zancen nan, so boring". "Na bari". In ji Dr. Turaki, "God bless you". Inji Ma arouf . "Amin". Duk suka yi shiru. Zuciyar Turaki na tafarfasa, in shi ne da wannan matar wallahi sakinta zai yi, ko da a ce da gold aka kera ta. 'Yar guda daya? Marainiya? Mai lalura? Alhalin ubanta ya mallaka miki duk wani jin dadi na duniya? Shi ne alfaharinki, gadararki? Sai ya tuna kuma fa Ma'arouf dan siyasa ne ba komai zai yi ba ko don ya tsira da mutuncinsa. Ya nisa. Amma ya kasa magana. Ma'arouf ya katse shirun nasu da cewa, "Yaushe za ka yi magana da likitar?" "Insha Allahu gobe. Yau tana off, kuma sai ta rubuta (leave without pay) in har ta amince. Zan yi kokari a ba ta (leave) din, don ba kowa a ke baiwa ba, kuma yana dan daukar lokaci. Ga shi zabe saura sati biyu, don haka in ta amince cikin sati biyun za mu gama komai. Allah ya ba ka nasara, kuri'unmu na tare da kai Ma'arouf. Ka dauke ta ka kai ta wurin mahaifiyarka har a gama zabe ya fi sauki, za kuma ka fi samun nutsuwa tunda ka riga ka rabota da asibiti. Da an gama zabe mun ga abin da Allah ya yi sai a dawo da ita. Amina ta zo. Jikina yana ba ni za ta amince, saboda tana ganin girmana, kuma ba ta yi auren fari ba". Da wannan suka rufe tattaunawar tasu, Ma'arouf ya yi ta yi masa godiya. ***** Shi da kansa ya shiga bayan mota tare da Amina, aka sa mata seat belt. Akilu direba da securities dinsa da sauran masu mara masa baya in zai je ko'ina suka dau hanyar Jigawa daga Bauchi. Daga nan suka yanke hanya suka shiga Gwaram suka mika Ji-kas. Hajiya ta yi mamakin ganinsu. Don ko jiya sun yi waya bai ce da ita za su zo ba. Shi kuma ba ya so ya barta ta kwana cikin (suspense) ne na menene dalilin da zai kawo su adaidai wannan lokacin. Ya shigo dauke da Amina a kafadunsa ya kwantar a kan gadon Hajiya. Sannan ya nemi kujera mai taushi cikin kujerun Hajiyar ya zauna. Ba ta tambaye shi komai ba sai da ta fara cika shi da abinciccika kala-kala a gabansa da ababen sha masu sanyi daga firizarta. Ga shi lokacin zafi ne. Ya sauko daga kujerar zuwa kilishi ya zauna ya tankwashe kafafunsa. Hajiya ta zuba masa ruwa ya wanke hannunsa a kwanon silver, Allah ya taimake su sun yi sallolinsu a hanya. Ta ce, "Me ya faru ne na ganka da Amina?" Ya yi dan shiru yana tunani, muddin Hajiya ta ji halayen Laila ba za ta dauka ba. Balle abinda ya shafi Amina, bata aje yarinyar nan kusa a zuciyar ta ba, soyayyar da take yiwa mahaifiyarta gabakidaya ta dawo kanta. Karamin hukuncin da za ta yi shi ne, Laila ta koma gidan ubanta, shi ya sa auren gaggawa ba shi da amfani. Shi kuma babu saki sai ladabtarwa a tsarin rayuwarsa. Tuni ya rufe (account) din da ya bude wa Laila, ya kuma yi alkawarin ba zai sake zuba komai ba, ta nemi guminta daga 'boutique' din da ya ba ta jari ta bude, kuma ba karamin tashin hankali ta shiga ba da faruwar hakan, don ba wani ciniki mai yawa ta ke yi a 'boutique' din ba saboda tsadar kayan sai matan manya ke iya saye. "Na kawo Amina wurinki ne saboda za mu tafi umrah Saudiyyah ni da Laila sai bayan zabe za mu dawo". Hajiya ta ce, "Masha Allah, to Allah ya ba mu nasara, a je lafiya a dawo lafiya, Allah ya tsare. In ce ko kun taho mata da kayanta da pampers?" "Eh an taho da su suna mota. Bari na yi wa Idris magana ya fito da su". Mutane dankam sun taru a kofar gidan Hajiya Saude suna jiran fitowarsa. Yau dai duk uzurinsa ya sa a ransa zai saurare su, ya yi musu maganin matsalolinsu ya roke su su yi wa Amina addu'a ba a san tsarkin bakin mutum ba. Falon Baba Liman na saukar bakinsa aka bude masa. Jama'arsa da securities da sakatare Idris suka shigo, sannan al'ummar Ji-kas suka shiga shigowa daya bayan daya suna fadin matsalolinsu Idris na kirgo abin da ya ce a ba su yana ba su daga (brief-case) din hannunsa. Yana fadin, "Ku yi wa yarinya ta Amina addu'a Allah ya sa tana da rabon sake taka kafafunta a doron kasa!". Ai kuwa Amina ta sha addu'a har 'ya'yansu kanana sun sa sun yi wa Amina addu'a a makarantun allo. Daga Ji-kas kai tsaye Abuja suka wuce shi da mukarrabansa, gidansa na Apo, ya ma manta da wata Laila. Bayan ya huta sai ya samu 'privacy' ya yi ibada yadda ya kamata shi kadai a gidansa. Ya roki Allah idan mulkin nan alheri ne a gare shi, Allah Ya ba shi nasara, in ba alheri ba ne Allah ya musanya masa da mafificin alherinsa. Washegari ya wuce Saudiyyah umrah. **** RANAR ZABE Yau asabar 9/9 ita ce ranar zabe. An tafka zabe, kowa ya fidda gwaninsa daga manyan jam'iyyun guda uku, NPC, APP da PCP. Masu magudi sun yi duk iya abin da za su iya na magudi, sun yi sun more. In banda 'Sai Ji-kas, wallahi sai Ji-kas, insha Allahu sai Ji-kas' ba ka jin komai daga bakin matasa, sai fastocinsa da ake ta rabawa ana lillikawa a ko'ina. Hakan ce ke faruwa a kowanne yanki (ward) da kowacce karamar hukuma (local government) na Bauchi guda ashirin da biyu. Can na gano Ilyan Goggo ya jefa wa Ji-kas kuri'a, Dr. Turaki da matarsa Zainabu, Amina da Goggonta da Inna Zulai duk Ilya ya tattago su sun zo zabe sun jefa wa (NPC). Amina na ta mitar Ilya ya sa
Chapter 5 · 0% Book details