Sashe 11
Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
WASHEGARI Wajen karfe tara na safe ya fito a shirye, ko karin kumallo bai yi ba, Laila ta kai masa har daki abinda bata taba yi ba saidai masu hidimar abincin gidan su jera masa a dinimg ko kalla bai yi ba. Ta ce, "Ina kwana?" Ya ce, "Lafiya kalau". Ya wuce ta ita da abincin nata. Ya yi sallama ya murda dakin Hajiya, ta amsa, ya sanya kai ya shiga. Ya same ta da jaka a gaba da lullubinta na tafiya, har da takalminta a kafarta. Ta shirya Amina tsaf har hijabi karami ta sanya mata, daga ganinsu za ka gane fitowarsa kawai suke jira. "Hajiya rigima!". Ya fada ciki-ciki. Ya yi kamar bai gane ba, cikin taushin murya ta lallashi ya ce, "Hajiya karin kumallonmu ya kammala, mu uku na sa a shiryawa ni da ke da Aminata". Muryar tashi ta fi kama da ta lallashi, a wani bangaren, nuna tsantsar kulawa ga wanda ake matukar kauna. Idan Hajiya ta ki dandana gidan gwamnati mene ne amfaninsa gare shi? Wannan ya nuna har yanzu tana fushi da abin da matarsa ta yi mata, to shi me ye nasa a ciki? An ce ya yi aure dole, ya yi babu bata lokaci, babu nazari, babu bincike. In Hajiya ta ki zaman gidansa saboda abin da Laila ta yi mata ba ya nan ba ta yi masa adalci ba. Duk da haka ya ji ya gani ya dauki laifin, fatansa ta amince ta zauna kamar yadda ta yi niyya da farko, kuma ta bar Amina da likiciyar da ya daukar mata ta ji da kanta da kananan lalurorinta na ciwuwwukan da girma ke haddasawa da nauyin mijinta. Ya kuma fi son duk sanda ya shigo ko zai fita ya ga Amina cikin gidan, ya san halin da ta ke ciki kullum, ko da babu ci gaba a lafiyarta. Ganinta da sanin kowanne motsinta kusa da shi shi ne kwanciyar hankalinsa. Hajiya ta ce, "Toh! Sabon salo, namiji da suyar naman sunan matarsa. Mu je mu ci sai ka kira min Akilu mu kama hanya". Ya yi dariyar abin da ta ce. Waya ya yi wa amintaccen kukunsa. Nan da nan ya zo ya shirya komai a gabansu a kasa kan kilishi, saboda Hajiya da Amina ba masu hawa tebir ba ne. Da kansa ya zuba wa Hajiya romon bindin saniya da ya dahu ya yi lugub. Ya hada mata shayi mai kauri, ya zuba mata gasassar hanta da koda, ya gutsira mata biredi mai laushi. Hajiya ta soma ci sai ya koma kan Amina, a baki ya ba ta 'tea' da 'cake', don abin da ta fi ci kenan. Ya zuba romon kaza a dan 'bowl' yana ba ta da cokali, sai da ta ture sannan ya ci nasa. Da suka kammala ya mike ya fiddo waya zai yi magana, Hajiya ta ce, "Akilun za ka kirawo mana?" Nan da nan dabara ta fado masa. "Ni ba Akilu zan kirawo ba, Dr. Turaki zan kirawo, wanda ya kawo likitar da za ta dinga kula da Amina. Yau muka yi da shi za ta zo". Hajiya ta yi shiru, a ranta ta ce, 'na ga mai sa ni in bar Amina a nan a wulakanta min ita'. Ya kai wayar kunnensa suka yi magana da Kwamishinan nasa. "Tura address din wayar Akilu ba wayata ba ya je yanzu ya taho da ita". Ya kashe wayar ya sanya a aljihu. Ya dubi agogon hannunsa na danyar azurfa karfe goma saura kwata, goma zai shiga office wanda ke nan cikin gidan nasa. Ba zai iya tsayawa jiran isowar likitar ba. Ya zauna yana fuskantar Hajiya cikin lallashi da taushin murya. "Hajiya abin da ya sa nake so ki zauna tsawon sati guda, don ki nazarci likitar Amina ne, don ni yanzu mata tsoro suke ba ni. Duk da Turaki ya ba ni tabbacin nutsuwarta dari bisa dari, akwai bukatar ki dan sa mata ido irin na manya cikin hikima, ki kuma ganar da ita abubuwan da suka shafi Amina, kamar abincin da ta fi so, abin da ta ke so da wanda ba ta so. Abubuwan da ta ke yi a da can kamin ta samu lalura da sauransu. Ki kuma nazarci cewa, za ki iya bar mata amanar Amina ko a'ah? Shi ya sa nake so ku zauna tare na akalla sati guda, na kuma riga na fada wa Baba Liman, ya ce ya yi miki izini". Hajiya ta nisa, "Shi kenan zan zauna". Ya sumbaci hannun Hajiyar ya mike, "Ni zan wuce office sai azahar zan shigo". "A dawo lafiya". Ya juya zai fita ya ji Hajiya na tambaya, "In ce ko ba kedara ba ce?" Ya dan daga kafada, "Ba na ce ba, amma na san ba zai kawo kabila ba, ki yarda da shi, shi ne babban abokina na kuruciya, ba zai kawo wadda za ta cuci Amina ba. Na yarda da shi Hajiya". "Shi kenan, je ka za mu dan kwanta kafin ta zo. Amma wane daki ka tanadar musu su zauna in na tafi? ka dan nesanta su da kai saboda matarka, in har da gaske ka yarda ba za ta cuci Amina ba, ka dan raba su da nan". "Ba matsala Hajiya, a nan (downstairs) dakin yara yake, sai su zauna a ciki. Zan sanya a zuba musu komai da za su bukata. Amma yanzu ku zauna a nan din tare zuwa tafiyarki. Kwamishina ya tura wa Akilu adireshinta ya tafi ya dauko ta". "Shi ke nan, je ka kada ka bar jama'a na jiranka don kai ne shugaba, babu dadi sam". "Toh Hajiya". Ya cika hannun Amina mai lafiya, ya fita. Bai dade da fita ba Laila ta yi sallama, bayan ta ma'aikata ne da manyan 'trays' suka shigo tare. "Hajiya ga (breakfast)". "Ai mun karya Laila". Ta juya ta kalli kwanukan ko kwashewa ba a yi ba. Ta mike, cike da haushi, wato ya ki cin nata yazo nan ya ci da uwarsa da yarsa, ta daure tace "Mu wuni lafiya to, ina da taro ne da hukumar makarantun firamare, ban san lokacin da zan shigo ba. Gobe kuma zanyi tafiya". A ranta tana fadin, 'Tunda na ji kamshin mutuwa a kanki tsohuwar nan gara in lallaba ki mu rabu lafiya'. Hajiya ta ce, "A dawo lafiya". Tana fita Hajiya ta ja Amina suka kwanta. Ma'aikata suka fita da komai, suka gyara wajen, suka fita su ma. **** Amina na dakin tantabarunta, bayan ta shirya tsaf, sallama ta ke musu tana fada musu za ta yi dan balaguro, amma ta wakilta Baba Talatu ta dinga zuba musu abinci kullum, ta sauya musu ruwan sha in nasu yayi kura, sai kace mai magana da mutum dan uwanta-. Ilya ya zo zai sanyo kai gidan, wata luntsumemiyar jeep na fakawa a kofar gidan Malam Mas'ud. Nan da nan ya gane motar daukar Dr. Ameena ce zuwa gidan gwamnati. Ya danna kai cikin gidan da sauri, har yana tuntube saura kadan ya fadi. "Tafi a hankali Ilyan Goggo". In ji Baba Talatu. "Ina Dr. Amina? In ce ko ta shirya, an zo daukarmu". Daga dakin tantabarun Amina ta jiyo shi, ba ta san sanda ta saki dariya ba. Wai an zo daukarsu, kai ka rantse da Allah tare za su yi aikin. "To Ilyan Goggo ina zuwa, muna sallama ne da mutane na". Ilya bai san san da ya watsar da girman da yake bai wa Aminar ba, saboda haushin da ta ba shi, "Ke da Allah ki fito, Tantabarun me?" Ya isa ga akwatunta guda daya da ke gefe ya dauka. Goggo ta fito daga daki Amina ta fito daga dakin tantabaru, wata tantabara ta biyota ta hau kafadarta, ta kuwa sakar mata kashi a kafadar, Talatu ta goge mata, ta rungume Goggo da kyar ta sake ta, suka rako ta har zauren karshe ita da Talatu, tuni Ilya ya kame a gaban mota. Akilu ya fito ya bude mata ta shiga ta rufe kofar, ya ja motar a hankali suka bar unguwar suka dauki hanyar gidan gwamnati. Kasancewar Akilu ke jan motar ba a tsaya yi musu dogon bincike ba. Ilya na gaban mota, Amina na kame a baya. Farin cikin duniya ya cika zuciyar Ilya, yau ga shi a gidan babban masoyinsa His Excellency Engnr. Ma'arouf Habibou Ji-Kas, ban da yi wa Allah godiya cikin zuciyarsa ba abin da yake yi. Akilu shi ya yi musu jagora har falon shiga gidan na biyu. Nan ya ce su zauna zai kira Hajiya. Ya zaro wayarsa ya kira Hajiya, ya ce, "Likitar ta iso" Hajiya ta ce, "Ka yi mata kwatance ta iso ko ka kira mai aiki mace ta shigo da ita". Mai aikin ya sa ta shiga da ita, nan Amina da ilya suka yi sallama, ta dauko jakarta, amma sai mai aikin ta karba suka wuce can ciki. Akilu ya ce da Ilya su je ya maida shi. Hajiya da Amina suna kwance cikin bargo, Hajiya ba bacci ta ke ba lazimi ta ke, Amina ce ke bacci. Mai aikin ta yi sallama Hajiya ta ba ta izinin shigowa, ta murda kofar suka shiga. Amina na binta a baya. Hajiya Saude ta mike sosai ta janye bargon zuwa rabin jikinta, lullubin kanta yana nan bai fadi ba, ta zauna sosai tana kallon likita Amina kallo na kurillah, doguwar mace sambaleliya son kowa, kirar jikinta bata matan hausawa bace, tafi mata kama da mutanen Sirrleone, mai aikin ta ajiye jakar Amina ta tafi. Amina har sai da ta ji wani iri da kallon da Hajiya Saude ke mata. Kamar tana son gano ta inda zata cutama jikarta. Ta tsugunna har kasa ta gaishe ta. Hajiya ta dan saki fuska ta amsa jin tayi hausa, kenan ba kedarar bace. "Taso-taso ki zauna a nan kin ji 'ya ta". Hankalinta ya kwanta yanzu tunda ba kabila aka dauko ba. Amina ta samu gefen kilishi mai taushi ta zauna. Ba ta yarda ta hau gadon da Hajiyar ta yi mata tayin zama ba. Ta sadda kai kasa tana wasa da yatsunta. Hajiya ta ce, "Ya sunan 'yar tawa, ko in ce likitar tamu?" Ta yi murmushi, "Sunana Amina". "Ikon Allah, sunanku daya da 'yar taki. Allah ya yi albarka, Ya ba ki ikon kulawa da ita da