← Book details Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 20

Sashe 1

Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry WordDocument 0Table Data Normal Default Paragraph Font Normal Table No List 0Header Char_34457df9-d6f7-4f81-9850-48c6ddbb647d header 0Footer Char_f8179cde-3f89-4ca3-aa0e-ebb39081e3d5 footer Hyperlink SANADIN KENAN! 2 Sumayyah Abdulkadir [email protected] HYPERLINK "mailto:[email protected]" [email protected] SADAUKARWA Sadaukarwa ne ga duk makaranta littattafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda ban sani ba, Allah ya hada mu cikin alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi. DON TUNAWA DA Domin tunawa dake marigayiya Kakata kuma Goggo na HAJ. HAWWA ABUBAKAR WALI. GARGADI Ban yarda a kwafi wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba ko karanta shi a rediyo ba tareda iznina ba, hakan zai kaimu ga tsayawa gaban hukuma, wadanda bansan inda kuke ba kuma zamu hadu a kotun Allah ranar da bawa bashi da abin biyan hakkin dan uwansa sai kyawawan ayyukan sa. Takori. TUNASARWA Littafin SANADIN KENAN! Kirkirarren labari ne don fadakarwa da nishandantar da mai karatu kamar sauran littattafan TAKORI. Bashi da nasaba dani ko wani nawa ta kowacce fuska, SANADIN KENAN! Kirkirarren labari ne don haka a kiyaye. SANADIN KENAN-2 Sun isa Ji-kas lafiya, wadda ke karkashin karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa. Maigidan Hajiya Malam Halilu, shi ne babban limamin garin Ji-kas, saboda haka gidan na Hajiya ba boyayye ba ne. Ga kuma gyaran da Ma aruf ya yi masa ya zama abin kwatance, in za a yi kwatance za a ce gidan Hajiya Saude farin Gida, kamar ita kada ke da gidan babu kishiya. Hajiya ba ta kara haihuwa ba tun haihuwar Ma arouf, wannan kuma tsarin Allah ne, kuma hakan bai sa Malam Halilu ya taba canza mata fuska ba ko sau daya, don shi yana da yan har takwas duk maza wadanda ya haifa tareda matarsa ta lalle Lami wadanda ke karatu karkashin kulawar Ma arouf. Tafiya da Hajiya ke yi ta huta wajen Aisha bai taba damuwa ba. Haka yanzu da ta ke jinyar jikanyarta Akwai kyakkyawar fahimta tsakaninsu. Kishiyarta Lami ba wai ba ta kishinta ba ne, kawai wutsiyar rakumi ce ta yi nesa da kasa, don gabadayansu har maigidan kamar karkashin inuwar Hajiyar suke, shi ya sa ta shafa wa kanta salama, ta kwantar da kai ta ke cin arziki hankali kwance. Yaran makota suna ta tsalle suna murna Hajiya ta dawo, don sun san tsarabar chaculet ta zo, suna ta kwaso kayanta daga mota suna direwa kofar dakinta. Ta sa mukulli ta bude dakinta, ya yi kura sosai, kwana arba in da biyu ba kwana biyu ba. Ta rasa me za ta ce musu, tunda yau daga asibiti ta ke ba ta da alawa. Sai ta sa mai aikinta Tambai ta gyara dakin, ita kuma ta sallami yaran da kudi ta ce su je su sayi alawar. Ta fada kewaye ta yi wanka, ta yi sallar la asar da ta riske su a hanya. Ta kwanta tana hutawa, Tambai na ba ta labarin abubuwan da suka faru ba ta nan na suna, biki da mutuwa. Hajiyar ta jajanta, ta ce, in ta huta duk za ta leka, koda yake kwana uku kacal za ta yi, Aminatu na asibiti har yanzu. Tambai ta gama abinci lafiyayye ta zubo mata. Lami ta shigo suka gaisa ita ma da nata kabakin abincin. Hajiya ta yi godiya ta zauna tana jajanta jikin Amina, a hakan Malam Halilu ya dawo ya riske su. "Yau babbar bakuwa gare mu ashe?" Abin da ya fara fada kenan yana ta fara'a, da gani ya yi murnar ganin matar tasa. Ta ce, "Ga ni nan dai, duk da ba zama zan yi ba zan koma, har yanzu Mamar Manzo na kan gadon asibiti". ya ce, "Assha! Allah sarki uwata, Allah ya kara afuwa. To yaushe za ki koma ke nan?" Lami da ta ga sun manta ta a wajen sai ta fita ta ba su waje, dan kishi-kishi na cin ranta. Don in ka ga maigidan nasu na wannan fara'ar to tabbata a gaban Hajiya Saude yake. Bayan sallar isha ya dawo daga masallaci ya ci abincin dare, duk a dakin Hajiyar tunda ita zata karbi girki, ta ke gaya masa abin da ya taso ta rana tsaka, wato nema wa Ma'aruf aure na gaggawa. Malam Halilu ya gama sauraronta, ya gyada kai. "Kirawo min shi mu yi magana yanzun nan, akwai kuskure cikin al'amarin nan". Hajiya ta dauko wata katuwar (cellular) wadda ake amfani da ita a wancan zamanin, duk da haka sai masu hannu da shuni ke iya rikewa. Ta danna kiran Ma arouf. Yana dakin tattaunawa da dukkan 'yan majalissar Najeriya, ya manta bai kashe tafi-da-gidansa ba, kiran Hajiya ya shigo da sunan da ya yi 'saving' dinta 'MA MERE' wato uwata da harshen Faransa. Sai ya fito waje ya amsa saboda dukkan uzurinsa ba ya (ignoring) kiran Hajiya. "Karbi, Imam ke son magana da kai". Ya karba suka gaisa da Malam. Malam Liman din ya tambaye shi, "In kana kan uzuri mu bari sai ka koma gida ka samu nutsuwa". "Babu komai, mun gama. Yanzu kowa zai tafi". Malam Liman ya ce, "Madallah. Wato na ji kuna son yin wani shirme ne kai da uwarka, aure ba abin wasa ba ne, ba kuma wasan yara ba ne. Umarnin Ubangiji ne, don haka dole a tsarkake niyya wajen yinsa. Kuna so ku ce don siyasa za ku yi aure, wanda wannan aure ba karbabbe ba ne a wurin Ubangiji. Ka sanya ikhlasi a zuciyarka, cewa za ka yi auren sabida Allah ba don ka yi siyasa ba, sannan ka ga matar sau uku don ka tabbatar da lafiyarta kalau kamar yadda Manzo (S.A.W) ya yi umarni. Ku tattauna, ku aminta da juna, a yi baiko sannan a sanya lokacin aure, wannan shi ne aure, amma ba ka ce ta zo ta nema ma aure kai babu ruwanka ba ko ganin matar ba ka yi ba, wannan aure bai yi ba". Haka ya yi ta jawo masa nassi na Alqur ani da hadisi masu nuni da tsarkake zuciya wajen yin aure ba don cimma wata manufa ta duniya ba. Jikin Ma arouf ya yi ligib, yana son dattijon ko don farke gaskiyarsa a kan komai tsakaninsa da Allah ba irin malaman da ke ba da fatawar son rai don a ba su wani abu ba. Ya ce, "Malam, na yi niyyar aure da zuciya daya, ku zaba min mata kowacce iri ce, zan zo mu ga juna. Amma ni ba zan iya zaba da kaina ba, sai in ta ganin kamar na ci amanar A isha". Maganarsa ta karshe ta baiwa Liman tausayi, shi kansa ya girgiza da gushewar A isha a doron kasa, ya sha tunanin a ina Ma arouf zai samo mata kamarta? Sai ya yi saurin kauda tunanin, ya ce, "Allah zai dubi kyakkyawar zuciyarsa da kyawawan halayensa ya ba shi mace tagari tamkarta, ko fiye da ita". "Babu wani cin amana Ma arouf, A ishar za ta so ka samu nutsuwa a bayan ranta, ba ka yi ta ragaita ba. Yanzu na ji magana, za a bincika, insha Allah Allah zai dubi zuciyarka da halayenka na kyautayi ga kowa, Ya ba ka mata ta gari". Washegari Hajiya da maigidanta sun gama tunaninsu tsaf! Sun kuma tsaida kan 'yar maigarin Ji-Kas, wadda ke karatu a jami'ar Jigawa. An sa ranar aurenta har za a yi watannin baya mijin ya ce ya fasa. A ganin Hajiya da Baba Liman, zai fi dacewa su nema masa 'yar birni mai ilimin zamani, ba irin yaran su na kauye ba, Ma arouf din zai fi son hakan. Hajiyar ta shirya da kanta ba aike ba da yammacin washegari ta tafi gidan Maigari, shi kuma Liman ya tafi wajen mahaifinta. Kowanne ya fadi abin da ya kawo shi. Amsa iri daya suka samu. Yaransu 'yammata uku ne, Sadiya, Laila da Asiya. Wadda duk suke so za a ba Ma aruf ba tare da jan dogon lokaci ba. Amsa daya su ma suka samu daga Hajiya da Liman, a ba shi wacce aka ce ta ke jami'a, suka ce, Laila kenan. To Allah ya sa a yi a sa'a. Uwar Laila guda ce kawai ba ta rangada ba, amma ta taka rawa a tsakar dakinta, 'yar ta aka zabarwa attajiri dan Hajiya Saude farin gida. Nan fa kishi ya tashi, da ma matan uku ne, kuma kowacce na da 'ya budurwa, wato Asiya da Sadiya, sai dai su bana suka kammala makarantar sakandire. An zabi ta Jami'a an bar su. Wannan abu ya yi musu ciwo. Laila kuwa da ma ba dama ce wajen iya yi da kidifiri. Jin mijin da Allah ya kawo mata rana tsaka bayan Mahadi ya fasa auranta kan laifin tara samari barkatai, ta ce da uwarta, "Ashe gaba ta kai mu?" Uwar ta ce, "Gobarar titi a Jos ba!". Ta ba ta hannu duka kashe tare da rungume juna suna murna, babu godiya ga Allah, sai ka dauka wasu kawa da kawa ne ba uwa da 'ya ba, kai ka ce wata ajiya ce suka yi yanzu suka dauki abarsu ba nufin Allah ba. Ita kadai ce mace cikin 'ya'yanta, don haka ba karamin buri ta ci a kan Laila ba, ga shi tun ba a je ko'ina ba Allah ya fara cika mata. Kwanan Hajiya uku ta ce Ma arouf ya baro ayyukansa ya zo su ga juna da matar da suka zabar masa, don a bar sahihiyar magana kafin su bar Ji-kas, dukkansu hankalinsu ya koma kan Amina. Sai a lokacin ya gano Hajiya hannun likitoci ta bar Amina, hankalinsa bai tashi da yawa ba, don ya yarda da kokarin Dr. Umar Bolori a kan Amina da kaunar da yake masa. Motoci uku suka biyo shi a baya zuwa Ji-kas ban da securities dinsa guda biyu da suke tare da shi daga Abuja har Jigawa. Mutane dankam sun yanyame kofar gidan Hajiya Saude kamar yadda suka saba duk sanda ya zo Ji-kas, to yau ma hakan. Da kyar ya samu ya shige dakin mahaifiyarsa bayan ya sa sakatarensa Idris ya sallame su. Ya yi sallah ya ci abincin da Hajiya ta tanadar masa, sai da duhu ya shigo bayan magriba Liman ya karasa da shi gidan Maigari, lokacin babu idon mutane. Ya sanya 'dark-shade' wanda ya boye kwayan idanunsa, yana sanye da shadda (getzner) ruwan siminti da hula zanna kalar shaddar, an yi ma rigar ado da
Chapter 1 · 0% Book details