← Book details Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 20

Sashe 14

Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kwatanta fada akan halshenta ko da a zuciyarta ne, saboda girmansa da kimarsa da ta ke gani fiye dana kowa a duniya in ka dauke iyayenta. Ko sallama ya yi a dakin sai zuciyarta ta girgiza, balle su yi magana baki-da-baki. Ma'arouf ya lura ta takura sosai da zamansa saboda rashin Hajiya. Shima kuma dama sauri yake zai shiga masallaci. Ya mike tsaye, "zaki gida ko? Babu wani sako to?" Ta mika masa ledar maganin da ke hannunta, "Kowanne sau biyu a rana, sai messaging. A kula da cin abincin ta sau uku a rana, magani akan lokaci, canza diaper sau uku, wanka sau biyu. Gashi (thermotherapy) dole sai ni in na dawo". "Ba matsala. Sai kin dawo din. A weekend din gabadaya ina gida for Ameena, ni zan ci gaba da kula da ita, duk abubuwan da ki ke mata na lura na iya banda gashin, zan gwada iya kokarina, zan rufe kaina ba fita ko'ina daga aikin Amina sai scheduling (tsare-tsaren) abubuwan da zan sa gaba idan an shiga renakun sati". Amina ta girgiza kai, "What a simple politician!'. Tana so ta ce, 'Ina matarsa da zai yi wannan aikin mai gajiyarwa na Amina?' Ta ga cewa hakan ba huruminta ba ne, ta ja baki ta yi shiru. Ita tunda ta zo ma ba ta ga matar ba, kodayake ta ji Hajiya tace ta je Saudiyyah. Yau zata dawo. Gashi ita kuma zata tafi. Za ta so ganin wace ce matar Ji-kas??? Lallai za ta kasance babbar 'yar kwalisa kamarsa, ma'abocin ado kamar Dawisu. Ya soma taku zai tadda kofa yana latsa wayar hannunsa. "Akilu ya zo daukarki, ki same shi a falon farko kafin Ameena ta tashi". Ta mike tana tura 'yar jakar matafiyanta mai tayoyi (trolley) ita ma ta yi kofar. To bai fice ba, ya tsaya a bakin kofar yanata waya, sai ta dan dakata daga nesa kadan. Ya gama ya rufe wayar ya sanya a aljihu, hannunsa na dama na bisa 'handle' din kofar. Ba tareda ya juyo ba ya tambayeta. "Ranar lahadi karfe nawa zai zo ya dauke ki?" "Karfe shidda na yamma". Ya juyo gaba daya ya zuba mata fararen idanunsa na yan sakanni, kafin yace. Na dauka za ki ce karfe goma na safe?" Amina ta yi murmushi har kumatunanta suka lotsa kanta a kasa, cike da girmamawa take magana. "Ina kiwo ne ranka ya dade, bayan ganin Goggo, I want to spend some time with them". "Kiwon na mene ne?" "Tantabaru (pigeons)". Ya yi dan faffadan murmushi wanda har ya bayyanar da fararen jerarrun hakoransa wanda ba kasafai yake yi ba, sosai abin ya birge shi. Yana sha awar sana i na kiwon gida irin wadannan, wannan dalilin nema yasa yanada gidan gona na kiwon dabbobi da tsuntsayen gida nashi na kansa. Amma babu tantabaru a ciki. "Zan sayawa tawa Ameenar aure biyu, ita ma ta kiwata, nawa ne kudinsu?" Amina ta girgiza kai, "Ba na sayarwa ba ne. Amma ita zan ba ta kyauta". "Godiya ta ke Dr. Amina, ina son account number". "In wata ya kusa cika zan bayar ba yanzu ba......" Ya tare ta, "Ba albashi zan saka ba, sakon mahaifiyarki ne". Amina ta girgiza kai, "Zan so kada hakan ya shiga tsakaninmu Your Excellency. Banda albashina babu wani abu makamancin wannan da zai hada mu". Ya dan daga kafada, alamar baida damuwa akan hakan, ya kuma tattare gira cikin mamakinta da jin haushin kalaman ta, amma ya shanye, ko kadan fuskarsa bata nuna komai ba. Ya bude kofar saura kadan ya fita ya dan dakata yayi magana cikin tsare gida. "Ki je Akilu na jiranki, yanzu za ki ga ta tashi. Naki asusun ma in kin ga dama kada ki bayar". Ya sa kai ya fita. Da alamu bai ji dadin maganganunta ba. Duk kuma sai ta ji ba dadi, ta shiga damuwa. Amma ita iyakar gaskiyar abin da ke ranta ta fada, ba ta zo don cin daular gidan gwamnati ba. Ta zo neman guminta ne, gumin nata kawai take son ci, don haka a sanyaye ta tura jakarta ta fito zuwa inda direban ke jiranta. Ta gaishe shi don ya manyanta. Ya amsa da karramawa, ya karbi jakarta ya sanya a mota ta shiga suka tafi. **** Goggo na alwala a gindin famfo, Amina ta yi sallama. Goggo ta dakata ta amsa tana kallon mai shigowa. Aminanta ce, tayi wani kyau mai sanyi, hatta muryarta ta canza. Wani sanyi ya ratsa zuciyarta, da gudu Amina ta yar da jakar hannunta ta sheka ta rungume Goggonta. "Na yi kewarki Goggo, na ji dadin samunki lafiya". Goggo ta yi murmushi, "Cika ni to in karasa alwalata. Ke kam, ban san yaushe za ki girma ba". Ta cika ta tana dariya, ta nufi dakin tantabarunta. Tana ciki tana duba lafiyar kowannensu, Ilya ya yi sallama ya shigo. Ya ce, "Aha! Wannan sassanyan kamshin na san daga inda ya fito. Barka da zuwa Hajiya Dr. Amina". Ya fadi tare da dunkule hannu hadi da rankwafawa alamar jinjina. Amina ta ce, "Umh, Ilyan Goggo na Baban Ameena. How I wish zan iya dumi da shi in ba shi labarinka ko watarana ya kira ka ku gaisa". Ilya ya gintse fuska, "Kina nufin ba kya ganinsa? Na dauka tuni an wuce gurin kin gabatar da ni?" Amina ta girgiza kai, "Oh-oh! Mutumin nan ina ganinsa dare da rana, as if ganin nasa ya fi komai arha. Amma wallahi Ilya bana iya doguwar hira da shi, kamar wani babban Zaki ko Giwa yake zama a idanuna. In ba a kan abin da ya zama dole ba, bana iya bude baki a gabansa. Gara yau zan ce mun yi zancen mintuna biyar amma ya zama dole ne, saboda mahaifiyarsa da nake amfani da ita wajen jakadanci a tsakaninmu ta tafi. Hirar kuma ta tantabaru ce, karshe kuma bata kare da dadi ba, baram-baram muka rabu a kan account number". Ta kwashe yadda suka yi ta gaya masa. "Ba ki kyauta ba Amina". Goggo dake gefe tana jin su ta fada, "Tunda ya ce ki ba shi sai ki ba shi ba kawai? Ba abokin musunki ba ne. Watakila shi bai saba da a yi masa musu ba ma. Ba a mayar da hannun kyauta baya, musamman kyautar manyan mutane, kuma ya ce ba ke zai yi wa ba, a nan ya nuna girmamawa ne ga mahaifiyarki. Ba wai na damu da abin da zai banin ba ne, amma kin san ko me zai bada din girmansa ne. Ba abinda zai tsikari abin da yake da shi ba ne, hanya ce ta kyautatawa wanda ya kyautata maka ka ji dadin taimakon da yake yi maka". Ilya saboda kuluwa harararta kawai yake yi. "Kyale ta Goggo, shashasha 'yar bukulu. Ni na yi nan Goggo kada zuciyata ta buga. Talatu ba ta jin dadi shi ya sa ba ta zo ba, ina da abubuwan yi da yawa". Ya shuri takalmansa ya fice kamar kububuwa, ji yake kamar ya kirbi Amina ko ya huce. Shi ba abin da za a bayar din ne ya dame shi ba, a'ah, ita wace ce da za ta yi wa masoyinsa musu, har ta bata masa rai? Ina ruwan Ilya mai soyayyar babu gaira babu dalili alhalin ba a san da kai ba. Haka Amina ta shiga hidindimunta a gidansu kamar yadda ta saba, jefi-jefi Ameena karama na fado mata a rai. Ta debi kyawawan Tantabaru aure biyu manya-manya ta saka a karamin keji ta ajiye don cika alkawarin da ta yi. In dare ya yi zama ta ke a gefen gadonta ta shiga bincike cikin manya-manyan littattafan (Physiotherapy) don kara wa kanta sani a kan lalurar Paralysis. Ba ta da buri a yanzu irin na samun lafiyar Ameena Ma'arouf, tana tausaya mata amma ta fi tausaya wa ubanta, wanda ba shi da kwanciyar hankali sam saboda ita. Don ma dai an ce zuciyar shuwagabanni mai fadi da zurfi ce, da suke iya daukar large abubuwa ba tare da kowanne ya gogi dan uwansa ba. Goggo ta ba ta wasu addu'o'i ta ce, a cikin zam-zam za ta dinga tofawa tana shafe mata gabbai da su in tana yi mata gashin kashi. ***** Ranar Lahadi karfe shidda daidai na yamma kuwa suka ji dirin mota a kofar gida. Aka aiko yaro wai Akilu yazo daukar Amina. Ta tattara yan komatsanta cikin handbag dinta tayi sallama da Goggo da Talatu yaron ya fitar mata da trolley din kofar gida. Akilu ya karba ya sanya a mota, Ilya baya nan balle su tafi tare, tana fitowa Akilu ya karbi kejin tantabarun hannunta ya sanya a bayan motar ya bude mata kofa ta shiga, ya zagaya ya shiga mazauninsa ya tada motar suka hau titi, Amina tana rokonsa kada ya kara bude mata kofa, domin a haife ya haife ta. Babu inda ake bincikarsu har suka tadda mansion din masu gidan. Dakinsu ta nufa kai tsaye da kejin tantabarunta a hannu. Babu kowa a dakin sai Ameena, tana ganinta fuskarta ta yalwata, daga kwancen da take ta daga hannunta daya mai lafiyar tace aunty Amina ta aje kejin a kan mudubi, ta karasa ta tayar da ita zaune, ta dora ta a cinyoyinta ta rungume ta a jikinta, sai kuma ta sunkuce ta sai bandaki, ta wanke ta tas! Ta yi mata duk abin da ta saba yi mata sannan ta fito da ita. Tana cikin yi mata gashin kashi, bayan ta shirya ta cikin sababbin tufafi taji an murda kofar an shigo. Kamshin turaren sa ne ya ankarar da ita cewa shine. Ya shigo da sallamar sa ciki-ciki, mai nuna har yanzu fushi yake da mai dakin. Ta amsa, ba tareda ta juyo ba don bata distracting aikinta, ko ya zauna ko bai zauna ba? Bazata ce ba! Ta cigaba da abinda takeyi. Ya harde hannu a kirji yana kallon su, sai a lokacin ta tuna fushi yakeyi da ita, da abinda Goggo tace akan argument din nasu da ta je gida, na (account number), ta dakata da abinda takeyi ta shiga nutsuwarta sosai ta juyo sai karaf! Idanunsu suka hadu dana juna, tayi saurin sunkuyar da kai kamar yadda ta saba in tana gabansa, bata iya kallonsa ko na minti daya directly cikin idanunsa, a bisa dalilai masu yawa da har
Chapter 14 · 0% Book details