← Book details Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 20

Sashe 19

Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sha gaya mata ba ya son ganin artificial make-up, bai saba ganinsa a Aisha Maman Ameena ba, in don shi ta ke yi ba ya so. Ta bar fuskarta natural hakan yakeso amma ta ki bari, a ganin Laila ita daban matacciyar matarsa daban kowa tabi ra ayinta. Ba yadda za a ce mata biyu sun taru sun zama daya wajen ra ayi da akida a wannan zamanin. Karamin tsaki yayi, har sai da ya shiga kunnenta, ta dauke kanta daga akwatun talabijin ta dube shi. "Ya ya dai?" Ya hadiye haushinsa. "Me ya sa ba kya gaisawa da physiotherapist mai kula da Ameena, idan Amina bazata samu alfarmar sannu daga gareki ba?" Ba ta ce komai ba, baya ga cuno baki gaba, bai damu ba ya ci gaba da cewa, "nasan ko sunanta baki sani ba duk tsayin zamanta a gidannan. At times inaso muyi maganarta sai wasu abubuwan su mantar dani, ke kuma baki taba tuna min ba. Kamar bakisan da zamanta a gidan ba. Sunanta Dr. Amina to, suna zaune a dakunan downstairs na bangaren nan, amma kamar ba ki san da su a gidan nan ba Laila. Don ban taba ganin sawun kafar ki a inda suke ba, a cire Amina karama don dama bata cikin lissafi, amma ita wannan bakuwa ce dake aiki a karkashina, a matsayinki na matar gidan ta cancanci kulawarki ko da da gaisuwa ne. Na hore ki da gaisuwar mutunci ta cigaba a tsakaninku. Zaman Ameena ta ke kadai ba na wani ba". Laila ta sake cuno baki. "A kan me zan dinga gaishe ta? Ni da ita waye a saman wani? Ta taba zuwa inda nake ta gaisheni? Ta fiya girman kai, ba ta taba nemana a gidan nan ta gaishe ni ba, sai ni zan zubar da girmana in dinga zuwa inda ta ke?" Cikin girgiza kai ya ce. nida ba ni da girman ai ni nake zuwa inda suke ina gaishesu . Daga haka ya yi shiru ya kyale ta, ya ci gaba da abin da yake yi. Ta kyabe baki a ranta tace kai ka ga zaka iya ***** Wannan satin da Amina ta zo gida, Goggo ta lura da ta faya shiru-shiru, ta zama wata irin sukuku da ita. Ita kuma ba wani abu ke damunta ba kamar ta inda za ta dauko wa Goggo zancen Tantabaru, ga shi ba za ta iya kin ba da su ga Baban Ameena ba a kan dalilai masu yawa, wadanda ta sani da wadanda ba ta sani ba. Duk da ta san za ta kasance cikin kewa mai yawa idan ta bada rabin tantabarun nan. Amma abin mamaki zuciyarta ta ki zama lafiya idan ba ta bada su din ga Gwamna Ji-kas ba kamar yadda ya bukata. Kuma ba a kan ko sisi ba. Da yamma tana dakin Goggo da manyan littattafanta a gabanta tana nazari, wanda bata rabo da yinsa sai dai in bata kadai ce ba, amma da aka dan jima sai ta rufe ta ture su gefe, ta zuba uban tagumi. Goggo ta shigo ta ganta a haka, har ta dauki abinda zata dauka a dakin ta fita ta dawo Amina bata san anyi ba, ta karasa bakin gado ta zauna, yayin da Amina na zaune a kan kilishi, har Goggo ta zauna ba ta ganta ba, sai da ta kai hannu ta taba ta. Ta juyo firgigit ta dubi Goggo. "Me ke damunki ne Amina? Tunda ki ka zo wannan satin nake ganinki cikin damuwa. Wannan uban tagumi na magani da mene ne?" Amina ta ga cewa, dole ne ta gaya wa Goggo tunda dai ba za ta dauki tantabarun nan ba tare da saninta ba. Sai dai ba ta san ya ya Goggo za ta karbi maganar ba, kada ta yi wani tunanin otherwise. Duk da haka dai ta ga bata da mafita sai ta daure ta ce. "Goggo, wai Baban Ameena ne ya ce na ba shi rabin tantabaruna". Goggo ta dan yi shiru, kafin tace "rabin tantabaru? Me zai yi da su? Wace irin hira ku ke yi tare da har ki ka yi masa maganar tantabaru? Me ya hada ku ban da aikin 'yarsa?" Ta bi ta tsattare ta da ido, cike da tuhuma sai da Amina ta daburce. "Ba...... ba abin da ya hada mu Goggo, amma kullum kafin ya fita office da bayan ya dawo sai ya shigo ya ga lafiyar 'yarsa, in har yana gari. Farkon zuwana gidan ko kallona ba ya yi, ko inda nake ba ya kallo. Wani irin mutum ne shi din a lokacin da mahaifiyarsa kadai ke ganin hakoransa. Ko magana za mu yi a kan lafiyar yarinyar ba ya kallona, ni ma bana kallonsa muke yi. Sau uku Hajiyarsa ta zo ita ta sanya muka fara magana da juna, don cewa ta yi ya yi wa matarsa fada ta dinga zuwa inda nake muna gaisawa tana ganin lafiyar Ameena, to matar ta ki mu gaisa, ta kuma ki zuwa ganin Ameenar. Daga lokacin ne ya soma yi min 'yan tambayoyi a kan rayuwa ta ina ba shi amsa. Sai muka dan fara sabawa har na kan bashi shawarwari akan siyasarsa kuma abin mamaki yana dauka. Rannan ya ce in dawo da wuri ranar wata lahadi, zaki iya tuna ranar Goggo? Na ce masa ba zai yiwu ba don ina kiwo, ya tambaye ni na me ye na fada masa, sai ya ce zai saya wa Ameena aure biyu na dauka na ba shi. Wannan satin kuma gabadaya rabi ya ce in ba shi". Goggo da ta tsura mata ido ta nisa, ta ce, "Ni dai ina kara gargadinki da tsare mutunci a ko'ina. Ba ni da mummunan tunani a kanshi, a kwashe a ba shi, ai hayayyafa suke". Amina ta ji kamar an sauke mata dutsen Dala da Goron Dutse daga kanta. Ta ce, "To Goggo, zan gaya masa kin amince ya turo a kwashe". Rana ta farko da Amina ta yi tunanin buga wa Ma'arouf waya a rayuwarta. Sai dai wani barin na zuciyarta na hana ta. Amma barin a yi kiran ya rinjayi na kada a yi kiran. Yana tura Ameena cikin wheel-chair a wata farfajiya da ke cikin gidansa ya ji kira daga wayarsa da ya kunna yanzu-yanzun nan. Ya yi magana da Turaki ne, ya manta bai sake kashewa ba ya sanya a aljihu. Abin mamaki sunan da ya baiwa lambar da bai taba tsammanin kira daga gareta bane wato Amina's Doc' ya bayyana a fuskar wayar. Ya amsa ba tare da ya ce komai ba. Da dai ta fuskanci ya amsa, sai ta fadi sakonta kai tsaye, "Goggo ta amince a zo a kwashi Tantabarunnan". Murmushi ya yi mai sauti, "Babu gaisuwa sai sako kai tsaye Dr. Amina?" Amina ta yi shiru, jikinta har rawa-rawa yake yi don wani tsoro-tsoro ma take ji na kiran data yi, a ganin ta ta zarce limit din da ya kamace ta (ta wuce gona da iri), bayan ganin kima da girmansa, he s someone she respect most! Maimakon ta yi gaisuwar sai bakinta ya subuce da fadin zahirin abin da ke zuciyarta. "Ina Ameena? Ya ya ta ke? An yi messaging din yamma? An fito da ita shan iska? Ta sha magani?" Murmushi ya yi. Ya dan russunar da gazing dinsa kan Ameenar da ke cikin wheel-chair zaune abinta, a zuciyarsa ya ce, '....Ameena kina da wadda ta damu dake da lafiyarki, bayan ni da Hajiya. How I wish Laila ce haka! Da gininnikan da na yi wa rayuwa ta ba su soma kokarin rushewa ba.......!.' Ya lumshe ido ya bude, bai ce komai ba. Sai ya kara wa Ameenar wayar a kunnenta. "Ameena ga Aunty". Ameena ta yi magana da iyakacin sautin ta mara karfi, "aunty yaushe za ki dawo? I'm missing you... I prefer your messaging than Daddy's...(Ina kewarki, na fi son tausarki a kan ta Daddy)". Dr. Amina ta yi murmushi, ta kara makale wayar a kunnenta na dama. "Kin manta na ce kullum na tafi ki kirga kwana sau uku zan dawo?" "Na kirga, yau ne ko?" Amina ta ce, "That's my girl, I'm coming soon". Ya dage wayar daga kunnen little ya mayar kunnensa, "Za a zo da wata motar daban a dauka, na gode Dr. Amina tunda an ce ba na sayarwa ba ne. Duk abubuwan da ki ka tambaya an yi su. Ki gaida ILYAS!" Ya kashe wayarsa. Amina ta zaro ido, wayarta na neman subucewa daga hannunta. "ILYA? A ina ya sanshi?" Ta ajiye wayarta a gefe cike da mamaki. Ta fito da gudu tsakar gida, Ilya ba ya nan sai Talatu tana hada zobo, "Talatu ina Ilya?" Talatu ta ce, "Kaf yau bai shigo ba, ya je karbar balance". Ba ta rufe baki ba ta ji alamar shigowar sako a wayarta. Ta koma ta zauna ta bude. Abin da ta gani ya ba ta mamaki, (alert) ne guda biyu daga banki na zunzurutun kudin da ba za ta iya fadar adadinsu a fatar bakinta ba. Ta dauko calculator ta hau lissafi. Ga dai albashinta kamar yadda aka yi alkawari sau hudunshi a kowanne wata, har na watanni takwas. Ga kuma wasu makudan wadanda daban suka shigo daga account din wani mai suna Usman Turaki. Amina ta tabbata Dr. Turaki ne, Ma'arouf ya turo kudin daga account dinsa. To shi Turakin wa ya ba shi (account number) dinta? Da sauri ta danna masa kira. Kwamishinan yana gida cikin iyalinsa, kasancewar yau Lahadi ce. Ya amsa kiran Amina cikin murmushi. "Ya ya dai Dr. Amina?" Ya fada cikin kulawa. Amina ta hau in-ina, "Umh---um da ma na ga alert ne". Ya gyara zamansa, "Ta inda aka hau ba ta nan ake sauka ba???" Amina ta yi murmushi jin da muryar da ya yi maganar kamar mai yi da karamin yaro. Tana so ta ce, to daya alert din fa? Ba ta san cewa a fili ta fada ba. "Na Tantabaru ne!". Ya fada cikin murmushi mai sauti. Ta karyar da murya, kamar mai shirin yin kuka. "Wallahi ni ba siyar masa na yi ba, kuma na gaya masa". "Ya ce na gaya miki idan ba ki karba ba ki bar tantabarunki". Ta yi hanzarin cewa, "Na karba!". Sanin cewa dukkaninsu babu sa'an ja'in'jarta. Magana
Chapter 19 · 0% Book details