Sashe 17
Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
**** Abinda basu sani ba shi ne, wadannan manyan yan siyasar da Ma arouf ya sauke daga muqamansu sun ja gefe su da magoya bayan su suna kokarin kafa sabuwar jam iyyar adawa mai karfi wadda zata tuzge gemun (NPC) wato jam iyyar Ma arouf. A cewar su Ma arouf yayi musu butulci. Dasu aka fadi aka tashi aka sha rana kafin ya samu kujerarsa, amma yanzu yayi kaurin wuyan da zai iya tsigesu bayan amintaka tun ta jami a. Sun sha alwashin ko zasuyi yawo tsirara Ma arouf bazaiyi ta-zarce ba (wanda babban burinsa kenan yanzu kuma burin al ummar Bauchi birni da kauye). Tunda dukkan sirrikansa sun san su sunyi alkawarin rarake kasan sa a zabe mai zuwa. ***** Asabar ce sassanya kuma ranar hutu ga dukkan ma aikata, abincin maraice yake baiwa Ameena don baza a kirashi abincin safe ba tunda ta karya kumallo da jimawa tun takwas na safe, yanzun kuwa ana maganar karfe goma sha daya ne na rana, bayan ya dawo da ita daga zagayen da yake yi da ita cikin wheel chair daga bakin ruwa (swimming pool), chips (dankalin turawa soyayye) mai tsananin laushi yake bata, duk da laushin nasa sai ya murza mata shi da hannunsa don ta ji saukin ci, yadda ya ga Dr. Amina na yi mata. Tun ranar juma'a yake jin kansa cikin wata irin kewa da sanyin jiki, wadanda ya rasa daga ina suka zo. Ya san dai ba tafiyar Laila garin Ji-kas ba ne ya haifar da hakan ba, don ta saba tafiye-tafiyenta tun ma kafin ya zama gwamna bai taba jin komai ba. Yau din ya bude mata wuta ne a kan dole ta je mahaifarta ta kwana biyu, shi ba zai dauki wofintar da iyaye ba saboda rashin hankali irin nata, idan kuma ba za ta je ta kwana ba, to ta tattara yanata-yanata ta san inda dare ya yi mata. Dole kan ba yadda za ta yi tana zumbure zumbure ta debi kayan sanyawarta kala biyu, aka cika boot din hummer jeep' da kayan abinci da sitturu, shadda bandir-bandir ta kame a bayan mota da 'yar sandarta mace a gaban mota, aka nufi Ji-kas da ita. Wannan ya faru ne ranar Juma a kwana daya da dawowarta daga wata tafiya data yi Dubai inda ta kara komawa check-up. Don haka weekend din daga shi sai little Ameena suka yi shi, ya dauke ta suka koma nashi dakin, a can suka kwana. Ko wanka ya kasa yi mata, tun bayan tafiyar Amina ta wannan satin, ba shi da wannan kuzarin. Yana jinsa (incomplete) tamkar wani bari na jikinsa ya mutu shi ma. Ya kuma laluba a zuciya da gangar jikinnasa ya kasa gane abin da ya haifar da hakan. Al'amarin ya ci gaba to such an extent that..... ya taho dakin da Ameena da Dr. Amina suke, yana dube-dube, domin ya ji a jikinsa kamar a can din ne ya rasa abin da ya maida shi incomplete. Ya tsaya ya zuba dukkan hannauwansa biyu a aljihun bakin wandon jeans da ke jikinsa yana dube-dube. Ga injinan aikinta nan ba ta tafi da su ba. A can kan madubi kayan shafarta ne da turare guda daya da wani deo-spray zungurere (right guard) shima guda daya. Ya karasa gaban madubin ya daga turaren ya kai hancin sa ya sunsuna. Sassanyan kamshinta na kullum shi ne a cikin turaren. An rubuta 'Davidoff (cool water)'. Kayan shafar duka sai da ya bi su ya sunsuna, ta yi gyaran gadon tsaf kamin ta fita. Ya karasa ya zauna a gefen gadon ya yi tagumi, ya dauki filonta ya rungume a cinyoyinsa, ya runtse idonsa. Yanzu dai komai ya bayyana gare shi, babu sauran bincike ko hesitation (shakka). Dr. Amina Mas'ud yake kewa, bayan tarin nazarinta da ya yi watanni bakwai yana yi, ya lura daban ta ke da sauran mata. Abin da bai taba faruwa da shi a kan mace ba bayan Aisha. Ba kuma zai ji shi daidai (cikakke) ba, sai ta dawo cikin gidansa. Komawa ya yi dakinsa ya dauko Ameena ya dawo da ita dakin. Ameenar ta tambaye shi, "Daddy, Aunty ta dawo ne?" "A'ah Ameena, sai gobe da yamma za ta dawo. Mu koma can mu kwana, dakina akwai sanyi". Ta yi shiru ba ta kara cewa komai ba, don da ma maganar jefi-jefi ta ke yinta. Imagine! Ma arouf a dakin Amina yar Goggo Hauwa, suka kwanta a lallausan gadon, ya karanta addu'o'i ya shafe ta da su, sannan ya yi azkar din dare da yake yi kamin ya kwanta. Ya ja lallausar duvet din gadon ya rufe su kasancewar lokacin sanyi ne. A daddafe ya kai wayewar gari. Bai taba ganin dare mai nisan wannan ba. Washegari Lahadi, bayan sun karya shi da Ameena ya dauki wayarsa ya kunna, ya kira Kwamishinan lafiyansa Dr. Usman Turaki. Turaki ya daga yana fadin, "Ya aka yi ka kunna waya yau lahadi Yaa Maulaya? Na gaya maka ka bar komai a hannunmu, samun wadataccen hutu a kowanne karshen sati yana da kyau a gare ka". "Yaushe zan huta tunda ba a halicci dan Adam don ya huta ba? Daga wannan sai wancan. Babban farin cikina Ameena's condition is improving, bakinta ma ya bude tuntuni tana magana cikin kokarin likiciyarta. Da gaske ka ba ni physiotherapist kwararriya, wadda bayan likitanci tana da hikima da basira on her own unique way. Yanzu dai ba ni lambarta shi ne abin da ya sa na kira ka". Dadi ya rufe Kwamishina Turaki, hamdala da tazbihi da addu a ya kama yi cikin ransa; Allah ya sa Amina ta zamo karshen matsalolin Habibu-Jikas. In abinda ya yi zargi ya zama tabbatacce bai san irin farin cikin da zai yi ba. "Zan turo lambar yanzu (through text). Amma ya ya uwargida ta karbi zaman Amina a gidanta ne? Bamu taba yin zancen da kai ba". "Ban gane ba? Kana nufin ni da gidana akwai mai ba ni 'do and don ts ne?' "Ba haka nake nufi ba, ka san halin mata da kishi, za ta karbi abin the other way round". "To ban samu matsala da ita ba gaskiya har yanzu akan zaman Dr. Amina. Saboda ba kowa ne mutum a idon Laila ba, balle har ya ishe ta kallo. Ta yi tafiya ranar da Aminan ta zo. Ranar da ta dawo kuma Aminan ta je gida, da ta dawo na dan gabatar mata da maganar Amina a gurguje lokacin zan fita, ba ta ce komai ba, harkokinta ta ci gaba da yi, amma bana jin har zuwa yau ko gaisawa sun taba yi, Laila ba ta zuwa inda ta ke saboda girman kai irin nata. Kuma bata cika zaman gida ba. Ta sake komawa Saudiyyah ta dawo shekaranjiya, a ranar kuma ko hutawa ban bari tayi ba na kada ta Ji-kas ta gaida iyayenta, don ita ba ta san ya kamata ba sam sai an yi mata jan ido. Don haka abinda zan iya cewa shine har yau bamu zauna specifically munyi magana akan Ameena ba amma ta san da zamanta cikin gidannan. Duk lokacin dana so yin hakan sai wani uzurin ya sha kaina, ita kuma bata taba yimin maganar ta ba tun gabatarwar dana yi mata na Aminan a gurguje, wai ance ido da kunya, abinda tasan bazata yi bane don na samo mai yi kaga bata da Lambar Amina da nake nema a wajenka, zan tura Akilu ya dauko ta ne shi ne ya sa na ke bidar lambar tata don in gaya mata gashi nan zai taho. Ba zan iya bari sai yamma ba kamar yadda muke yi. Abubuwa da yawa ina kasa yi wa Ameena, ni da ita duk muna jigata". Turaki ya jinjina kai zuciyarsa kal, a ransa ya ce, 'A juri zuwa rafi dai... Maigirma Gwamna, wanda bai iya kallon mata ba, yau yana bidar lambar wayar su... yake kuma zaune da wadda ya tabbatar ba sonsa ta ke ba, kudinsa ta ke so. Ina nan zaune za ka sake kira na with different story....! Sun gama magana da Dr. Usman din bayan nan ya tura masa lambar. Ya tsurawa lafiyayyun lambobin ido na layin mtn yana mai shawara da zuciyarsa kan ya kira, ko kada ya kira? Abu ne da bai taba yi wa wata mace a rayuwarsa ba bayan mahaifiyarsa sai ko A isha. Bai taba kiran Laila ba, ita ta ke kiransa koyaushe. Me ya sa ya damu da Dr. Amina har haka? Kwarai yake son jin sassanyar muryarta, a wasu lokutan hakan na faruwa da shi duk sanda ta je gida. Bai dai taba tsananta a gare shi ba kamar yau, ko dai ya sa Turaki ya kira ta ya fada mata? Ma'arouf yarinyar nan wata iri ce da ba a gane kanta at times. Ita ce mutum ta farko da ta taba yi maka musu a rayuwarka. Idan tace bazata taho yanzun ba ya zaka ji a ranka kuma me zaka iya yi mata banda ranka ya baci a banza? Be careful da girmanka a idanunta! . Zuciyarsa ke karantowa, ta kuma yi sa ar yakar duk wani ego da ya kawo tunanin ayi kiran wayar. Don haka maimakon kira, sai ya rubuta mata gajeren sako mai layi biyu kacal. Wanda bai kunshi wata ma ana ba. 'Ga Akilu nan ya taho daukarki yanzu, please don't ask me why?' Ji-Kas. Amina na zuba wa tantabarunta abinci da ruwa a safiyar lahadi da waya a kunnenta, tana magana da wata abokiyar aikinta Dr. Nazifa da ke 'specialist hospital Bacas' tana gamawa kafin ta sauke wayar sakon ya shigo wayarta. Ta ji karar shigowar tasa, don haka ta ajiye kwanon dawar da ke hannunta ta bude. Tun kafin ta karanta ta ji gabanta ya yanke ya fadi ganin sunan da ta yi saving watanni bakwai a baya ya bayyana, bata kuma taba amfani da shi ba (ba a kirata da lambar ba, itama bata kira ba ko yin sako); JIKAS! Ba shakka ta firgita, tunda har ya yi mata sako da kansa wani muhimmin abu ne ganin bai taba yi ba a tsawon zamansu na watanni kusan bakawai. Tuni ta daburce. Allah ya sa ba wani abu ne ya samu Ameena ba. Tunaninta kenan. Da sauri ta karanta. Ta yi dan jimmm!