← Book details Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 20

Sashe 20

Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

daya ta makale mata a makogaro, ta kasa yo waje da ita. Wato, a ina suka samu (account number) dinta? "Kada ki tsaurara bincike......" Ya fada tare da karashewa cikin dariya, "Insha Allahu SANADIN KENAN da dukkaninku za ku amfana da juna, har hakan ya haifar da alkhairi mai yawa. Ke dai ki ci gaba da kokari, muna yaba kokarinki a kan Ameena. Allah ya saka da alkhairi". Kan Amina ya dau zafi, ta kasa warware komai a maganganun Dr. Turaki. SANADIN me? Ita fa ba ta iya falsafa ba, sunayi mata maganganun da bata fahimta. Bata son sanyawa kwakwalwarta abin da ta gagara fahimta balle har ya dame ta. Tana cikin rukunin mutanen da ba komai suke sanyawa a ransu ya damesu ba. Su suka sani iyayen daure wa mutum kai. Bata da abin cewa, bata da zabi bata da abin yi banda tayi godiya sukayi sallama da malamin nata. Bayan gama wayarsu da Turaki, ta kira Ilya. Ta yi ringing har ta gaji bai dauka ba. Ta gaya wa Goggo wai Baban Ameena ya ce yana gaida Ilya. Ita fa mamaki zai zautata, Goggo wa ya yi masa zancen Ilya? A ina ya san shi? Goggo ta yi shiruuu, tana kallon Amina, zancen Ji-kas ya yi yawa a bakin Amina. Daga wannan sai wancan. Ta danne tunaninta, ta ce, "To wadannan mutanen mene ne abin mamaki in sun binciko abu?" Amina ta ce, "Har account number dina fa sun samo A nan Goggo ta dan yi murmushi, amma ba ta nuna wa Amina komai a fuskarta ba. Amina ta yi shiru, maganar albashi da kudin tantabaru (kamar yadda Turaki ya ce), ta barsu a ranta har zuwa wa'adin aikinta ta isar da muradinta. In ta ce za ta mayar Dr. Turaki zai ga kamar raini ya shiga tsakaninsu, haka wanda ya turo kudin ba za ta ji dadi ya ce ya dawo mata da tantabarunta ba. Tana tunane-tunanenta har aka sanar da ita Akilu ya zo daukarta. Tare da shi wata irin babbar mota ce mara kujeru suka kwashi tantabarun cikin tukwanensu. Ita kuma ta yi sallama da goggo suka tafi. Tana ta sauri ta isa ga Amina suka yi karo da mai fitowa, saura kadan Amina ta fadi. Ta yi sauri ta dafa kofa. Ta dago don ganin waye haka da tafiya kai a sama? Aunty Laila ce, kamar yadda ake kiranta a gidan. Amina ba ta yi mamaki ba, ta bata hanya ta wuce bayan Laila ta rafka mata tsaki. Hakan ta sha faruwa in dai suka hadu. Don Aunty Laila ba ta shiga dakin da suke. Amina kuma bata taba gigin hawa upstairs ba ko da wasa. Amina ta tuno haduwarsu ta farko da Aunty Laila. Ranar wata litinin ce, ta dawo weekend da kwana daya, a ranar ne kuma Laila ta dawo daga tafiyar da ta yi. A lokacin ko gaisuwa ba ta shiga tsakaninta da ubangidanta kasancewarsa shi ma marar sakin fuska kamar matar sa. Ta ga kofar dakin daya daga shigifofin falon downstair dinsu a bude, kuma an kunna karatun alkur'ani yana tashi daga radiyo. Ta tambayi mai aikin da ke bayanta, "Hajiyan Ji-kas ta zo ne?" Ya ce, "A'ah likitar Ameena ce da Ameena a ciki". "Likita?" Ta tambaya cikin mamaki. Mai aikin ya ce, "Eh, mai kirkin gaske". Kawai sai ta danna kai dakin don ganewa idanunta bata ko yi sallama ba duk Amina na jinsu. Kallo daya ta yi wa Amina ta ji ba wanda ta tsana duk duniya irinta, saboda wasu irin ilhamomi, kwarjini, kuruciya da alamun wadatar ilimi mai zurfi da ke tattare da yarinyar. Amina ta katse kallon kurillar da ta ke mata da cewa, "barka da dawowa, ina wuni?" Laila ta buga tsaki ta juya. Ko Ameena karama ba ta kalla ba, balle ta samu alfarmar sannu. Banda ta san halinsa da tsarin rayuwarsa babu son mata a ciki ko cikin al'amuransa da burirrikansa, da ba za ta bar wannan likitar ta zauna mata a gida ba. Ko ta halin kaka sai ta kore ta. Wani bangare na zuciyarta ya ce, "kin isa? Ke a wa? Ya yi hukunci a kan rayuwar diyarsa da ki ka nuna ba za ki iya ba ki ce ba haka ba? Ai sauki da adalci ya yi miki in kina da adalci". Tun daga wannan ranar in sun hadu za ta san yadda ta yi ta bangaje ta ta harare ta, ta yi mata tsaki. Abin har dariya yake baiwa Amina, don haka duk sanda suka hadu tun daga nesa za ta kauce mata, wanda ma ba su fiya haduwar ba. Duk abin da ta ke nema tana da shi a dakinsu. Fitowarta sai in za ta zaga da Ameena a wheel-chair ta sha iska. Ba ta kuma taba yin gigin hawa upstairs ba inda suke da mijinta. Ta nisa daga tunanin da ta ke yi ta wuce ciki ta tadda Amina, ya kwantar da ita ya tafi tana ta barci. Kwana biyu ba su ganshi ba, ya je seminar jihar Lagos. Ranar da ya dawo ta kama Laraba, tana yi wa Ameena chemotherapy aka yi mata kararrawar kira zuwa falo na hudu kamin a tadda inda suke. Ta yi hanzarin kammala abin da ta ke yi, ta sanya Ameena cikin kekenta ta gangaro da ita suka fito tare zuwa falon da kiran ya fito. Amina ta daskare a tsaye ganin abin da ke faruwa a kasaitaccen falon............! Me ke faruwa??? Mu biyo Dr. Amina Mas ud Shira da His Excellency Ma arouf Habibu Ji-kas a littafi na 3, kuma na karshe Insha Allahu. Taku har abada; Takori.

SANADIN KENAN-2 TAKORI
SHAPE \* MERGEFORMAT
SHAPE \* MERGEFORMAT
PAGE \* MERGEFORMAT
Calibri
Calibri
Times New Roman
imes New Roman
SimSun
Arial Black
Arial Black
Calibri Light
Calibri Light
Cambria Math
Cambria Math
!%),.:;>?]}
$([{
Light horizontal
Light horizontal
_GoBack
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
user
Normal.dotm
TECNO LD7
2690
WPS Office
16.000
17006ae4654c4d1da49843419cafffd1
Chapter 20 · 0% Book details