Sashe 8
Rayuwa Da Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ameen" Du'a ta amsa. Hajiyan zuciya Inna wuro ta sauke sannan tace. "Amma wani hanzari bah gudu bah, ina so kiyi min alƙawarin cewa zaki dawo gida kafin ki cika shekaru ashirin ciff a duniya".
Murmushi Du'a ta sakar mata tare da mai kallon ta kan Inna wuro tace. "Karki damu Inna in sha Allahu zan dawo kafin na cika shekaru ashirin a duniya, ai naji kuna faɗa a tsakanin ku cewa idan na cika shekaru ashirin a duniya, wani abu zai bayyana a jikina, kuma sannan rayuwata zai kasance a koda yaushe cikin hatsari ne".
"Yanzu inada shekaru sha tara ne a duniya, nasan za'a yi mana hutu a makaranta kafin na cika shekaru ashirin".
"Dan aka duk ku kwantar da hankulan ku baki ɗaya". Tana kaiwa nan ta cinciɓi jakarta tareda ɗora wa akan a malanke na saniya, wanda mai gari ya tanadar musamman dan suje bakin ƙauyen.
Saida gaba dayansu suka hau sannan dokin ya soma tafiya, lokaci daya fuskar Du'a ya sauya daga walwala zuwa damuwa.
Saurin dakatar da su tayi da faɗin. "Ku tsaya". Tsayar da a malanke ɗin suka yi tare da mai da kallon su kanta.
Da sauri ta sauka daga kan amalanken sannan ta nufi cikin gida da gudu. Kai tsaye ɗaƙin magani da mahaifiyarta ta ke ta nufa.
Shiga ɗaƙin tayi, sannan ta durkusa kan gwiwowin ta tace. "Mama inason ki saka min albarka, nima yanzu zan zama yar birni zan je birni karatun likitanci sannan na samo miki sunan maganin da zata farfado dake kinji".
"Ina so kiyi min fatan nasara". Share hawayen ta tayi da bayan hannunta sannan ta kara da cewa. "Shike nen na tafi kuma zan so ace kafin na dawo ki farfaɗo daga wannan baccin da kike".
Sannan ta ƙara da cewa. "Ya Allah ka kiyaye min mahaifiyata, kasa mata nutsuwa da kwanciyar hankali, duk wani cuta koh damuwa ka yaye mata su, ameen ya rabbil izzati".
Tana kaiwa nan ta fice daga ɗaƙin tare da ficewa daga gidan ta nufi inda amalanken yake sannan ta shige ciki tare da ɗaura mayafi a fuskarta, saida ta tabbatar ba'a ganin komai na fuskarta in banda kwayar idanun ta, sannan ta yi wasu Inna sallama.
Abinci kala_kala mutanen kauyen suka saka musu ganin cewar za suyi kwanaki a hanya batare da sun samu abin taɓa wa bah.
Addu'a inna wuro tayi musu tare da mata fatan sauka lafiya.
Sai da suka yi wa kowa sallama daga bisani suka ja amalanken suka bar harabar kauyen.
Tafiya mai nisa suka yi sannan daga nan suka isa wani garin, saida suka yi kwanaki biyar a hanya kafin daga bisani suka hangi wata siririyar hanya, babu bata lokaci suka fara bin hanyar.
Tafiya suke batare da wani ya kula ɗan uwansa bah, babu zato suka ji an rufa su da raga yayinda gaba dayansu suka shige cikin ragar tare da yin sama.
Hatake gaba dayansu suka kwashe da dariya gami da faɗin. "Babu wanda yake bin hanyar nan ya tafi lafiya, wannan yankin mu ne babu wanda muka bawa umarnin bin wannan hanyar".
Kokarin cire kanta Du'a take daga jikin ragar, amma ina akan ya cutura. Kallon su tayi a fusa ce tace. "Kune waɗan nan yan dajin masu karɓar haraji Koh?".
Ƙeƙeta dariya gaba ɗaya suka yi!. Sannan daya daga cikin su yace. "Kamar naso na gane wannan muryar taki, su waɗan nan mazan da suke mara miki baya basu faɗa miki mu yan daji bane?".
"Maza_maza ku kunce mu kafin raina ya ɓaci". Ta ƙarashe maganar tareda kokarin kunce kanta.
"Ba za'a kunce bah mene ne za kiyi? Kin san mu su waye kuwa?, koh an gaya miki cewa bamu san abin da muke bane, mu ɗin jarumai ne na farko kin gane".
"Banzaye matsorata idan har ku ɗin da gaske jarumai ne, toh ku kunce mu mana".
Giegiza kai gaba ɗaya suka yi, yayinda ɗaya daga cikin su ya ɗauki wuƙa sannan ya yanka ragar, hatake gaba ɗaya suka faffaɗo daga cikin ragar.
Tashi su ukun suka yi yayinda Du'a ta karkaɗa jikin ta, sannan sannu a hankali ta fara cire mayafin dake kan fuskarta, inda daga ƙarshe tayi nasaran cire shi baki ɗaya.
Washe haƙora gaba ɗaya suka yi ganin yadda ta ke da matuƙar kyau na halitta.
Murmushi ta sakar musu tace. "Yanzu zaku barmu mu tafi ɗin ne koh a'a?".
"Sabo da me bazamu bari ki tafi bah?, mu asuwa? Ai mu bayin mata ne dan aka sai yadda kuka ce damu ".
"Yauwa koh ku fa". tana kaiwa nan ta hau kan amalanken, yayinda suma mazan suka hau, a sauka lafiya yan jejin suka yi musu yayinda suka buɗe musu hanya suka tafi.
Daga nesa Du'a ta hango wucewar motoci, zuru _zuru tayi da idanuwan ta ganin abinda bata saba gani bah a kauyen su.
Tsayar da amalanken suka yi sannan ɗaya daga cikin su ya kalli Du'a yace."zamu dakstar da amalanken a nan sabo da ba zai yu mu tafi akan amalanke bah, motoci ne kawai ke wucewa".
"Mene ne kuma motoci?" Du'a ta tambaya. Dariya gaba ɗaya suka yi sannan suka ce da ita. "Mota tans nufin abin da mutane ke hawa domin suje duk inda ransu yake so batare da sun taka da kafafin su bah ".
"Auu! Kenen shi ne mota. lallai gaskiya yan birni suna jin daɗi, babu ruwan su da shan wahala saidai kawai abin ya ɗauke su babu ruwan su da takawa".
Tafiya suka farayi daga bisani suka isa bakin titin. Tarar da adaidaita suka yi tare da yiwa mai napep kwatancen inda zai kai su.
Shiga ciki suka yi yayinda Du'a ta tsaya tayi zuru_ zuru da idanuwa.
Kallon ta suka yi suka ce da ita. "Ki shigo mana mu tafi kinga shima sauri yake, kuma inda muke ɗin nan komai zai iya faruwa".
Girgiza kai Du'a ta yi tace. "Ni bazan shiga bah, tsoro nake ji gaskiya, na fasa zuwa birnin mah kawai mu koma kauyen mu". Ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka.
"Kamar ya mu koma ƙauye bayan mun riga mun zo birni cewar ɗaya daga cikin su, sannan ya kara da cewa. " Wallahi idan baki shigo bah akwai yan mafiya masu shan jini kuma hanan suke da zama, suna hango ki za su cinye ki, kuma gaki fara dama kuma farare suke ci".
Jin aka yasa cikin Du'a ya duri ruwa, babu shiri tayi saurin shige wa cikin adaidaitan. Daga bisani mai napep yaja adaidaita yayi gaba.
Kai tsaye medile aka nufa dasu, inda gefe guda Du'a ta saki baki sai kallon gidaje ta ke tana daɗa jinjina kai, taɓa ɗaya daga cikin su tayi tare da nuna gidajen tace. "Su kuma waɗan nan mene ne su? Na gansu kamar dodo".
Dariya mai napep ya fashe dashi yace."gaskiya baiwar Allah kina da ban dariya, yanzu sabida Allah da Annabi gidajen ne kamar dodo, koh da yake abin ka da yar ƙauye ba lallai kisani bah ".
"Toh waɗan nan gidaje ne wanda mutane ke rayuwa a ciki, dan aka ki daina ƙauyanci kada ayi miki dariya, kema da kaɗan_kaɗan zaki saba ".
"kana nufin house?". Du'a ta faɗa tareda kauda kai gefe. Zaro idanu mai napep yayi yace. "Abin mamaki yar ƙauye da jin turanci, kenen kuna da makaranta achan ƙauye kenen".
"Kwarai kuwa". Du'a ta faɗa. Gaskiya ne amma makarantar tana da tsada har kika san mene ne house ai kin more wallahi". Cewar mai napep.
"Eh mana amma ni a cikin gida aka koyar dani". Sosai Du'a ke hira da mai adaidaita tamkar sun san juna a da.
Saida suka isa bakin wani gida sannan adaidaitar ta tsagaita da tafiya tare da tsayar da napep ɗin.
Fitowa suka yi daga cikin napep ɗin tare da biyan mai napep ɗin kuɗin sa. Karɓa yayi tare da yi musu godiya sannan yaja nepep ɗin shi ya bar wajan.
Ƙwanƙwansa kofa suka soma yi, saida aka ɗau kusan mintuna sha biyar suna tsaye a wajan kafin daga bisani aka buɗe kofa.
Sosai hajiya Sakina tayi farin ciki ganin su Du'a tare da yi musu tarɓa mai kyau. Saida su Du'a suka ci suka sha kafin daga bisani suka tashi tare da ɗauro alwala suka tada jam'i suka yi sallah tare da rama sallolin da ake binsu.
Bayan sun idar da sallah mutanen Mai gari suka tashi da zimmar tafiya. Haƙuri Hajiya Sakina ta shiga basu da cewa su kwana in yaso gobe sai su koma. Amma ina suka ce mata yau suke son komawa.
Ba yadda hajiya Sakina ta iya, aka tana ji tana gani suka fice daga gidan tare da tafiya.
Ɗaukar ghana must go ɗin Du'a hajiya Sakina tayi tare da saka su a cikin mota ta maida kallon ta kan Du'a tace. " Masha Allah gaskiya Allah ya azurta ki da kyau, keɗin karshe ce kuma maƙura a kyau. Na tabbata maza rububin ki za su dinga yin".
Murmushi kawai Du'a ta yi tace. "Na gode sosai mama".
"Yauwa muje na kaiki makarantar koh domin nayi miki registration, Allah dai yasa su baki admission domin shi ne the most important thing, yanzu aka mah ƴata tana chan amma a hostel take zama, dan aka kema a hostel zaki dinga zama ".
"Dan idan kika ce zaki zauna dani a nan zan gundureki ne, dan aka bana son ki takura". Tana idda magana ta shige motar sannan ta buɗe kofa yan zaman banza tace da Du'a ta shigo.
Ganin Du'a bata motsa daga inda take bah yasa ta faɗin. "Du'a lafiya? Me yasa kika tsaya kuma?".
Amsa Du'a ta bata da faɗin. "Ina jin tsoro nee ". Murmushi hajiya Sakina tayi tace. "Kada ki samu damuwa ki kwantar da hankalin ki babu abin da zai faru shigo mu tafi kinji ".
Shiga cikin motar Du'a ta yi bsyareda ranta yaso akan bah.
Tada mota hajiya Sakina tayi daga bisani ta bar harabar gudanar.
Kai tsaye makarantar Northwest university ta nufa ba tare da jinkiri bah. Saida suka dau lokaci kafin su isa makarantar. Baki sake Du'a ke kallon shige da fice na daliban makarantar.