Sashe 3
Rayuwa Da Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zira hannun sa yayi cikin jakar sakar sa, ya ciro kullin magani, sa'anan ya mikawa Inna wuro, karba Inna wuro tayi, Tareda jujjuya shi a hannun ta tace, wannan fah?
Malam Ali yace, wannan maganin kariya ne, a Duk lokacin da kika ga tana wani irin abu, koh Kuma, ta suma, toh ki dunga bata wannan maganin insha Allahu za'a samu sauk'i.
Ard'o yace, amma Malam, matan kauyen mu shekaru sha daya, sha biyu, wasu mah basua Kai wa aka, muke aurar da su, taya Kuma zamu bar Joda acikin daki na wajan tsawon shekaru sha biyar, ai kawayenta mah a lokacin suna da yara, ina ganin kamar a barta basai an rufe ta bah.
Murmushin takaici Malam Ali yayi, yana mai fadin, idan babu lafiya Hana yin aure ne? Idan babu rai zaka yi aure ne? Wannan abunda za'a yi badan aceci rayuwarta daga, mugun abunda zai tunkare ta bane, ku kuka sani, Kuyi yadda kuka gadama, nidai na ruga danayi iya bakin kokarina, an wuce gurin.
Yana kaiwanan ya juya da niyan tafiya, kamar ya tuna da wani abu, sai Kuma ya juyo. Yace na manta, ban fada muku abu daya bah, Duk wani da namijin da ya fara ambatar mata Kalman soyayya, koh akasin aka, toh shine zai kasance mijin ta, na har abada. Amma sai wanda da gaskiya yake sonta bada yaudara bah, shine kawai zai aureta, kuma shi zai yi sanadin yadda zatasan Wacece ita daga wane ahalin ta futo, yana kaiwanan ya bar wajan.
Barin shi keda wuya, Mai gari yasa aka rufe taro kowa ya watse.
Inna wuro bata nufi ko ina bah sai cikin gidan ta,
Kallon Joda Inna wuro tayi, tace Joda, mene yake faruwa dake aka, meyasa kike suma a makaranta, bayan kece dogaran wannan kauyen, ke zamu tura makaranta domin ki gyara mana kauyen mu, meyasa Kuma akan zata dunga faruwa dake.
Daidai lokacin Joda ta bude idanuwan ta a hankali,
Cikin rashin fahimtar maganar Inna wuro, Joda" ta Motsa karamin bakinta wanda yake ja sharkaff, cikin muryar yara tace Inna menene kike fada?
Cikin Yaren fillanci ta cigaba da fadin, Inna yaushe zaki bude min kofan dakin da mama ta take, Inason zangan ta Dan Allah,. Ta karashe maganar kamar zatayi kuka.
Murmushi Inna wuro tayi tace, Aa Joda har yanzu ke yarinya ce, bai kamata na bude miki dak'in nan bah, kinji zan bude miki kofan amma sai nan da shekaru masu zuwa.
Kallon ta Joda tayi, tace yaushe kenen? Dago hab'ar Joda Inna wuro tayi, sannan tace, a lokacin da zaki Shiga shekaru ashirin a duniya,
Kuma kinsan mene, girgiza mata Kai Joda tayi, Inna wuro tace Baba yace zai siya miki kayan wasa, daga yau a daki zaki dunga wasa, zaki zama tamkar sarauniya, Kuma idan kika zauna acikin daki, batareda kin futa bah, na wajan shekaru, kina da babbar kyauta ta mussanman,
Cikeda jin dadi, Joda tace, Inna da gaske, gaskiya inason kyauta, idan na Zauna a daki saina samu kyauta koh? Murmushi Inna wuro tayi, ta bata amsa da cewar kwarai kuwa, kinga kece zaki zamo lamba ta daya, Baba zai baki kyautar doki,
Yeeeeee! Joda tace tareda buga tsalle, cikeda farin ciki, tace shikenen nima zan samu doki, ga kayan wasa, gaskiya naji dadi sosai, zan zauna a daki saina samu kyauta ta.
Tashi tayi tareda hawa kan gadon karar dake tsakiyan dak'in ta Fara tsalle a Kai. Hawayen ne ke shirin zubowa Inna wuro, da sauri ta share da bayan hannun ta, ta maida Kallon ta kan Joda tace, ya isa aka koh, yanzu kizo kici abinci, kiyi sallah, daga yau bake bah futa, kin ji dadin ki, malamin makarantar boko dana islamiyya, da kansu zasu dunga zuwa koyar dake. Kinga kin zama yar gatar Inna,
Comments & share PLXX
ALKALAMIN
A'ISHA M.B
(Zinariyar Jajirtattu)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹
🌸RAYUWA DA MACIJIYA 🐍 🐍 🐍
*PAID BOOK ₦400 complt*
kacal babu tsada
*9043687746 Hassana Aliyu Opay bank*
*Evidence of payment*
2347085977298
FREE PAGE 4️⃣➡️5️⃣
WRITTEN & DIRECTED✍️ BY
A'ISHA M.B
(Zinariyar Jajirtattu)
*______________________________________________________________________*
*BAYAN SHEKARU SHA HUƊU*
hankali kwance take busa sarewar nan batare da wani tsoro koh fargaba bah. yayin da karar sarewar gaba ɗaya ya karaɗe dajin. kwance take akan jibgegiyar bishiya dake tsakiyar dajin. lumshe idanuwan ta tayi waɗan da suke Ars colour masu daukan ido da hankali.
Yayin da gashin ta wanda yake baki ya rufe mata fuska, akan bai bani damar ganin fuskar ta sosai bah.
baje gashin ta tayi. Masha Allah baki na ya iya furta wa ganin irin tsananin kyawu da take dashi. Sanye take cikin rigar yan fulani wanda suka yi matuƙar karbar jikin ta sosai.
A hankali na fara ganin macizai na fitowa daga cikin ramu kansu, suna nufar inda take, yayin da suka zagaye ta baki daya.
Murmushin jin dadi tayi, ganin su firfito ga Rike ɗaya daga cikin su tayi, sannan ta motsa ɗan karamin pink lips ɗinta tace, "yau dai na kawo muku ziyara koh, yanzu kunyi farin ciki".
"Shikenen toh yanzu ni zan tafi kar Inna taga bana nan, sabo da tsawon shekaru bata san ina futa bah, duk zaton ta ina cikin ɗaki, ɗan aka ni zan tafi yanzu, saimun sake haɗuwa".
Dira tayi daga kan bishiyar, yayin da ta fara nannaɗe fuskar ta da mayafi, dan kar wani daga cikin kauyen ya ganta.
Tafiya ta ke ƙoƙarin yi, amma sai ta ji an ririke mata ƙafafuwa. Kallon kafar ta tayi, ganin yadda macizan suka riƙe mata kafa alamin basua so ta tafi.
Murmushi tayi wanda yasa asalin kyawun ta kara bayyana, sannan ta cire macizan daga jikin ta, ta kalle su tace, "Aa abokai ku bari na tafi, ku kanku kunsan da cewa bani da babban aminai sama da ku".
"Idan ban tafi bah, asiri na ne zai tonu a wajan Inna, saboda ta gargade Ni cewa kada na kuskure na futa dai-dai da tsakar gida karna futa".
Kuma ta dauka tsawon waɗan nan shekaru, ina cikin ɗaki ne ban taba fita ba". Zama tayi hawaye ya fara sauka kan kuncin ta, sannan tace,"Ni kadai ce a kauyen nan ba'a bari na fita, kuma ni kadai ce nayi karatu a kauyen nan".
"Duk sanda na tambaye ta nace mata, yaushe ne nima zan dawo rayuwa kamar kowa, yaushe zata barni na fara fita kamar yadda suma yaran kauyen nan keyi, amma koda yaushe amsa daya take bani, shine sai nan gaba, sai kin cika shekara ashirin a duniya".
Taɓa sarkar dake wuyar ta tayi, yayin da take jin zuciyar ta nayi mata kuna da radadi, tace,"Yanzu shekaru na sha tara ne, har yanzu bata bari na in futa, babu wani ɗan kauyen nan daya taɓa gani na ba".
"Yanzu sau biyu kenen tsawon waɗan nan shekaru ina fita batare da sanin kowa bah, gashi mahaifiya ta har yanzu bata farfaɗo bah".
Dan aka ku barni na tafi, tana kaiwa nan ta tashi tare da barin wajan. Can cikin kauyen ta nufa, saida ta tabbatar babu wanda yake kallon ta, sannan daga bisani ta haura kan gidan Inna wuro, tare da dira ciki da sauri ta shiga cikin ɗaki tare da cire tufafin dake jikin ta, sannan daga bisani ta kwanta akan gadon karar dake ɗakin.
Jin takun tafiya na mutum yasa tayi saurin rufe idanuwan ta, yayin da tsoro da fargaba ya cika zuciyar ta. Sallama riƙe s baƙin ta shigo ɗakin. Amsa sallamar Dua tayi tace, "sannu da zuwa Inna". Murmushi Inna tayi tace, "yauwa ƴata shin na same ki lafiya?.
Girgiza kai Dua tayi sannan tace, "eh ina lafiya kalau, ta faɗa baƙin ta na kakkarwa.
Binta Inna wuro tayi da kallo ganin yadda gumi yake keto mata ta koh ina.
Sannan tace, "Dua meyafaru naga kina gumi?, hanya kina da gaskiya kuwa?".
Sosa kai Dua tayi tare da faɗin,"hmm babu komai fahh". Murmushi Inna wuro tayi tace, "aba Dua mara gaskiya fah koh a ruwa yake gumi yake, dan aka ki fada min menene?".
Aa inna da gaske nake babu komai. tom shi kenen tunda kince babu komai cewar Inna, sannan ta ƙara da faɗin, ni yanzu zan je na kwanta sabo da gobe muna da shagali na al'adun gargajiya da za'a gabatar, dan aka ba lalle ki tashi ki tarar dani bah, dan koh yanzu mah daga gidan mai gari nake. Dani za'a shishirya abubuwa, kuma ina ganin kamar zan kai dare achan".
Tashi Dua tayi sannan ta nufi inda take a zaune tace, Inna shin zan iya neman wata alfarma daga wajan ki?. Murmushi Inna tayi tace, "ki tambaye ni ko mene ne indai bazai fi karfin na bah, toh ni kuma zanyi miki.
Gyara muryar ta Dua tayi tace, "dan Allah Inna nima ina son naje, tunda ake shagali a kauyen nan, dai-dai da so ɗaya ban taba zuwa bah, ki taimaka ki barni naje kinji. ta karashe maganar hawaye na sauka kan kuncin ta.
Hatake naga fuskar Inna ya sauya daga walwala zuwa damuwa. Kallon ta Inna tayi tace, "nasan da cewa bai kama ta a dinga barin ki a ɗaki bah, amma sabo da babbar kyauta wacce za'a baki yasa nace ki dinga zama a ɗaki.
Ke baki ga cewa ke yar gata bace, na farko ke kadai kikayi karatun boko da islamiyya a cikin yaran kauyen nan, ke kadai kika iya turanci, gashi duk faɗin kauyen nan babu wacce ta kai ki kyau. Ki cigaba da hakuri harki samu kyautar ki na doki, ance ma hakuri ci mahawadaci.
Girgiza kai Dua tayi sannan tace, Ni bana so, na fasa yin gasar da aka sa, bana son kyautar doki. Abin da nake bukata yanzu shine ki dinga bari na ina futa, ina shiga cikin mutane, nima na dinga rayuwa kamar yadda kowa yake yi a cikin kauyen nan.
ajiyan zuciya Inna wuro tayi tace, "maza jeki kwanta". Dua na shirin magana Inna wuro ta dakatar da ita da faɗin, ba tarbiyar dana baki kenen bah, ban baki tarbiya cewa in gaya miki abu sannan ki ƙi ji bah, ban baki tarbiyar da zaki bijire wa magana ta bah".