Sashe 6
Rayuwa Da Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hatake gaba ɗaya suka ja da baya yayinda kowane a cikin su ya faɗi kasa.
A hassale ta bude idanuwan ta wanda suka kara rinewa suka yi Ars sosai. Yayinda iska ya ɗaga ta sama, ya kasance ita ba'a kasa bah kuma ba'a sama bah.
Kallon su tayi yayinda gashin kanta ya baje ya tsaya a mimmike. Cikin gurnani wanda yasa fuskarta yayi jaa yayinda saɓar maciji ya fara bayyana a jikin ta.
Cikin dashashiyar murya tace dasu. "Maza kuzo ku tunkari inda nake, bana tsoron mutuwa kuma sannan bana tsoron abinda mutane ke tsoro, ku tunkare ni idan kun isa".
Hatake munanan halittun suka fara yowa kanta.
Cike da jarumta ta tsaya batare da ta motsa bisa inda take bah. Tsalle ɗaya daga cikin Aljanun yayi tare da yin kanta cikeda mugunta.
Ganin akan da Dua tayi yasata shake masa wuya. Kakari Aljanin ya fara yi. Hatake kayoyi suka fara tsiro wa daga jikin sa.
Saurin sakin sa Dua tayi jin yadda kayar jikin sa ya chaki hannun ta. Rintse idonta tayi jin yadda hannun ke mata zugi.
Cikin daƙewa ta ɗaga idanuwan ta. Da mamaki kuwa taga sun ɓace batt.
Murmushin jin dadi tayi sannan tace. "Aka ce bakua ji, baza ku iya dani bah domin ni nafi karfin tunanin ku.
Babu zato taji an ɗaga ta sama tareda naka ta da kan wani ringimemen dutsen dake tsakiyan dajin wanda suke wa lakabi da dutsen mutuwa.
Wani azababiyar ƙara Dua ta sauke! Hatake jini ya fara zuba daga kanta.
Jin karnin jinin ta, yasa sauran aljanun suka firfito suka fara yowa kanta. Zagaye ta gaba daya suka yi, Yayinda ta ke cikin tsakiyar su.
Hatake naga jibgegen dattijo acikin su wanda haɓar sa ke dauke da farin gemu har kasa. Tare da idanuwa masu kama dana jemage.
Ƙarewa Dua kallo yayi. Hatake gaban sa ya faɗi! Baki na rawa yace . "tabbas babu tantama ita ce, ta dawo daga mutuwa, macijiya mai kwanciyar ɗaukar rai. Sarauniya kuma shugaba na macizai da Aljanu harda mayu.
Shekaru kenen babu ita, yanzu kuma ta bayyana, idan tazo guri bata barin wajan saita yi shiƙa domin bata jure zalunci, duk inda taga hana ba dai-dai bah saita san yadda zata yi ta kawar da abin da ake yi.
Kunyi babban kuskure da kuka taɓa ta, idan har kuka bari ta tashi toh sunan mu mutattu. Domin ba zata barmu da ran mu bah".
Maza_maza ku bar wajan nan dan zata iya tashi a kowane lokaci.
Sarauniya kuma shugaba na gaba ki daya macizan duniya ta dawo, yanzu zata dora aikin ta a inda ta tsaya, zata ci gaba da kawar da azzalumai kamar yadda tayi lokacin baya. Wannan karan ta dawo ne da tarin karfi da kuma baiwa.
Mu gudu kada ta tashi.
gurnani suka jiyo daga bayan su, waigawa suka yi da sauri. hatake suka yi ido huɗu da jibgegiyar macijiya wanda girman ta ya cika dajin gaba ɗaya yayinda bakin ta ke fitar da wuta.
FANS KU BIYO NI A PAGE
NA GABA DON JIN YADDA ZATA KAYA TSAKANIN ALJANU DA MACIJIYA.
COMMENT & SHARE PLS
🙏🏻🙏🏻🙏🏻
ALKALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D80k1puBPBn6uJhojKKhK5
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹
*🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍
*PAID BOOK ₦400 complt*
kacal babu tsada
*9043687746 Hassana Aliyu Opay bank*
*Evidence of payment*
09130398321
FREE PAGE 9️⃣➡️1️⃣0️⃣
WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)
*_______________________________*
Cikin tashin hankali gaba ɗaya suka fara neman hanyar kuɓuta, yayinda suka fara gudun ceton rai. Ɓace wa gaba ɗaya suka yi yayinda suka tashi cikin sararin samania, batareda ɓata lokaci bah suka riƙe hannuwansu baƙi ɗaya tare da zagaye Dua wacce ta zama jibgegiyar macijiya.
Maganganu suka fara yi cikin yaren Aljanu. Ƙaran da Dua ta saki ne yasa gaba ɗaya suka saki juna yayinda ta fara wulli da su daya bayan ɗaya.
Sanin raunin ta da shugaban aljanun yayi yasa shi ya maida garin gaba ɗaya ta zama duhu, yayinda ba ka ganin komai in banda duhu.
Babu zato yaga haske ya bayyana a jikin ta wanda ya cika ilahirin dajin baki ɗaya. Ganin babu sarki sai Allah ya sa gaba ɗayan su ɓace wa daga wajan.
Hatake ta faɗi kasa, babu bata lokaci halittar ta na mutum ya fara dawo wa. Daga karshe ta zama mutum gaba ɗaya. Yayinda gaba ɗaya jikin ta ya mutu.
Saida ta dau kusan hour tana kwance bata farfaɗo bah.
Ɓangaren jama'a garin kuwa, ganin har yanzu Dua bata dawo bah yasa suka sallama cewa ta mutu, yayinda Inna wuro ta fara kuka, sosai gaba ɗaya suke dana sanin barin Dua da suka yi ta shiga wannan dajin.
A hankali ta fara buɗe idanuwan ta, a wahalce ta miƙe yayinda take jin duk gaɓoɓin jikin ta nayi mata ciwo, waigawa tayi taga babu kowa.
Rike kanta tayi don tuna abin da ya faru, amma ina babu abin da ta iya tunawa. Motsa leɓen ta tayi tace. "Me yake faruwa dani?, ina waɗan nan halittun suke?, waya kore su?". Tambayar data shiga yi wa kanta kenen.
Basar wa tayi sannan tace. "Koh ma mene ne su suka sani, nidai na shigo dajin nan kuma sannan ina da tabbacin cewa zan fita lafiya". Tana kaiwa nan ta nufi inda bishiyoyin magunguna suke. batare da ɓata lokaci bah, ta fara tsinkar ganyayyakin. saida ta tsinki adadin yadda ranta yake so, sannan daga bisani ta nufi hanyar da take tunanin cewa ita ce hanyar futa.
Saida tayi tafiya mai nisa sosai sannan daga chan nesa ta hango wani abu mai sheƙi da haske. Karasa wa tayi wajan domin cire kwarkwatar idanuwan ta.
Zaro ido tayi ganin madubi ne wanda aka ƙayata shi da furenni masu kyau da daukar ido. Mamaki ta shiga yi domin ita tun da ta ke bata taɓa gani abu makamancin aka bah. Ƙoƙarin kai hannun ta take kan madubin.
Ta ke taji wani zuciya yace mata kada ta taɓa. Barin wajan tayi sannan ta ci-gaba da tafiya, hango wani karamin bishiya tayi daga chan nesa, da sauri ta karasa inda bishiyar take.
Rubuce_rubuce taga hanyi a jikin bishiyar. yayinda jini ke malala a jikin ganyayyakin ta. Tsoro da fargaba ne ya mamaye zuciyar Dua, yayinda ta ke ji kamar ta kawo kanta ga halaka ne.
Rintse idanuwan ta tayi, cikin kwarin gwiwa ta kai hannun ta ga wannan bishiyar. Babu zato ta fara jin muryoyi mara amo da daɗin sauraro ta koh ina. Yayinda suke faɗin. "Barka da dawo wa duniyar ki sarauniyar macizai, muna miki maraba da zuwa".
Cikin rashin fahimtar furucin su tace."su waye ku?, mene ne kuke nema a gare ni?, maza ku faɗa min hanyar da zan fita daga wajan nan ".
An gama shugaba taji sun furta. Babu tsanmani taga anyi sama da ita sannan aka fara tafiya da ita akan iska.
Saida aka yi tafiya mai nisa daga bisani suka isa baƙin wani kogi wanda launin ta ke jajir tamkar jini.
Sauke ta suka yi sannan suka ce da ita. "Halitta ɗaya ce a duniyar nan zata iya bin ta wannan kogin kuma wannan halittar itace sarauniyar macizai, idan har ke ɗin ce da gaske toh zaki bi wajan nan batare da wani abu na cutar wa ya tunkari inda kike bah".
"Amma kuwa indai ke ta bogi ce toh ki ƙaddara cewa kin zama gawa domin zaki yi mummunan mutuwa ne, sabo da wannan kogin halitta ɗaya ta yarda ta bi ta kanta, kuma ita ce shugaba na macizai ".
'Koh mu da muke Aljanu bamu isa mun bi ta wannan kogin bah, domin idan muka kwatanta yin akan zamu zama mutattu ne. Fatan nasara a gare ki". Suna kaiwa nan wajan yayi shiru.
Bin kogin Dua tayi da kallo, yayinda take ganin kamar duk abin da suka fada karya ne. Tsugunnawa tayi ta dora idanuwanta kan ruwan kogin. Sannan daga bisani ta saka ɗan yatsarta acikin ruwan.
Babu zato taga ruwan ya fara juyi, sannan ya farayin sama, saurin ja da baya tayi ganin yadda ruwan yake jujjuyawa tamkar mutum. Cikin kankanin lokaci taga ruwan ya raɓe yayinda wajan ya bada siririyar hanya.
Batare da tsoro bah ta fara bin hanyar wajan da sauri. Sosai ta ke mamaki ganin baƙon al'amari irin wannan.
Tana barin wajan ta kuma ganin ta a tsakiyar wani dajin daban. Namomin daji gaba ɗaya ta ke ta harba dasu. Yayinda kyawawan tsuntsaye suka fara hawa jikin ta.
Cicire su ta soma yi daga jikin ta, amma a yayinda ta ke cire su wasu na zuwa. Saida tayi da gaske tukunnan suka bar jikin ta. Kowane dabba na dajin binta yake da kallo.
Hatake taga namomin dajin gaba ɗaya sun tsuguna cikin gwiwo winsu tare da saukar da kai ƙasa. Mamaki ne ya kama ta. A yayinda take ganin mene ne akan da suke yi.
Ci-gaba da tafiya tayi, a yayinda suke mara mata baya. Juyawa tayi da sauri gani ko wace halitta ta dajin gaba ɗaya ita suke bi.
Alama ta fara yi musu da hannu dasu koma, amma ina kamar basu san tana yi bah. Ci-gaba da tafiya tayi, su kuma na biye a bayan ta.
Juyawa tayi a fusa ce tare da daƙa musu tsawa! Babu shiri gaba ɗaya suka ja da baya. Cikin ɓacin rai ta nuna su tace. "Maza_maza gaba ɗaya ku koma kafin na hallaka ku baƙi ɗaya". Ta faɗa tsoro fal cikin ranta
Kamar da wasa taga gaba ɗaya sun juya tare da koma wa. Baki sake tabi su da kallo, a yayinda take mamakin kanta. shafa jikin ta tayi sannan tace. "Ta yaya kuma ni na iya yi musu magana? Wacece ni? Me yasa ina ce musu su koma kuma naga sun koma?.
Wani zuciyar tata tace. "Inaga sabo da tsawar da nayi ne shi yasa.
Tafiya ta cigaba da yi inda a karshe ta hangi wani baƙin kofa wanda ba'a ganin ƙarshen ta sabo da girma da tsayin da ta ke dashi.