← Book details Rayuwa Da Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 18

Sashe 15

Rayuwa Da Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Can ta hango ta a yashe a kasa. Babu jinkiri ta yi saurin karasawa wajan. Saurin ɗaga Du'a Maryam ta yi. Yayin da ta fara jijigata tana mai kiran sunanta.

A hankali Du'a ta fara buɗe idanuwan ta yayin da ta dora su hakan na Maryam. Saurin miƙe wa ta yi sannan ta fara waige-waige.

Kallonta Maryam ta yi cike da mamaki ta ce. "Meyafaru Du'a? Me yasa na ganki a yashe a wajan nan.

Girgiza kai Du'a ta yi ta ce. "Babu abin da ya same ni, ina cikin ƙoshin lafiya sannan ta ce.

"Maryam kin samu lafiya, babu abin da ya same ki Koh?". Du'a ta ƙarashe maganar tare da tattaɓa wuyan Maryam.

Murmushi Maryam ta yi ta ce. "Kada ki damu ba bu abin da ya same ni, yanzu ina cikin ƙoshi lafiya kin ji. Amma me ya sa na ganki a nan ke ɗaya?, keda waye ku ke a nan?".

Amsa Du'a ta ba ta da cewa. "Ba bu kowa Ni kaɗai ce hanan wajan". Tana kaiwa nan ta ja hannun maryam sannan ta nufi kujerun da ke garden ɗin da ita.

sai da suka isa wajan sannan Du'a ta zaunar da Maryam ta ce.

"Maryam ina so na yi miki wata tambaya. Shin mutum yana iya zama maciji koh kuwa karya ne?".

"Mamaki ne ya kama Maryam jin abin da Du'a ta furta. Amsa Maryam ta bawa Du'a da faɗin. "Kin taɓa ji koh koh ganin inda mutum ya zama maciji? Duk wacce ma ta fada miki cewa mutum yana iya rikiɗa ya koma maciji toh karya ta ke domin tatsuniya ce kawai bah wani abu bah. sai dai na taɓa jin wani labari da ummata ta taɓa bani akan wata macijiya".

Da sauri Du'a ta kalle ta sannan ta ce. "faɗa min dan Allah ina so na ji".

Kallon ta Maryam ta yi ta ce. "Me ya sa na ga kin bi kin damu? Ki bari bah yanzu bah
, kinga yanzu asuba ce, kuma kinga ya kama ta muje mu ɗauro alwala domin gabatar da sallah".

Riƙe mata hannu Du'a ta yi hawaye na sauka kan kun cinta ta ce. "Inaso ki fada min dan Allah, wannan abin abu ne da ya shafi rayuwata gaba ɗaya, ina so na san ko mai ga me da macizai dan Allah". Ta faɗa tare da haɗa hannayen ta guri guda.

"Ni wallahi ban san ta ina zan fara baki labari bah Du'a. kiyi haƙuri nan gaba za ki san ko mai ga me da macizai tun da aka ki ke so". Cewar Maryam.

"Shi kenen Maryam tun da baza ki faɗa min bah, zan samu masana wanda suka sani na san za su faɗa min".

"Kuma sannan dan Allah da ga yanzu mu daina tafiya tare, saboda ƴan ɗaƙin mu gaba ɗaya aushi na suke ji akan abin da ya faru da ke ɗazu".

Murmushi Maryam ta yi sannan ta ce. "Duniya kyakyawan guri ne, guri ne mai matuƙar kyau mutanen ciki masu kyawawan zuciyoyi ne, dan aka ki dunga kai zuciyar ki nesa kada ki bari sheɗan ya ci galaba a kanki".

Kallon ta Du'a ta yi tare da faɗin. "Ta ya ya gaba ɗaya mutanen ciki suka zama gaba ga masu kyawawan zuciyoyi? Duda cewa koh wane ƙarni sai an samu azzalumi koh sheɗani, shi ne kuma ki ke cewa masu kyawawan zuciyoyi ne, dan Allah kiyi shiru ki rabu rani".

"Da ace kowa addini ɗaya ya ke yi a wannan duniyar, da ba za'a samu kafirai bah, da kowa sai ya fi samun ƴancin kansa". Amma yanzu aikata zunubai da alfasha sun yawaita, Sheɗanci yanzu sune suka zama ruwan dare a cikin zukatan mu".

Murmushi Du'a ta yi tana mai cewa. A duk lokacin da Sheɗanci ya kai makurar tsananta, adalci ne kaɗai ke iya yin maganin sa, kamar yadda idan duhu ya mamaye rayuwar ɗan adam toh haske ne ke iya yin maganin wannan duhun".

"Duda cewar a makarantar nan ina ji kamar akwai sheɗanu, amma ni samm bazan yi wani abu a kai bah domin bah abin da ya shafe ni bane, amma da ina da halin dakatar da su da kuwa ba bu tantama sai na kawar da su".

Murmushi Maryam ta yi ta ce. "Koda ya shafe ki ma ba za ki iya bah, keda bah kowan kowa bah shi ne za ki ce wai za ki dakatar da sheɗanu makarantar nan, kuma bara kiji na faɗa miki, a makarantar nan ba bu sheɗanu. dan aka ki dinga kiyaye harshen ki dan Allah domin ba bu wanda ya san me zai zo ya biyo baya".

Girgiza kai Du'a ta yi ta ce. "Koh kare ya zama sarki, toh kura ta fi karfin haraji. Idan na faɗi abu toh ki yarda cewa sai na yi, a ƙauye mu har dajin da ba bu wanda ya ke iya shiga ta fito a raye na shiga kuma na fito batare da na ji koda kwarzane ne".

"Ƙauye da birni Du'a suna da banbamci, ke ƙauye ki ka sani bakisan birni bah, abin da ki ke gani a kauye bah lallai ki zo birni ki tarar da shi bah, aka zalika abin da ki ke gani a birni babu tabbacin ki iya gani sa a ƙauye".

"Ni Allah na tuba ma daji nawa ne ban shiga bah, koda yaushe a makarantar nan muna cikin zuwa excusion, kuma ba bu inda muke zuwa sai daji, domin samo magani cututtuka. Amma bah gashi bah ba bu abin da ya same ni".

"Shi kenen" Du'a ta faɗa. Tana kaiwa nan ta miƙe tsaye tare da nufar cikin hostel. Bin bayan ta Maryam ta yi da kallo tare da sakin murmushi ta ce. "Allah ya yaye miki Du'a".

Tana kaiwa nan ita ma ta miƙe tsaye tare da bin bayan Du'a.

Ƙarfe takwas ya yi musu a cikin hostel, kafin daga bisani suka fito cikin shigar su ta alfarma. Sanye Du'a ta ke cikin abaya milk colour wanda umma ta aiko a ba ta.

Kayan bah ƙaramin kyau ya yi mata bah. Gaba ɗaya ɗalibai idanuwansu akanta.

Murmushi Maryam ta yi ta ce. "Du'a kinga yadda ɗalibai maza da mata suke binki da kallo?".

Amsa Du'a ta bata da cewa. "Wannan su ya dama, sun daɗe basu kalle ni bah, ni buri Na yanzu shi ne muyi sauri mu isa inda Ahmad ya ce mu haɗu dan wallahi bana son koma wa ƙauye" ta faɗa tare da fito da sarƙar ta daga cikin kayan ta.

Zaro idanu Maryam ta yi ganin sarƙar da ke wuyan Du'a. Baki na rawa ta ce. "Du'a ina ki ka samu wannan sarƙar? Na tabbata wannan sarƙar lu'ulu'u ne kuma zai kai makudan kuɗaɗe kuma naga kamar harda tambarin masarauta a jiki. Du'a a ina ki ka samo shi?"

Kallon sarƙar wuyarta Du'a ta yi sannan ta saki murmushi ta ce. "Wai kinq nufin wannan sarƙar? Toh ai wannan sarƙar ta daɗe sosai. Inna ta fe min mamata ce ta bani kyautar sarƙar, nima tashi nayi naga sarƙar a wuyana".

Bin ta Maryam ta yi da kallo sannan ta ce. "Du'a kuma kin tabbata ke yar ƙauyen gembiza ce? Dan idai har wannan sarkar naki ne kuma mamanki ce ta baki, Toh bani da tantama kin haɗa jini da sarauta, tabbas kina da halaƙa da jinin sarauta".

Kallon baki da hankali Du'a ta bita dashi ta ce. "Kinsan me ki ke faɗa kuwa Maryam? Ni da aka haife Ni can cikin ƙauye shi ne za ki ce na haɗa jini da sarauta, sai dai inaga kece ki ka haɗa jini da sarauta bani bah".

Taɓa ta taji Maryam ta yi. Saurin kallonta Du'a ta yi ta ce. "Mene ne?". Nuni Maryam ta yi mata da ɗan yatsarta.

Bin ɗan yatsar Maryam Du'a ta yi da kallo, zaro ido ta yi ganin yadda jama'a suka taru guri guda, gefe ɗaya kuma HOD da sauran lectures ɗin makarantar ne zazzau ne. Provost kuma na zaune gede ɗaya, yayin da kowanensu ya ƙagu ya ji mai zai fito daga bakin Ahmad.

Gaban Du'a ne ya bada wani sauti. Cikin ɗimauce wa ta ce. " Na shiga uku Maryam, kardai Ahmad ya tara su ne don a kore ni daga makaranta? In kuwa aka ne na tabbata tawa ta kare". Ta faɗa yayin da idanuwanta suka cicciki da hawaye.

Jan hannunta Maryam ta yi ta ce. "Dan Allah Du'a ki daina saka ire-iren waɗan nan abubuwan a ranki, in sha Allahu ma ba abin da ki ke tunani bane zai faru kizo muje mu kashe kwarkwatar idanun mu".

Girgiza kai Du'a ta yi ta ce. A'a ni bazan je bah, bana so naje naji abin da zai tayar min da hankali, ke kije kawai ni zan tsaya a nan wajan".

"Dallah can Du'a ki tawo muje ba bu ko mai fah kawai dai kina sawa ranki abin da bashi bane bah, kuma akan bah abu bane mai kyau, kawai ki tawo mu tafi".

Ta faɗa tare da jan hannunta, ba bu musu Du'a ta bita. Sai da suka isa wajan sannan suka tsaya, yayin da Du'a ta ƙagu taji abin da ya sa Ahmad ya tara ɗalibai da malamai a wajan.

Gyara muryarsa Ahmad ya yi sannan ya ce. “Barka da safiya fitattun malamai da sauran mahalarta taron nan. Abin da ya sa ku ka ga na tara ku a nan shi ne saboda, ina so na sanar muku da wata muhimmiyar magana ne.

"Kwarai da gaske ni ne shugaba dake kula da ƙoƙarin ƙungiyarsa akan abubuwan ayyukan ɗalibi da tsarawa, tallafin manufofin makaranta daga dalibai, kasafi kasafin kudi, tsara kasafin kudi, sanin abubuwan da suka shafi ci gaba da suka shafi dalibai, da sadarwa tsakanin malamai / ma'aikata da ƙungiyar dalibai, kuma ni ɗaya nake fafutuka wajan kula da fanin ɗalibai".

"Shi ya sa nake neman alfarma da a bani wanda zai dinga taimaka min a makarantar nan domin aikin ni kaɗai ya yi yawa".
Chapter 15 · 0% Book details