← Book details Rayuwa Da Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 18

Sashe 17

Rayuwa Da Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka Amina ta fashe dashi sannan ta ce. "Toh naji koh da ba za ka karɓi soyayya ta bah, kawai ka amince mu zama abokai nida kai".

Takaici ne ya kama Ahmad ya ce. "Shin ke kurma ce bakya jin magana ne? Na ce miki ba zan iya bah koh. Ke sai na ma tsaya yi miki dogon zance? Maza zo ki fita kafin na ɓata miki rai yanzu".

"Ka sani duk daren daɗe wa saika soni kuma saina sa ka faɗa a soyayya ta". Tana kaiwa nan ta fice da mugun gudu.

Su Jennifer wanda su ka maƙala kunne jikin gini ne su ka gano tawowar ta. Sai da Amina ta isa inda su Jennifer su ke sannan ta fashe da wani irin matsanancin kuka.

Rarrashin ta jennifer ta fara yi sannan ta tambaye ta meyafaru?. Duk abin da ya faru tun daga farko har karshe Amina ta zayyane musu.

Cikin ɓacin rai Jennifer ta ce. Sai yau nasan da cewa Amina bakida hankali, kema in banda abinki kin san da cewa koh mutuwa za ki yi Ahmad Ba zai saurare ki bah. Kuma kina so ki zama budurwarsa amma ki ke tambayar sa ko zaku iya zama abokai kawai. Me ya sa zai zama abokin ki kawai? Kuma ki faɗa masa aka sannan ki sa ran zai yarda?".

Daga sama suka ji muryar Du'a na faɗin. "Kin fara tuntuɓar wani ɗan makarantar nan halinsa? Dana son wancan banzan mutumi, na gwammace in shaƙe da gwada hakan. Idan ni ma ina son ki kuma na sarrafa na nuna miki ƙaramin kore haske kuma ba ki da wayo, kawai na yi watsi da kasancewar ki budurwa ta ya za ki yi, kawai ki manta da shi ki fara sabuwar rayuwa".

Cikin huci Amina ta ce. "Ina ruwan ki dani? Shin an gasa magana da ke ne da za ki zo ki wani saka mana baki?".

Murmushi Du'a ta yi ta ce. "Baku gasa dani bah, amma kawai na faɗa muku magana ne a kaikaice amma idan na fassara muku abin da nake nufi toh ba za ku ji daɗi bah".

Sannan ta ƙara da cewa. "

Ƙaunar namijin da ba ya son ka yana da wuyar gaske, amma ba sabon abu ba ne - wannan yanayin ya haifar da yawancin fasaha a duniya, Abin takaici, idan wani ba ya son ka, ba za ka iya canza ra'ayinsa bah".

"Samun kan wanda ba ya son ka yana yiwuwa gaba ɗaya, Ba yana nufin keda shi ba ku cancanta ba, ko kuma ba ku isa ba. yana nufin gaba ɗaya jininki bai zo ɗaya da nasa bane koh wani abu mai kyau tsakanin ku biyun. Wasu zan basua son mace mara kamun kai koda kuwa ita ce maƙurar kyau a duniya".

"don aka inaga ki dage koh Allah zai sa ya fara sonki". Tana kaiwa nan ta bar wajan.

Tsaki gaba ɗayansu suka ja, yayin da Amina ta ce. "Nasan da cewa saboda ita ne ya ƙi ƙarbar soyyayata, amma mudin nasa aka kawar min da ita daga doron duniya toh komai zai dawo dai-dai.".

Murmushi Jennifer ta yi ta ce. "Rabu da ita kawata, za ta san duk wanda ya ci tuwo damu miya yasha. Sai mun nuna mata matsayin ta a makarantar nan".

"Ke Du'a ina ki ka je tun ɗazu na ke ta neman ki? Shin Ahmad ɗin ne ya tsayar da ke aka kome?".

Amsa Du'a ta ba ta da cewa. "rabu da shi zai san dani ya ke, ba'a min na ƙyale wallahi, saina nuna masa bambancin da ke tsakani na dashi".

Ɗan jimm Maryam ta yi sannan ta ce. "Aa Du'a ki bi komai a sannu, kinga next week muna da exam wanda kuma kowa sai ya biya kuɗi kafin ya rubuta, kamata ai a ce ki fara neman kuɗaɗen da za ki rubuta jarabawa, bawai ki tsaya ki biye wa Ahmad bah".

"Kuma fah Maryam kin kawo magana mai kyau, in sha Allahu ma mi ba zan ƙara shiga harkar sa bah. Kum...

Maganar ta ne ya dakata sakamakon jin sallamar Umar daga bayan ta.
Juyawa ta yi da sauri sannan ta kalle shi ta ce. "Me kuma ya kawo ka nan wajan?".

Kallon mamaki Maryam ta bi Du'a da shi sannan ta ɗaga mata gira ɗaya ta ce. "Shi ɗin wane ne?".

Amsa Du'a ta bata da cewa. " Shiɗin sabon aboki na ne, jiya muka haɗu da shi ya ce yana son mu zama abokai".

"Ohhh masha Allah akan ma ya yi Toh ya ka ke abokin mu". Maryam ta faɗa. Dariya Umar ya yi sannan ya ce. "Wallahi lafiya kalau alhamdulillah, ya karatu da fatan dai hana mai da hankali kan karatu sosai Koh".

Amsa Maryam ta bashi da faɗin. "Eh wallahi karatu sai abin da ya yi gaba, dan alhamdulillah muna mai da hankali sosai".

"Masha Allah aka akeso. Dama na zo ne na yi wa Du'a sallama na tafi. Shi kenen Ni zan tafi sai gobe. kuma ku tabbata cewa kun fara karatun exams yau domin ku tsallake sharrin carry over".

"In sha Allahu zamu yi karatu". Cewar Du'a.
Shi kenan Toh sai goben. Yana kaiwa nan ya shige cikin motarshi sannan ya fice daga makarantar.

Duk abin da suke akan idanuwan Ahmad wanda ya jingina jikin motarsa yana hayyana wane irin azabtar wa zai yi wa Du'a ya ji sauƙin abin da ta yi masa.

Abdul ne ya karaso inda Ahmad ya ke yana mai cewa. "Babban president bada kanka a sare, me aka yi maka naga ranka a bace?".

Kawar da kansa Ahmad ya yi ya ce. "Bana son takura Abdul, ka rabu dani ka yi abin da zai finshe ka, bawai ka tsaya ka dinga tsegumi bah".

Kallonsa Abdul ya yi ya ce. "Ahmad ni ka ke cewa ina maka tsegumi,Ahmad ni". Ya faɗa tare da nuna kan sa. Sannan ya kara da cewa. "Shi kenan Ahmad in sha Allah ba zan sake tambayar ka wani abu wanda ya shafi rayuwar ka bah". Yana kaiwa nan ya bar wajan.

Tsaki Ahmad ya ja sannan ya ce. "Ka ji dashi, shashancin banza kawai".
Wayarsa ya ji ta fara Ringing, dauka ya yi sannan ya shige cikin mota tare da jan motar ya bar makarantar gaba ɗaya.

"Ke Du'a gaskiya Umar ɗin nan yana da mutunci sosai, har namiji ya zo ya ce yana son ku zama abokai bana soyayya bah kinga mutumin kwarai ne. Gashi kyawawa amma fah bai kai Ahmad bah".

Takaici ne ya kama Du'a ta ce. "Ni fa idan muna tare da ke bana son ki dinga ambatar sunan wannan mutumin a inda na ke. Kuma shi Umar ɗin da ki ke magana akai ma ni ban yarda da shi bah wallahi , gaba ɗaya fuskarsa baiyi kalan mutanen kirki bah. Kin san ance, Kada ka yanke hukunci da littafin da murfinsa (don't judge book by it cover)".

"Haka ne Du'a ban musan dame ya zo mana dashi bah, koma mene ne aniyarsa ta bishi". Yanzu muje kawai mu fara shirye-shiryen exam na first semester, Na riga dana faɗa wa umma komai kuma ta ce in sha Allah za ta tura mana da kuɗin".

"Shi kenen" kawai Du'a ta furta. Yayin da kai tsaye suka nufi cikin hostel.

Bah dare bah rana su Du'a suke fafutuka wajan karatun exam. Yayin da suma sauran ɗalibai na course ɗinsu suke karatu sosai. Gefe ɗaya kuma tsakanin Du'a da Ahmad ba bu wanda ya sa ke haɗa ido da wani. Gefe ɗaya kuma ƴan ƙauyen su sun yi fafutuka wajan neman kuɗin da Du'a za ta rubuta jarabawa, aka suka dinga siyar da amfanin gonar su don cika muradin ƴa ɗaya tilo wacce za ta zamo jagoran ƙauyen. Inda a karshe da ƙyar da wahala suka samu suka haɗa dubu amsin kuɗin jarabawa.

Ya Inna wuro ce ta kira Du'a a wayar mai gari sosai suka gaisa da Du'a yayin da Inna wuro ta ce wa Du'a. "Ƴata kiyi min alƙawarin cewa ba za ki faɗi wannan jarabawar bah, idan ki ka faɗi toh ki sani cewa ba zamu kara baki kuɗin karatu bah sai dai kije ki nemi wanda zai dinga biya miki kuɗin jarabawa. Dan aka ki dage sosai dan bakisan irin wahalar da muka sha bah wajan ganin mu fidda wannan kuɗin".

Murmushi Du'a ta yi ta ce. "In sha Allah Inna ba zan taɓa yin rashin nasara bah, a koda yaushe zan kasance cikin yin nasara ne. Dan aka ku kwantar da hankulanku wannan jarabawar kamar naci ne".

Ranar Monday su Du'a suka rubuta jarrabawar su da kwarin gwiwar cewar za su yi nasara a wannan jarabawa.

Yau ne ta kama ranar Friday, wato ranar da jarabawar su ta fito.
Du'a na hango ita da Maryam sun ci hijabi onion colour wanda bah karamin kyau ya yi musu bah, bare ma Du'a wacce hijabin ya yi matuƙar karbarta.

Dafa Maryam Du'a ta yi ta ce. "Maryam ba zan iya karasa wa wajan da ake duba wa bah jarabawa bah, baki ga yadda ɗalibai suka cika wajan bah?. Kuma ni ina tsoro kada naje naga na faɗi, don zuciyata tana raya min cewa banci wannan exams ɗin bah".

"Aba Du'a an ce fah faɗi alhkairy ko ka yi shiru, in sha Allahu ma babu abin da zamu je mu tarar sai alhkairy dan aka tawo muje".

Tana kaiwa nan ta ja hannunta suka nufi wajan. Tsaya wa suka yi ganin sun isa wajan. Dubbuba sunanta Maryam ta fara yi yayin da ita ma Du'a ba ta yi jinkiri bah wajan duba na ta".

Ihuun! jin daɗi Maryam ta yi tans mai faɗin. "Du'a na aye alhamdulillah naci jarabawata duka bani da carry over".

Murna sosai Du'a ta taya ta, yayin da ita ma Maryam ta taya ta neman sunanta a jerin daliban da suka ci jarabawa.

Amma ina sunyi neman duniya basu ga sunanta bah. Hankalin Du'a bah ƙaramin tashi ya yi bah ganin ba bu sunanta. Kallonta Maryam ta yi ta ce. "Kiyi haƙuri Du'a".

Kallonta Du'a ta yi ta ce. "Me ya sa ki ke bani haƙuri kuma?".
Amsa Maryam ta ba ta da cewa indai bski ga sunanki bah toh akan yans nufin baki ci wannan jarabawar bah, kin faɗi Du'a".
Chapter 17 · 0% Book details