Sashe 4
Rayuwa Da Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Share hawayen ta Dua tayi, sannan tace,"kiyi hakuri Inna idan na ɓata miki rai, insha Allahu bazan sake tambayar ki komai bah". Tana kaiwa nan ta miƙe tareda shiga ɗakin da mahaifiyar ta take.
Hawayen dake shirin zubo mata Inna wuro ta share. Sannan ta karkade shimfidar ta, ta kwanta...
Fashe wa Dua tayi da matsanancin kuka, tare da rike hannun mahaifiyar ta tace,"nasan da cewa da idon ki biyu na tabbata ba zaki bari na dinga zama a ɗaƙa bah, na tabbata cewa ke zaki tausaya min".
"Sabo da mene ne za'a ce a koda yaushe na dinga zama a ɗaki har saina kai shekaru ashirin a duniya". Share hawayen ta tayi da bayan hannun ta sannan tace, "wallahi koh mene ne zai faru, saina je wajan shagali shekara da za'a yi gobe". Tana kaiwa nan ta miƙe tsaye tare da shiga cikin ɗakin ta.....
Washe gari da sassafe Inna ta tafi gidan msi gari, batare da ta ɗora ƙarin kummallo kamar yadda ta saba.
Ganin Inna wuro bata gidan, yasa dua fara shirye_ shiryen yadda zata fita daga gidan batareda kowa ya ganta bah.
Ɗaukar mayafin data saba ɗaurawa a fuskar ta idan zata fita tayi, sannan ta nannaɗe fuskar ta da mayafin tayi rawani a kanta da wani mayafin. Sannan ta nufi tsakar gida, cikin sa'a kuwa ta tarar da babu kowa a tsakar gidan, ganin aka yasa ta saurin ficewa daga harabar gidan.
Kallon hagu da damar ta tayi, yayin da take ganin mutanen kauyen na wucewa, kowannen acikin su da shigar da yayi.
ɓadda kama tayi acikin su sannan ta jera dasu suka cigaba da tafiya.
Gaba ɗaya babu abinda kake gani a gidan mai gari sai tarin jama'a da kayan al'adu, gefe guda kuma tukun yoyi ne a jere ba iyaka, yayin da ko wace tukunya akwai abin da ke cikin ta.
Yayin da ɓangare guda kuma, ake ta kaɗe_kaɗe, hana rawa, dama al'adar kauyen kenen, ko wace shekara sai sunyi murnan zuwan ta.. .
Kallon koh ina na gidan tayi, chan ta hango mutane a zazzau ne suna rera waƙoƙin gargajiya. Zuwa tayi daff dasu sannan ta samu guri a kusa da su ta zauna.
Binta mutanen wajan suka yi da kallo, ganin gaba ɗaya shigar ta ya bambanta da sauran yan kauyen, gashi kuma ta rufe fuskar ta, ba damar mutum yaga wacece..
Sosai Dua ke farin cikin samu dama irin ta yau, wai ashe watarana itama zata shiga gidan mai gari. Maganar da ta shiga yi kenen.
Jin karar takun kofaton doki gaba ɗaya suka yi, yayin da gaba ɗaya naga fuskar kowannen su ya sauya daga farin ciki zuwa damuwa.
Sanye gaba daya kansu su yake da rawani, kallo ɗaya zaka musu kasan kasurguman kafirai ne, kuma marasa tsoron Allah.
Magana ɗaya daga cikin su ya fara yi kamar aka. kowa ya bada hankalin shi nan wajan. Yanzu wata ya kare har an shigo wani watan, amma baku biya haraji bah, shin yaushe ne zaku biya.
Kallon su Mai gari yayi yace, "kuyi hakuri zamu biya, abin da yasa kuka ga mun daɗe bamu biya bah shine saboda, wannan shekarar bamu samu amfanin gona bane sosai shi yasa, amma nayi muku alkawari kafin wannan watar ta ƙare zamu haɗa gaba daya mu kawo.
Bamu san wannan zancen bah, cewar daya daga cikin yan jeji. Sannan ya kara da faɗin, "baza mu taɓa barin nan wajan batare da kun biya haraji ba".
"Da bakuda amfanin gona, da baza ku haɗa wannan abun da kuka kira shagalin bah". Karasa inda suke Inna wuro tayi, sannan ta tsugunna cikin gwiwo win ta tare da haɗa hannayen ta guri guda, tace, "ku kara hakuri, baku taɓa zuwa karbar haraji mun hana ku bah. Tabbas abin da zai hana mu bada haraji toh babban abu ne, muna mai rokan ku da kuyi hakuri.
Tsugunnawa gaba ɗaya yan kauyen suka yi, suka shiga basu hakuri yayin da Dua ke tsaye ta harde hannuwan ta a kirji. Yayin da ta bi kowannen su da kallon mamaki.
Kallon Dua dake tsaye ɗaya daga cikin mutanen jeji yayi, sannan yace, "ke har wacece da zaki tsaya a tsaye bayan kowa yana a tsugunne.
Murmushi Dua ta yi, sannan ta kalle shi tace, "ba'a haifi wanda zan tsugunna na bashi hakuri bah akan abin da nasan ban aikata bah, kuma koda mah zan bada hakuri bazan taba iya bawa ku kasurguman kafirai yan jeji hakuri bah".
Wani wawan dariya! gaba ɗaya yan jejin suka kwashe dashi, sannan wanda yake jagoran su ya kalle ta yace, "mene ne na rufe fuska toh, ke yar wace a wannan ƙauyen, shin ba'a taɓa baki labarin mu bane, mu shika kawai muka sani da zubda jini. Kada ki sake ki fusa ta mu, idan kuwa kika fusata mu toh saimun wanke wannan ƙauyen da jinin ku.
Sai dai idan babu rai a jiki na, in kuwa ina nan koh dabba baku isa kuce zaku cutar da ita bah, balle kuyi kokarin cutar da mutum cewar Dua.
Bin Dua da kallo gaba ɗaya mutanen kauyen suka yi, yayin da suke jin alamun nasara a tattare da ita.
Wani mahaukacin dariya ya kwashe dashi!, cike da ɓacin rai ya kalle ta yace,"zan nuna miki misali". Yana kaiwa nan ya dauki kafar sa na hagu tare da ture Inna wuro ta faɗi kasa.
Wani razananniyar kara Dua ta saki!, babu bata lokaci, macizai suka fara fitowa daga cikin ramu kansu, yayin da suka fara nufar gidan mai gari.
Gurnani Dua ta fara yi, babu shiri jikin shugababn nasu ya fara kakkarwa. Yayin da gefe guda Jama'an kauyen suka miƙe tare da cunku shewa guri ɗaya, gefe guda kuma tsoro da fargaba gaba daya ya baibaye zuciyoyin su.
Babu zato suka ga, macizai na tunkaro inda suke, saboda yawan su mah ba zasu irgu bah, cikin kankanin lokaci suka shiga sarar mutanen jejin.
Ihuu! Mutane jejin suka shiga kwalla wa, yayin da kowanne acikin su ya fara gudun ceton kansa.
Gudu suka dinga yi har suka bar gidan mai gari, yayin da macizan suka bisu a baya .
Murmushi Dua tayi,sannan ta karkaɗa hannun ta, ta juya da niyar tafiya. Daga sama taji muryar Inna wuro na faɗin. "Wacece ke?.
🌸RAYUWA DA MACIJIYA 🐍 🐍 🐍
*PAID BOOK ₦400 complt*
kacal babu tsada
*9043687746 Hassana Aliyu Opay bank*
*Evidence of payment*
*2347085977298*
COMMENTS & SHARE PLS
ALKALAMIN
A'ISHA M.B
(Zinariyar Jajirtattu)
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D80k1puBPBn6uJhojKKhK5
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹
*🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍
*PAID BOOK ₦400 complt*
kacal babu tsada
*9043687746 Hassana Aliyu Opay bank*
*Evidence of payment*
2347085977298
*___________________
*Dedicated this page to my fellow members of Jajirtattu writer's association,(J.W.A) Almighty Allah will continue to be guide us, protect us from the hands of devils and remember us In heaven. Muna tare har abada insha Allah🙏🏻🙏🏻*___________________
FREE PAGE 6️⃣⏩7️⃣
WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B 💞
(Zinariyar 🪙Jajirtattu)
*______________________________________* Murmushi Dua ta saki. sannan ta ɗora hannun ta akan ta, ta fara kunce rawanin dake kanta a hankali.
Hatake gashin ta wanda yake baƙi da mugun tsantsi da tsayi ya bayyana. Daga bisani kuma ta fara kunce maya fin dake ɗaure kan fuskar ta. daga karshe tayi nasaran kunce shi baki daya.
Rasss gaban Inna wuro ya faɗi!. Cikin ranta tace. "Wannan yarinyar me take shirin jawo min ne?, meya sa kuma ta fito bayan saida na fada mata cewa kada taje koh ina".
Sosai mutanen ƙauyen ke yabon irin tsananin kyau na halitta da Dua keda shi. Yayin da suke ganin cewa tun da zuka zo duniya basu taɓa gamo koh mafarkin mace mai mugun jarabbaben kyau kamar Dua bah. Bin ta suka ci gaba da yi da kallo, yayin da kowa da abin da yake sawa a ransa.
Motsa leɓen ta Dua tayi sannan tace. "Sunana Dua". nice nan wanda kuka kulle a ɗaki a gidan Inna wuro tsawon shekaru sha huɗu".
Zabura gaba ɗaya suka yi, yayin da gaba ɗaya tsoro da fargaba ya mamaye zuciyoyin su.
Kallon ta Mai gari yayi yace. "Waya baki izinin fitowa? Me yasa kika fito bayan kin san da cewa an hana ki fitowa dai-dai da tsakar gida. "Kin san dalilin da yasa aka ce miki kada ki kuskure ku fito ne?, koh kuwa kin san hatsarin da yake shirin tunkaro ki?.
Amsa Joda ta bashi da cewa. "Ban san dalilin ku na hajiye ni a ɗaki bah, kuma sannan ban san wace cutarwa ce John hatsari dake tun karo inda nake bah ".
"Amma abu ɗaya na sani, "Allah ne mai kare wa, kuma sannan ita kanta abin da kuke ikirarin cewa zai cutar dani bata isa ta tunkari inda nake ba, domin kuwa ina tattare da kariyar ubangiji".
"Kuma sannan ina da yaƙini cewa zai kare ni".
Ba zai bari na cutu ba ".
Takaici ne ya ishi Inna wuro tace. "Kwarai Allah shi ne mai kare wa. "Amma bayan Allah ya kare ka, kaima saika kare kanka".
"misali ki je yaƙi, sai kika ga makiyin ki ya tunkari inda kike da wuka, shin a lokacin zaki ki jira Allah ya kare ki tareda kawo miki agajin sa? Bayan kuma kinada hannun da jiki da zaki iya kare kanki".
Murmushi Dua tayi tace." Har yau, har gobe abu ɗaya kawai zan ci-gaba da maimai ta wa shine. "Allah shi ne mai kare wa".
Mai gari dake zaune kan kujerar sa yace. "Toh yanzu da kika fito, me kika fito yi? Kuma sannan taya lokaci ɗaya kika kwalla ƙara macizai suka fito?.
Karasa wa inda yake Dua tayi tace. "Na fito ne domin zuwa shagalin shekarar da kuke yi, batun kuma macizai ban sani bah, nima kawai gani nayi sun zo, amma ban san daga ina suke bah".
"Sannan kuma dan Allah ina son na nemi wata alfarma". Ta faɗa tana mai maida kallon ta ga mutanen ƙauyen.
"Muna jin ki me cece alfarmar da kike nema?". Cewar mai gari.
Gyaran murya Dua tayi sannan tace."ina so ku bani ƴancina dawo yin rayuwa kamar ko wace mace a wannan ƙauyen".