← Book details Rayuwa Da Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 18

Sashe 5

Rayuwa Da Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bayan nan kuma, tun da yanzu na kammala karatu na a gida, ina son ku barni naje birni na fara makarantar jami'a. Tun da ai kuna so na zama likita".

"Kuma nima wannan shi ne mafarki na, dan Allah kada kuce zaku hanani ". Ta karashe maganar tare da haɗa hannayen ta guri guda.

Ajiyan zuciya kowa ya sauke. Yayin da Inna wuro ta nufi inda Dua take tare da jan hannun ta tace. "Ina mai bada hakuri game da abin da Dua ta aika ta, nayi alƙawarin cewa, akan ba zata sake faruwa bah ".

Mai gari ya kalli Inna wuro yace. "Shikenen zaki iya tafiya da ita, kuma sannan kada ki kara barin ta tayi yinkurin futa, sabo da a halin yanzu rayuwar ta yana cikin hatsari ne".

"Maganar jami'a kuma babu inda zaki je, idan kuwa kikayi yin kurin fita daga kauyen nan, toh saimun yanke miki hukunci kamar yadda dokar wannan ƙauyen ta tanadar wa waɗan da suka bar wannan kauyen ba tare da izinin kowa bah".

"baza mu taɓa zuba ido muna ji muna gani wani cutarwa ya nufi inda take bah. Domin kuwa idan wani abu na cutarwa ya same ta, toh saimun fi kowa shiga baƙin ciki da damuwa. sabo da itace garkuwar da kuma jagora na wannan ƙauyen baki ɗaya".

Wafce hannun ta daga riƙon da Inna wuro tayi mata Dua tayi, sannan ta kalli mutanen ƙauyen tace." Me yasa kuke wasa da rayuwa ta ne? kubar ni mana na samu yancin kaina. Shin dama na bukaci taimakon kune? Tun da nake yarinya baku taɓa barni na fita bah, shin wannan abin da kuka yi min ne kuke tunanin cewa kare ni kuke yi? Koh kuwa a ganin ku bazan iya kare kaina bane? duda cewa ni ba kowa bace, amma karfin gwiwa da rashin tsoro wanda yake tattare dani yafi naku baki ɗaya".

Abin da kuke min samm ba za'a kira ta da kariya bah, domin kuwa babu wani ɗan adam daya isa sauya ƙaddara, duk abin da Allah ya rubuta cewa shi zai faru, toh babu wani dan adam koh Aljani koh kuma maye daya isa ya chanz akan".

"Kuna tsoro kada wani abu ya same ni koh ya taɓa lafiya ta. "Amma abin da baku sani bah shi ne idan Allah yaso koh ina cikin ɗakin ban fita bah, abin da kuke gudun kada ya faru dani saiku ga ma idan na fita ɗin abin bai same bah. " Amma saiku ga abin yazo har gida ya same ni".

"Dan aka ina roƙon kowanen ku da ya barin na tafi birni don karo karatu, duk abin da kuke ganin ina yi duk dan sabo da ƙaruwar mu ne ".

Cikin ɓacin rai Mai gari yace. "Inna wuro maza_maza ki shiga da yarinyar nan ciki domin raina ya soma ɓaci".

Rintse idanuwan ta Dua tayi masu kama dana mage, yayin da taji lokaci ɗaya ranta ya soma ɓaci. A fusa ce ta kalli mutanen ƙauyen sannan ta riƙe kanta da hannuwan ta guda biyu ta kwalla wani ƙara! Wanda ya sanya gaba ɗaya kowa firgita.

Babu zato aka fara iska mai karfi wanda gaba ɗaya ya karaɗe kauyen. Yayin da guguwa ta soma wanzu wa, hadari baƙin ƙirin ya taso ya mamaye ƙauyen.

Yayin da gaba daya ƙauyen tayi baƙin ƙirin, baka iya hango mutanen dake cikin ta sabo da mugun duhun da tayi.

Ganin aka da Inna wuro tayi ya sata saurin jan hannun Dua, tare da dora sarƙar dake wuyar Dua a saitin zuciyar ta.

A hankali Dua ta fara sauke numfashi, yayin da faɗi a wajan sumammiya.

A hankali a hankali garin ya fara washe wa. Daga ƙarshe garin ya washe baki ɗaya.

Ganin yadda suka ga Dua a kwance ya sa su firgita. Yayin Malam liman yayi karfin halin faɗin.

"Abin da muke tsoro shi yake shirin faruwa, domin idan baku manta bah Malam Ali yace damu, "kada mu bari tana fito wa har saita kai shekaru ashirin a duniya". Idan kuwa bah aka bah komai zai iya faruwa".

Miƙe wa Mai gari yayi yace."wannan yarinyar tana da abin al'ajabi, domin wasu baƙon abubuwa nake gani a tattare da ita".

"Hanya yariynar nan mutum ce kuwa?".........

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
COMMENTS & SHARE PLS 🙏🏻🙏🏻🙏🏻
ALKAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D80k1puBPBn6uJhojKKhK5

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹

*🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍

*PAID BOOK ₦400 complt*
kacal babu tsada
*9043687746 Hassana Aliyu Opay bank*
*Evidence of payment*
09130398321

FREE PAGE 8️⃣▶️9️⃣
WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)

*___________________*
dakatar dashi inna wuro tayi, gami da faɗin. "Mutum ce kamar kowa, amma waɗan nan kalubalen da take fuskanta ina tunanin cewa koh aljanu ne da ita ".

Babu zato suka ga ɗaya daga jama'an kauyen ya faɗi kasa, yayinda ya fara shure _ shure kumfa ya fara fita daga baƙin sa.

Hankalin jama'a ƙauyen ba karamin tashi yayi bah ganin yadda wannan mutumin ya fita a hayyacin shi.

Da sauri suka yi kansa tareda ɗaga shi sama. Ririke shi suka yi, yayinda shi kuma yake ƙoƙarin kwace kansa daga gare su.

Kallon mutanen garin malam liman yayi gami da faɗin. "Cutar sa na farfadiya ce ta tashi, kuma a halin yanzu ba muda maganin warakar ta, duk magunguna suna cikin wan nan jejin ne".

Kallon sa inna wuro tayi sannan tace. Toh
"Shi yasa na ke ce daku mu dinga zuwa dajin jarmuna domin samo magunguna amma kuk.......

Maganar ta ne ya tsaya chak sakamakon tsawan da mai gari ya daka mata! Gami da faɗin.

"Abin da ba zai taɓa yiwuwa bah kenan.
Tayaya zamu je dajin da ya zama haramtacciyar wa wan nan ƙauyen. Ke kanki kin san da cewa tsawon shekaru amsin Koh sama da aka ma babu wani ɗan adam da ya isa dora kafar sa da niyar shiga dajin nan, domin kuwa duk wanda ya shiga zai mutu, kuma sannan ba za'a ga gawar sa bah domin aljanu sun yi fata _fata da naman sa. Dan aka kisa a ranki cewa babu wanda yake da zarrar shiga wan nan dajin. Dan aka Allah zai ci gaba da ƙare sa kamar yadda ya ke ƙare sa a da".

Daga sama suka ji muryar Dua na cewa. "Ni zan je sannan na dawo da magani".

Kallon ta gaba ɗaya mutanen ƙauyen suka yi yayinda Inna wuro tace. "Hankalin ki ɗaya kuwa? Dajin da mutum ba zai shiga kuma ya dawo da rai bah, Toh babu inda zaki je kinji na faɗa miki".

Share hawayen dake shirin zubo mata Dua tayi sannan tace. "Ina son mahaifiyata ta samu lafiya. Kuma sannan shima wannan ya samu lafiya".

"Nayi muku alkwari cewa zan shiga kuma na dawo lafiya ".

Murmushin yaƙe Mai gari gami da cewa."indai har kika shiga sannan kuma kika fito lafiya toh na daukar miki alkawarin cewa zaki je birni karatu kamar yadda kika bukata kuma sannan mu zamu biya miki kuɗin makaranta har ki gama ".

Murmushin jin dadi Dua tayi tace."insha Allah zan je na dawo. ina ne hanyar wajan?

Mai gari bai kama ta ace an barta taje bah, mu mene aikin mu? Tana diya mace amma zata je wan nan dajin yayinda mu bamu je bah".

"Aa ku barta taje, tana son ta nuna mana cewa ita ɗin jaruma ce kuma mu bamu san abin da muke bah, dan aka zamu barta taje". Maza taso mu kaiki har wajan.

Miƙe wa Dua tayi, yayinda taga mai gari da sauran mutanen kauyen na nufan hanyar dajin.

Hatake taji zuciyarta ya karaya. yayinda take ji babu sauran karfin gwiwa a tattare da ita. Mazewa tayi yayinda take ji yau koh mutuwa zata yi saita shiga wannan dajin. Kuma sannan mai gari ya cika mata alƙawarin da ya ɗaukar mata na zuwa birni karatu.

Ganin sun yi nisa a tafiya ya sata saurin bin bayan su.
Saida suka yi tafiya mai nisa sosai daga bisani suka isa baƙin kofan dajin.

Tsayuwa gaba ɗaya suka yi yayinda suka maida kallon su kan Dua.

Tsayawa Dua tayi tare da ƙarewa dajin kallo. Murmushi tayi tareda nuna dajin tace. Shin akan wannan dajin kuke jin tsoro? Ni zan shiga kuma sannan zan fito.

Tana kaiwa nan ta isa baƙin dajin, batareda bata lokaci bah, ta sanya kafar ta na dama acikin dajin sannan tayi bismillah daga bisani aka neme ta aka rasa a wajan.

Fargaba da tsoro ne gaba ɗaya ya mamaye zuciyoyin kowannen su. Gefe guda Inna wuro ta haɗa hannayen ta guri guda sannan ta fara addu'a.

Dua bata tsinci kanta a Koh ina bah, sai chan cikin dajin wanda mutanen kauyen kewa lakabi da *Jarmuna*.

Kallo koh ina na farfaɗiyar dajin tayi, yayinda idanuwan ta ya sauka akan kyawawan bishiyun masu ɗaukar hankali da ido. Gefe guda kuma furenni ne a jere babu iyaka sai sheƙi da ƙyalli suke.f

Tafiya ta soma yi babu alamun tsoro a tattare da ita. Taku ɗaya, biyu tayi taji kamar hana binta a baya.

Saurin waigawa tayi taga babu kowa. Hajiyan zuciya ta sauke tareda maida kallon ta gaba.

Wani razannaniyar kara ta saki! Sakamakon harba da tayi da wasu munanan halittu. Fuskar su gaba ɗayan ta Baƙin kirin ne Wanda babu ido balle hanci. Baƙin su tamkar yadda kasan baƙin jakuna, wanda ke ɗauke da gantsara_gantsaran haƙora wanda suka yi matuƙar muni da abin tsoro. Babu abin da ke tsiro wa daga jikin su sai macizai ta koh ina. Yayinda kafafun su babu maraba dana doki.

Babu shiri jiri ya ɗibi Dua ta faɗi a wajan sumammiya.
Aljanun cikin dajin wanda yawan su bazai misaltu bah na ganin akan suka yi kanta a guje tareda malalo da harshen su waje jini na malala.

hadari baƙi ne tashi, yayinda aka fara iska mai karfi. Babu abin da kake gani sabo da duhu gaba ɗaya ya karaɗe dajin.

Saida suka je daff da ita da nufin cutar da ita suka ga haske ya bayyana a jikin ta wanda ya karade dajin gaba ɗaya.
Chapter 5 · 0% Book details