← Book details Rayuwa Da Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 18

Sashe 2

Rayuwa Da Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sosai jama'a kauyen, ke farin cikin sake haduwa da irin wannan ranar da ruwan sama zata zubo a yankin su.
Mai gari yace tabbas wannan babbar kyauta ce daga ubangiji, shekara da shekaru kenen muna fafu tuka wajan neman ruwa, amma Zuwan wannan jaririyar Allah ya sauko mana da ruwan sama, tabbas wannan yarinyar yar sa'a ce Kuma yar baiwa, Zuwan ta wannan garin bah karamin kawo cigaba zai yi bah .
Bamusan Wacece wannan jaririyar bah, kuma bamusan daga ina ta futo bah amma tabbas wanda ta haife ta, ta haifo mana da kwarin gwiwa, sa'a da Kuma kwanciyar hankali.
Hamdalah gabadayansu sukayi, babu bata lokaci, suka koma cikin garin, suna shewa, Tareda fara tsalle tsalle, farin ciki lullube a fuskan kowanne su,
Tara tulun su kowa yayi, suka ajiye a inda ruwa ke zubowa,
Wanka sukayi wa jaririyar, sa'anan suka saka mata kayan Fulani, Wanda suka karbi jaririyar ciff kamar an auna ta.
Washe garin ranar, Ard'o da Kuma makarabban sa suka futa domin yin farauta kamar yadda suka saba,
Daya daga cikin su ne ya hangi, ciyawa tafara tsirowa daga cikin kasan, ihuu ya kwalla, wanda yasa mutanen yankin suka Fara futowa daga cikin mu'alinsu.
Ard'o yace sani meyafaru? Sani yace ciyawa ta Fara tsirowa a gonar mu, shekara nawa kenen, rabonda muga kasar mu a jik'e ,amma yau Kalli ciyawa mah ta tsiro, acikin kasar.
Hamdalah gabadayansu sukayi, suna mai godiya wa Allah,
Ard'o yace, yanzu kenen zamu iya Shiga gona muyi shuka, Allah mun gode maka, shekaru kenen, da gonan nakin suke a bushe, yau Kuma ga gonar mu a jike sharkaff.

Malam liman yace, inda Allah ke ikon sa kenen, babu abunda ya Kama ta muyi sai godiya ga ubangiji, Wanda yasa muka sake yin ido hudu da wannan ranar wanda ya sanya kowannen mu acikin kauyen nan farin ciki.
Inna wuro yaushe wannan matar zata farfado, Kallon matar Inna wuro tayi tace, dije, sanin Yaushe zata farfado wannan bah a hannu na ya rataya bah, ki Bari Allah yayi ikon sa, wannan matar bah Lallai ta farfado nan kusa bah, saboda ta fada doguwar suma
Sai dai aci gaba da kula da ita, acikin wannan bukkar, har sai lokacin da Allah yayi zata farfado.

Dije tace, Tom shikenen Inna wuro, barana tafi, zanje na dora girki, Kallon yarinyar dije tayi tace, Tom Dan Allah Inna wuro a tayamu kula da Du'a. Murmushi Inna wuro tayi tace,

Idan ban kula da ita bah wa kike son ya kula da ita, karki damu dije itama kamar yarmu take, kulawa da tarbiyar da zamu iya bawa y'ay'an mu, aka itama zamu bata, insha Allah bazan taba bamban ta, ta bah da sauran yaran garin nan, ba iya ni kadai bah, har mutanen kauyen nan.

Tom shikenen barana jee, tashi dije tayi ta fuce daga bukkar , bayan fucewar dije, Inna wuro Ta dauki Dua, tareda dora idanuwanta akan yarinyar tace, Dua, na miki alkawarin cewar zaki ga gata iya gata, zaki samu kulawa wacce koda wacce tayi sanadin kawo ki duniya bazata iya baki bah, zan kula da rayuwarki gabadaya. Ina matukar sonki y'ata. Tana kaiwanan ta rungume yarinyar.

BAYAN SHEKARU BIYAR.
Mai gari wannan yarinyar tabbas tana da kokari a boko harda islamiyya, amma abunda yake yawan ziyartar ta , ya fara yawa, ana cikin karatu kawai saidai muga, tana magana ita kadai kuma idanuwanta su sauya lauli su koma Ruwa toka,

Dan jimm Mai gari yayi, yana mai fadin, y'ata Dua zonan, Hatake naga yarinyar da bazata wuce shekaru biyar da haikuwa bah, ta nufa inda Mai gari yake a Zaune, kyakyawa ce makurar kyaun gaske, kana ganinta Kaga cikakkiyar Shuwa. fuskanta a hade, babu walwala a tattare da ita.
Ta karasa inda Mai gari yake a Zaune.

Mai gari yace, y'ata Dua menene ya faru,? Meyasa kike magana ke kadai?
Motsa Dan karamin lebenta tayi cikin muryar, yara tace, Baba zuciyata yana fadamin cewar wani mummunan abu na shirin faruwa a wannan kauyen. Kuma ina iya ganin abunda Bakua gani ,

Inna wuro tace, mee, kike gani? Kallon ta Dua tayi tace, ina ganin Macizai.

Manage page pls
Comment & share
ALAKALAMIN
AISHA M.B (BABY ISHA)

BISSMILLAHI RAHAMANI RAHEEM
🌸RAYUWA DA MACIJIYA 🐍🐍
PAGE 3⃣➡4⃣

WRITTEN & DIRECTED 🔏
AISHA M.B (BABY ISHA)

PEN🔏 IS MIGHTER THAN SWORD🗡

-----------------------------------------
Binta Inna wuro tayi da kallo, Cikeda jin mamakin kalaman ta tace, Joda me kika ce? Macizai fah kika ce, a ina kenen?

Shiru sukaji tayi, cikin kankanin lokaci, jiri ya d'ibeta ta, Hatake ta fadi a wajan sumammiya.
Cikin tashin hankali mutanen kauyen baki daya, su kayo kanta!, daukar ta inna wuro tayi, ta nufi dakin magani da ita

Kwantar da Joda Inna wuro tayi, sa'anan ta yayyafa mata ruwa, babu bata lokaci, Joda ta tashi. Hamdalah Inna wuro tayi,
Babu bata lokaci bacci yayi hawan gaba da ita.

Tashi Inna wuro" tayi, Tareda fucewa daga dakin, bata nufi koh ina bah, sai fadar Mai gari, da sallama ta Shiga, yayinda yan kauyen suka bita da kallo, Damuwa bayyane a fuskokin su ganin ta yasa Mai garin hanzarin fadin ya jikin Joda"? Inna wuro ta bashi amsa da fadin, da sauk'i.

Hamdala gabadayan su, sukayi. Gyaran murya Inna wuro tayi, sannan tace, Mai gari, ina da wata k'ok'an to, Mai gari yace, menene? Inna wuro ta cigaba da fadin, ina tunanin kamar yarinyar nan akwai shafar aljanu a tattare da ita, saboda ba yau aka fara dawo mana da ita bah, yau ace ta suma, gobe Kuma ace ta na sauya kammani .

Wannan abunda yake faruwa da ita, ya kamata munemi mafuta, saboda kar abun nata yayi tsamari, dan naga abun nata kara harzuka yake. Dan jimmm Mai gari yayi, yana mai fadin, toh me kike so ayi Inna wuro, ke da ni da Kuma wadanan mutanen kauyen, munsan da cewar yarinyar nan, bah yar kauyen nan bane, bamusan daga wace ahali ta futo bah, bamusan sanadin dayasa ta fada a wannan mummunan halin bah. Ga mahaifiyar ta mah rai a hannun Allah, tabbas na yarda da maganar ki, amma kuma wajan wa zamuje mune mi taimako.

Malam liman yace, me zai Hana muje Dajin Jarmuna, domin neman taimako. Zaro idanu gabadayan su sukayi, cikin kidima! da tsoro, Malam liman yace, me kika ce, dajin Jarmuna, wanda babu wani bil Adam dazai Shiga dajin nan ya futo, idan ya Shiga, ya Shiga kenen, saidai buzun shi, bashi bah, dajin Aljanu da mayu, dajin Macizai, wannan bazai yuhuba gsk, nidai ban shirya mutuwa bah

Ard'o yace akane Malam liman Nima ban shirya bah, dajin da babu Wanda yake Shiga saboda hatsarin ta, tabbas akwai magunguna acikin dajin nan, da Kuma magani warke kowane cuta, amma babu Wanda yake da zuciyar dazai tunkari wannan dajin.

Khadija wato matar Ard'o tace, wannan gaskiya ne, amma me zai hana muje wajan, Malam Ali, shine kawai zai iya Sanin abunda ke damun Joda,

Mai gari yace, aba khadija, kin manta gabar dake tsakanin mu da Malam Ali, na nasan cewar bah Lallai ya taimake mu bah,
Inna wuro tace, zai taimaka mana, tabbas ina da tabbacin cewar Malam Ali bazai k'i taimakon mu bah.

Kallon dakaransa Mai gari yayi, sannan yace musu, suje su kira Malam Ali, Mai gari na nemansa, yanzu nan. Babu bata lokaci, dakaran nasa suka nufi gidan Malam Ali.

Cikin kankanin lokaci, Malam Ali ya bayyana a wajan, Kallon Mai gari Malam Ali yayi, sa'anan yace, me Kuma ya faru, koh yau din mah, an kara makala min sharri kamar yadda aka saba.

Kallon sa Mai gari yayi, sannan yace dashi, Aa Ali bah aka bane, na sa a kira ka ne don sulhu, inason wannan gabar dake tsakanin mu yazo karshe, Dan Allah, akawo karshen komai a yau

.Murmushi Malam Ali yayi, yana mai fadin, aini komai ya ruga daya wuce a wajena, saidai Kuma Allah ya kiyaye gaba. Inna wuro tace, Malam Ali, abunda yasa Kaga mun taru Hanan, ba komai bane yasa akan, sai Joda, munason mu ceci rayuwar ta, muna tunanin kamar tanada Aljanu .

Murmushi Malam Ali yayi, yace sun kansu Aljanu basu isa sun tunkare ta bah, shin bakusan Wacece wannan yarinyar bah, itadin daya ce tamkar dubu, yanzu yarinya ce bah Lallai kusan wane irin baiwa Allah ya bata bah, amma kijira nan da shekaru, zaku sha mamaki.

Ard'o yace yanzu me zamuyi tadaina
sume -sumen da takeyi, kuma wani sa'in idan tana kuka, saimu ga za aitayin ruwan sama ruwan bazai tsaya bah, harsai tadaina kuka. Menene zamuyi domin ta daina

Malam Ali yace babu wani abunda zamu iya yi akai, kukan da takeyi Hana ruwan sama wannan baiwar tace daga ubangiji, babu wanda ya isa ya karbe wannan.

Kuma ina gani cewar tabbas wani abun al'ajabi zai faru da yarinyar nan bayan shekaru masu zuwa. Amma kuma a halin yanzu naga rayuwar ta yana cikin hatsari, kuma dole Tana bukatar kariya, saboda Joda bah kowace mutum bace, ta bambanta da sauran mutane.

Mai gari yace, Ali menene mafuta yanzu? Me zamuyi Dan kar rayuwarta yashiga hatsari?

Malam Ali ya bashi amsa da fadin, mafuta daya ce, wannan yarinyar za'a ajiye tane a d'aki, wato ina nufin daga yau, ba za'a Kara barin ta, ta futa koda tsakar gida bah, karatu, ci da sha, futsari, komai, zai kasance Tana yinshi ne a d'aki, yayinda za'a yi mata ba aya a dak'in da za'a saka ta., za'a barta ne a dakin na wajan shekaru sha biyar masu zuwa,

saboda ranar da zata cika shekaru ashirin a duniya, ranar abun al'ajabi zai faru wanda koda wasa, baku taba tsanmmani bah, a ranar ne asalin Wacece ita zai bayyana, ikonta, da baiwar ta, zasu habbaka a lokacin ne zata fara yin aikin da ya dawo da ita duniya,

Bazata sarara wa azzalumai bah, sufarta, halittar ta, yanayin ta, zai sauya saboda lokacin zata kasance asalin DU'A dinta.
Cikin rashin fahimtar magannanun shi, Inna wuro tace, bamu fahimci abunda kake nufi bah, Malam Ali, murmushi Malam Ali yayi sannan yajuya ya Kare wa kauyen kallo, yace, na tausaya muku, bazaku fahimta bah sainan gaba.
Chapter 2 · 0% Book details