← Book details Rayuwa Da Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 18

Sashe 12

Rayuwa Da Macijiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh na gani, naga ɗalibai sun tashi, ni kuma bai kai matsayin wanda zan tashi na gaida bah, idan ma mafarki ya ke toh ya farka, dan bazan taɓa gaishe shi bah saidai duk abin da zai faru ya faru".

A hassale Ahmad ya fara tunkaran inda ta ke, babu tsammani Du'a taji saukar maruka kam fuskarta, yana sauke hannunsa ita ma ta ɗaga nata hannun.

*TUNATAR WA......, Free page ya kusan kare wa, fan's ina fatan Allah(SWA) ya hore muku ya baku ikon biyan kuɗin wannan littafin Naira ₦400 complt babu tsada, ki siya ki mori karatun ki cikin kwanciyar hankali*.

COMMENTS & SHARE PLS 🙏 🙏 🙏
ALKALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar 🪙Jajirtattu)

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹

*🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍

*PAID BOOK ₦400 complt*
kacal babu tsada
*9043687746 Hassana Aliyu Opay bank*
*Evidence of payment*
09130398321

FREE PAGE ️️1️⃣2️⃣➡️1️⃣3️⃣
WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)

*_______________________________*
Chak Du'a ta tsaya sakamakon riƙe mata hannu da jennifer ta yi.
Murmushi Jennifer ta sakar ma Du'a, sannan ta ce. "Mene kike shirin aikata wa? Wai da niyarki ki ɗaga hannu sannan ki maresa? Toh ki sani duk wanda ya yi yinkurin akan sai ya fuskanci hukunci, dan aka kema dole ki fuskanci hukunci".
Cike da ɓacin rai Ahmard ya kalli Du'a ya ce. "Da tunanin ki ki ɗaga hannu ki mare ni? Har yanzu baki san waye ni bah Koh? Toh ki jira kiga abin da zan aikata yanzu a wajan nan".

Yana kaiwa nan ya ja mayafin ta sannan ya riƙe hannunta ya fara jan ta. Ƙoƙarin kwace kanta ta ke amma akan ya cutura. Ganin dai da gaske waje zai kai ta ya sata fara bashi haƙuri. Shiko Ahmad kamar ma bai san tana yi bah.
Sai da ya kaita tsakiyar makarantar ya yin da dalibai daga kowane department suka fara fitowa daga classes ɗin su.
Zama ya yi akan mota, ya yin da ita Du'a ke tsugunne a kasan wajan. Ganin dalibai sun zagaye su ya sashi sakar mata murmushi.

Ganin jama'a sun taru waje ɗaya tare da kewaye wajan ya sanya su Abdul suka karasa wajan.
Kallon ɗalibai makarantar Ahmard ya yi ya ce. "Wannan da kuke gani ta raina muku shugaba sannan ta daga hannunta da zimmar mari na".

Shin wane mataki ya kamata na ɗauka akan ta? Na hukunta ta ne ko na barta taci bulus?".
Hatare gaba ɗaya ɗaliban suka haɗa baki wajan cewa . "A hukunta ta".
Ku kan da Du'a ke riƙe wa ne ya subuce mata. Ya yin da ta fara ku ka hawaye na zarya kan fuskarta.
Babu zato suka ga gaba ɗaya garin ya yi duhu, ya yin da hadari ya ta shi a sararin samania tare da iska mai karfin gaske.

Da mamaki gaba ɗaya suka kalli sama ya yin da suka yi matuƙar mamaki ganin lokaci ɗaya hadari ya ta shi. Babu zato suka ga an zuge da ruwan sama mai matukar yawan gaske.

A ta ke ɗalibai suka fara komawa aji da sauri. Ganin aka ya sa Ahmard sauƙowa daga kan motar da ya ke kai sannan ya shige cikin mota sannan ya figi motar tare da barin wajan.

Da sauri Maryam ta isa inda Du'a ta ke sannan ta ja hannunta da zimmar ɗaga ta sama. Fizge hannunta Du'a ta yi sannan ta ce. "Bana so ki rabu dani, harni zai ci wa mutunci, ni zai tarawa jama'a sai kace wacce ta yi sata a kasuwa, tun da har ya kuskure ya yi min wannan cin mutuncin wallahi saina nuna masa cewa Allah ɗaya ne"

"Zan nuna masa bambancin ƙauye da birni. Ki tafi kawai ki barni a nan wajan".

"Ta ya ya zan tafi na barki a nan Du'a? Kema kin san ba zan iya tafiya na barki ke kaɗai a nan wajan bah, kizo mu koma class, kada ki bari professor's su zo su gan mu a nan wajan". Maryam ta ƙarashe maganar tare da jan hannunta.
"Ki rabu dani!". Du'a ta faɗa cikin daka tsawa.

"Shi kenen Du'a zan barki kamar yadda kika buƙata". Maryam na kaiwa nan ta shige cikin class.

Ruff da ciki Du'a ta yi sannan ta ci gaba da rusa ku ka. Daga sama ta ji muryar mutum a kan ta yana faɗin.

"Barkan ki dai kyakkyawar sura, mene ne ki ke yi a cikin ruwan sama kuma? Bai kamata a ce kyakyawa irin ki tana cikin ruwa bah, ki ta shi kada ki bari zazzaɓi ya kama ki". Saurin ɗago da kan ta Du'a ta yi sannan ta ɗora a kan sa.

Motsa leɓenta ta yi sannan ta ce."wane ne kai? Mene kake bukata daga waje na? Shin waya turo ka domin ka cutar dani?".
Tambayar da ta shiga yi masa kenen.

Murmushi ya yi sannan ya kalle ta ya ce. "Babu wanda ya turo ni kuma bawai na zo ne don cutar da lafiyar ki bah".

Koda ma zuwa ka yi don cutar da lafiyata toh akan ma ba zata faru bah, don ka ma cire a ranka cewa zaka cutar dani domin babu wanda ya isa kwatanta akan". Cewar Du'a.

"By the way ni sunana Umar habib harun ne, kuma ni ɗin ba kowan kowa ba ne, nima ɗan makarantar nan ne kamar ke ɗin nan, jiya na ga lokacin da shugaban ɗalibai na miki magana kina mayar masa, akan yasa naji tabbas tun da har ki ka iya yi wa shugaban ɗaliban makaranta magana ba tare da wani tsoro koh fargaba bah, ya sa naji cewa koma waye ba zaki kyale ba".

"Shi ya sa nake so kiyi min wani taimako".
Kallonsa Du'a ta yi ta ce. "Mene ne?".
Amsa Umar ya bata da cewa. "Ina so na zama abokin ki, mu kasance tare koh ina duk abin da baki gane bah a boko zan fahimtar da ke, kuma ina so ki yarda dani cewa bah cutar da ke na zo yi bah".

"Shi kenen na ji amma da sharaɗi". Kallonta Umar ya yi sa'annan ya ce. "Faɗa min mene ne sharaɗin? In sha Allahu zan bi kuma zan kiyaye".

Tashi Du'a ta yi sannan ta nufi garden ɗin makarantar. Ganin akan da Umar ya yi ya sa shi saurin bin bayanta.

Zama Du'a ta yi daga cikin kujerun da ke wajan ya yin da shi ma ya zauna ba tare da tsoron abin da zai biyo baya bah.

Kallonsa Du'a ta yi ta ce. "Kace sunanka Umar koh"? Amsa umar ya bata da cewa. "Eh".

"Shi kenen sharaɗin dama shi ne abota ni da kai ta tsaya a iya abota kawai banda soyayya, domin babu abin da na tsana a duniyar nan sama na ji an furta kalman soyayya a kusa da ni bana sonta dan aka a tsaya a iya abota".

Murmushi Umar ya yi sannan ya ce. "In sha Allahu ma a iya abota zamu tsaya, nida na ke da tawa budurwar me kuma zan yi da guda biyu".

"Karki damu nayi miki alƙawari iya abota ce kawai zata haɗa mu da ke banda soyayya, amma dan Allah ina so tun da yanzu kin ɗauke ni a matsayin aboki kuma ɗan uwa, kuma a matsayin aboki nake so na faɗa miki wannan magana. Kuma maganar ita ce ina so kije ki bawa Ahmard haƙuri dan Allah".

A ta ke fuskar Du'a ya koma daga walwala zuwa ɓacin rai. Lokaci ɗaya ta tuna da irin cin mutuncin da ya yi mata ɗa zu, cikin jin aushin maganarsa ta ce.

"Bazan je bah, Allah ya kiyaye na je na basa haƙuri sabo da shi ɗin autar maza ne zai sani na je na basa haƙuri, ai koh da me ya ke yawo a makarantar nan bai isa na je na basa haƙuri bah shi ɗin banza shi ɗin wofi".

Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "Du'a ina da dalilin da ya sa ki ka ji na ce aka, wallahi Ahmard bah kunya ce ta ishe shi bah, a makarantar nan kusan ɗalibai amsin ya sa aka kora, kuma ɗaliban yawancin su mata ne kuma sabo da sun ce suna sonsa ne ya sa aka kore su daga makaranta".

"Shi ya sa ma babu wacce ta ke tanka masa a makarantar nan, indai ya yi magana ba'a ja hatta malamai sha yinsa su ke, indai har bakyason ki kunyatar da kanki da kuma iyayen ki toh dan Allah ki je ki ba shi haƙuri, in ba aka bah zaki sha baƙar wahala".

Ajiyan zuciya Du'a ta sauke ta ce. "Gaskiya wannan anyi shedani kuma mara tunani, aka kawai dan mata sun ce suna sonsa sai ya fara koransu sai kace ubansa ne ya gina makarantar, shi kenen in ba dan nayi wa yan ƙauyen mu alƙawarin cewa zan zamo musu garkuwa wacce zata dinga yi musu magani idan na zama likita bah koh, da Allah ba zan ba shi hakuri bah sai dai duk abin da zai faru ya faru".

Tana kaiwa nan ta miƙe tsaye tare da nufar inda department ɗin su ya ke. Bin ta Umar ya yi da kallo sannan ya saki murmushi.
Ciro wayar sa ya yi daga aljihu sannan ya yi dialling ɗin number wacce gaba ɗaya number bata yi kama da ta Nigeria ba.

Kira ɗaya biyu aka ɗaga, lankwasa kafa ya yi ya ce. "Yallabai na fara aikin kamar yadda ka umarta, ta ruga da ta bani haɗin kai yanzu shiga jikin ta zan yi sannan na sace ta tare da kawo maka ita fada".

Daga ɗayan ɓangaren aka ce. "Shi kenen abin da nake so kenen, amma ka tabbata baka cutar da ita bah, bana so koh kwarzane ta ji, idan har kayi mata wani abin toh ka tabbata ba zan kyale ka bah saina hukunta ka, domin ita ce goben wannan masarautar".

"Sannan ka binciko min mahaifiyarta naji ance tana wani kauye kuma sannan na ji an ce tana raye har yanzu. duk inda ta ke ka saka yaranka su bazu koh ina su nemo ta, domin ta dawo inda tushen ta ya ke ".
Chapter 12 · 0% Book details