← Book details Raunin Macce Baya Hana Daukar Fansa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 17

Sashe 16

Raunin Macce Baya Hana Daukar Fansa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmunshin manya yayi maicikeda fassarori kala-kala yace"wannan maganar dik shirme ne bayan ni bazata rasa maƙiyaba ni bansace ta ba kuma bansan da labarin ba saida nagani A medi'a nayi matiƙar baƙinciki akan hakan saboda ita mutum ce mara tsoro sannan ga gaskiya inafatan allah yaƙuɓutar da ita dik ma inda take kuma za'a cigaba da bincike insha Allah wassalamu Alaikum nagode"""

Ɗanjarida yace"wa'alaka salam Ameen ya Allah to jama'a anan muka kawo ƙarshen wannan tattaunawar"

COMMENTS AND SHARE

My whatsApp number 09030835117

OR

07031012948

*(ALƘHALAMI🖊️ YAFI TAKOBI⚔️)*
[09/11 7:55 am] 🥰Mujaheedah🥰 (MATAR MLM): *RAUNIN MACCE BAYA HANA ƊAUKAR FANSA-*
Page 93 to 94

*STORY AND WRITEN BY ✍🏼 🥰Mujaheedah🥰 (MATAR MLM) HEEDAH HAYDAR OTHSMAN-*

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌️*

9/11/2021 NOVEMBER TUESDAY

Hasken da yama idanta yawa yasa tafara ƙoƙarin buɗesu Amma inatakasa saboda hasken yama idanta yawa

Kujera Aka ajemai yazauna daf da ita yace"kiɓuɗa idanuwanki kiganni mana magana nazoyi dake"

Dakyar ta iyabuɗe idanuwanta kan Alhaji garba tasaukesu cikin muryar galabaita tace"dama kaine kasa aka satoni"

Dariya yayi yace"ƙwarai kuwa nine bari nabaki wani Albishir dafarko nagano saƙarku keda hjy marwa kuma itama tanacan tana ƙarɓar nata hukuncin sannan nasan Anwar yarona shine wanda zaki Aura yanzu idona nakanshi dazar naga yasoma munafuntata to zaban saurara masaba saina kasheshi albishir nagaba naje kotu ƙiris yarage a watsar da case ɗin amma ƙawarki tadage abaku 4 days yanzu saura 3 days mukoma ammafa kisani ko yanzu badake zamu koma ba kuma wannan komawar ni keda nasara zanmiki abu ɗaya kibani wannan plash ɗin inhar kinason numfashin ki yacigaba da bugawa"

Murmushin wahala tayi kafin tace"ban damu dakama Anwar komai ba amma nadamu akan marwa kada kasake wani abu yasameta plash bazan bayar ba kuma insha Allah saina kaika kotu sai anyankema hukunci kuma na tabbata yanzu haka ana bincike akanka kuma za'a gano inda kaɓoyemu""

Alhaji garba yace"kaji sakarya na gayamiki ban bar wata kafaba kinga wannan, vide'on zantawarsa da ƴanjarida yanuna mata yacigaba dacewa" dik Abinda Alhji garba yanema tofa saiya samesa koma mene kidaina gardama kibani plash ɗin kona kasheki anan"

"koda nabaka nasan saika kasheni bazaka barni ba to gwanda nasanma banbaka ba dole Asirinka yatona sai ka walaƙan....."
Zazzafan marinda tajine yasata haɗe maganarta batare da taƙarasa ba

Mari 4 yamata kowanne gefe kuma marin zazzafa saida jinta yaɗauke naɗan wani lokaci kafin tadawo hayyacinta bakinta haɗi da hancinta sai zubda jini suke

(((WAYYO KUNA ENA FANSSS HAYAT??? KUNAGANI KUWA GASKIYA NIKAM TABANI TAUSAYI AI DOLE NATARFA ƘWALLA😁)))))

Cikin zafi Alhaji garba yafara magana yace" dik wannan A zabar bai mataba kuɗan horata na kwana 2 kafin nadawo amma kada kubari tamutu"

Fuuuuuu yafice cike da ɓacin rai

Duguja yatsuguna gabanta yace" ki hutar da rayuwarki muma ki hutar damu kibada wannan plashi ɗin kawai kinji ƴar chiika"" yaƙarasa maganar yana shafar fuskarta

Tofa masa yawu tayi cikin ƙarfin hali tace"kada kasake taɓani da wannan ƙazamin hannun naka kuma bazan bada plaah ɗin ba kuyi dik abunda zakuyi""

Ran duguja yaɓaci sosai shima wanketa da mari yayi saina yakoma kan kujera yazauna yace" yanzu ko zakiga abinda zanyi" garwashi maza kaje kaɗebo kayan aiki'

Garwashi da tini yana gun tsaye da to kawai ya ansa yawuce baisan dalili ba kawai yaji tausayinta natsartuwa Aransa.............

TOFA KUNJI GARWASHI YAFARA TAUSAYIH HAYAT DUGUJA YACE AƊEBO KAYAN AIKI KOWANE AIKI XAIMATA???
MUKASANCE A NEXT PAGE DAN ALLAH KUYAWAITA COMMENTS FANSSS KUMA KUYI SHARE IDAN KE KARANTA KITURAMA WASU NAGODE

COMMENTS AND SHARE

My w nob 09030835117
OR 07031012948

*(ALƘHALAMI🖊️ YAFI TAKOBI⚔️)*
[09/11 9:52 am] 🥰Mujaheedah🥰 (MATAR MLM): *RAUNIN MACCE BAYA HANA ƊAUKAR FANSA!-* PAGE 95 TO 96

```STORY AND WRITEN BY ✍🏼 🥰Mujaheedah🥰 (MATAR MLM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN```

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌️*

Garwashi nabashi box ɗin yafice waje

Buɗeshi yayi wasu ƙarafa ne ciki dayawa kamar namai kanikanci

Wani Abu yaɗauko kamar reza sai walkiya yake

A zashi kan igiyar da ya ɗaure hannayenta yayi take igiyar ta tsinke saboda kaifin Abun

A zashi kan hannunta yayi take yamata wani mugun yanka ƙiris yarage yankan yashiga ƙashinta saiya ɗauke

Wani irin wahalallen ihu tasaki kafin tagama jin raɗaɗinsa yaɗauko wani ƙarfen yayi ja sosai saboda yajima cikn wuta kan ɗayan hannunta da ƙarta ya'aza take naman wurin yadare kini yafara tsartuwa wannan karon ihun da tayi da akwai gida kusa dasu to tabbas da anjita luuuuu tayi baya tafaɗi kwance dariya kawai duguja yayi

Jin ihub yasa garwashi shigowa ɗakin dagudu ganinta kwance bata ko motsi ga jini yasashi tsorata yace"kashe ta kayi'"

Miƙewa yayi tareda jansa suka fice waje yarufe ɗakin sannan yace "aiki kawai namata irin na masu taurin kai irinta sumane kawai tayi amma bata mutuba" ficewa yayi
Jiki ba ƙwari garwashi yabi bayansa

®®®®££££©©©¥¥¥©©

Miƙewa zaune mamy tayi cikin firgici tace"nashiga uku ni saratu shikenan sunkashemun ƴata kuka tafashe dashi""

Abba dake gefen gadon zaune yamatso tareda janta jikinsa yafara lallashi haryasamu tanatsu tana sauke numfashi yagane bacci yaɗauketa

Haka anawar tinda yaji ajikinsa anacan ana axabtar da ita sam bacci yaƙauaracewa idansa

AFTAR 2 days

shigowa ɗakin Alhaji garba yayi kwance take kamar ta mutu ruwa masu sanyi sosai yawatsa mata Aɗan firgice tafarka dakyar ta iya miƙewa zaune taɗan jingina da bango

Alhaji garba yace"dube ki dan allah ji yadda kika dawo wai ke baki tausayin kanki ne? kinfison kiyita wahala a kan kimana abinda mukeso? kibani plash ɗin a ƙaro na ƙarshe inagargaɗinki"'

"bazan bayar ba kasani """RAUNIN MACCE BAYA HANA ƊAUKAE FANSA!"""

"Ai ko zaki mutu a wahale dan bawata fansa dazaki ɗauka kaina ke macce ce ba abinda kuka iya face kuka ""RAUNIN KI BAZAI IYA TSINANA MIKI KOMAIBA FACE KUKA""

Duguja"gobe ne zamu koma kotu zansake biyowa kafin naje kada abata abinci ko ruwa a yau gaba ɗai"""

"Angama ogarh""
.....

COMMENTS AND SHARE FANSSS

My whtspp nob 09030835117 or 07031012948

*(ALƘALAMI🖊️ YAFI TAKOBI⚔️)*
[09/11 11:40 am] 🥰Mujaheedah🥰 (MATAR MLM): *RAUNIN MACCE BAYA HANA ƊAUKAR FANSA!-* PAGE 97 TO 98

*STORY AND WRITTEN BY ✍🏼 🥰Mujaheedah🥰 (MATAR MLM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN*

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌️*o

Anwar yashirya tsaf yau zaibada shaidar dake hannunsa

Dikansu sun hallara kotu hardasu mamy

Harabar kotun cike take fam yanjarida mutane dayawa A gun

Saida Alhaji garba yabiya amma ko yanzu takefe yanzunma basu rabu da daɗiba saida yamareta har sau 3 sannan yafito yace "kukasheta kawai""

Yawuce kotu...

FEDERAL HIGHER COURT

shari'ar taɗau zafi sosai

Mamy aka gabatar da tabada shaidar dum gaban Alhaji garba yafaɗi dama waɗannan suna raye??

Bayan gabatar da suna mamy tabada labarin dik yadda abun yakasance hakama daddy yazo yabada shaidar harda Abba yabada tasa da irin yanayin da yatsincesu

Brr, bilky tace"wannan ƙaɗai ya isa kotu tagane Alhaji garba ba mutumin kirki bane"

Objection my lord kamal yafaɗa "wannan baikai hujjar da za'a ɗauramasa laifi ba subada hujjar gani da ido mana""

Alƙali yace"yana buƙatar ƙwaƙwƙwarar sheda"

Anwar bilky tagabatar yabada shaidar gami da faɗar shine"ya mai shari'a ni S.c.i ne nayi aiki A matsayin yaron Alhaji garba nayi hakan ne dan nasamu wasu evidance Alhmdllh nasamu ga waɗannan kuma inazarginsa da shine yasace brr hayat saboda yaci gaba da boye sirrinsa"

Objection my lord kamal yace" wannan maganace mara tushe idan shine yasace ai bazai zuba ƙuɗi akan dik wanda yasamota abashi""

Bilky tace"amma ai yakamata kotu ta kalle vide'o""

Kunnawa Akayi Muryar Alhaji garba da Abba ta bayyana da ma sadda matarsa marwa tayi vide'o komai ya bayyana dumu dumu Alhaji garba da kisan Alhaji Hussain

mamaki ya bayyana kan fuskar mutane shikansa Alƙali shuru yayi

Haya niyar mutane tafara yawa saicewa suke" AKASHESHI AKASHESHI AKASHESHI!!!

Duguja yashigo ɗakin tana zaune daƙyar take fidda numfashi saboda wahala murmushi kawai yake yace" Anbani damar nakasheki amma kafun nan saina yagalgalaki""

Girgiza kai take tana kuka dakyar take matsawa baya "a'a kada kamun komai dan allah"

cire belt ɗin wandonsa yayu tare da zuge belt ɗin wandonsa fizgota jikinsa yayi yana ƙoƙarin yaga rigar jikinta

Runtse ido tayi kuka kawai taje sosai batada ƙarfin iya kare kanta

Ahankali garwashi yasaɗaɗo tabayansa yashigo jikake gammmmmm yabugamasa wani ƙaton icce a kai ihu yasaki Atake yasulale ƙasa sumamme

Cikeda tsoro hayat tabuɗe idanta ganinsa ƙasa tayi sheme shiko yana riƙe da iccen

Matsowa inda take yayi yafar ƙoƙarin kwance ta baki sake take kallonshi kwancetan yayi yace' tashi mugudu kafin ya falka dan bai mutu ba koma shi Alhaji garba yadawo"""

Da mamaki Hayat tace"kana nufin taimakona kayi"?

Kinga ba wannan magar yanzu kawai kitashi mugudu

Da kyar tamiƙe da taimakonsa sannan sukafice

Tafiya mainisa sukayi tafaɗi tace'bazan iyaba bazan iya tafiyarba nagaji""

"kidaure mubar dajinnan""

"wallahi bazan iyaba nagaji dubi ƙafata jini zuba kawai yake""

Yagar rigarsa yayi yaɗaure mata ciwon

Wayar sa yaɗauka yakira police akan akawo masu taimako

Ai ko take sukazo wasu suka ɗauko duguja wasu kuma suka sakashi mota muje Asibiti garwashi yace" a'a Hayat tace muje court ɗin kawai

A kotu kuwa Alƙhali yabada oder sannan yace'" Alhaji garba yayi wasa sosai da hankalin kotu kuma ya salwantar da ƙuɗaɗen jama'a bugu da ƙari yakashe mutane saboda cikar burinsa Aciki harda Alhaji hussain saboda haka kotu tayanke masa hukun ɗaurin kisa ta hanyar tara kuma kotu tabada umarnin A ƙwace dik wasu ƙadarori da yatara bisa zunubi amaidama mai abu kayansa"" kotu. .....

Dafe da bango taƙaraso ciki tana tafi hankalin kowa yadawo kanta

Tace" koda A haka na mutu nayi farinciki dan naga ƙarshenka koba komai ayanzu kagane """"RAUNIN MACCE BAYA HANA ƊAUKAR FANSA!""""""""

COMMENTS AND SHARE FANSSS

*(ALƘALAMI🖊️ YAFI TAKOBI⚔️)*
[09/11 7:46 pm] 🥰Mujaheedah🥰 (MATAR MLM): *RAUNIN MACCE BAYA HANA ƊAUKAR FANSA!*
```LAST Page 99 TO 100```

*STORY AND WRITTEN BY ✍🏼 🥰Mujaheedah🥰 (MATAR MLM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN*

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌️*
Chapter 16 · 0% Book details