← Book details Rashida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 17

Sashe 8

Rashida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce "Amina mene ne a ciki dan Allah wannan ledar ha ka?."

Ta ce "Yaya kawai turare ne da kayan kwalliya fa."

"A a wannan kan ai sai A'ishah me Inna za ta yi da kayan kwalliya."

"Dama kana da ƙanwa amma ba ka faɗa min ba?."

Muhammad ya ce "Eh ai ba ki nemi sa ni ba."

"Eh haka ne yanzun dai sai ka dawo."

"Toh shi ke nan."

Fita ya yi sai tasha ya shiga motar Sokoto.

Muhammad ba shi ya isa ba sai la'asar, ya na shiga gidan ya tarar da A'ishah na hura wuta, da gudu ta ce "Laa Yaya Inna ga Yaya ya zo."

Kayan hanun shi ta karɓa su ka shiga ɗaki ko da Ibrahim ya ji zuwan Yayan shi, da sauri yazo gida shima sai murna ya ke yi.

Gaishe-gaishe suka yi sannan ya fara labarta ma su abin da ke faru a Kano .

Ita kam A'ishah daÉ—i kawai ta ke ji wai Yayanta zai yi aure.

Ita dai Inna Allah ya sanya alkairin kawai ta yi .

Haka dai su ka yi maganganun su har har aka kira sallar magarib.

Ya ce "Tafiya zai yi."

Inna ta ce "Ba dai yau ba ko?."

Ya ce "Inna bai ce na kwana ba fa."

"Toh kace ma sa ni nace sai ka kwana."

Shi dai Ibrahim dariya kawai ya ke wa Inna.

WASHEGARI

Ya tashi tun da safe ya ce "Koma wa zai yi", wannan karun Inna ba ta hana shi ba dan ta san aikin shi .

A'ishah ta ce "Yanzun Yaya sai yaushe za ka dawo"? .

Ya ce "Zan dawo ba da jimawa ba zan kawo ma ki auntyn ki."

Ehu ta saka da murna .

Haka dai rayuwa ta ci gaba da gudana, ciki har da auran Muhammad da Amina da taimakon Amina ya sa mu aikin yi gidan ma da taimakon Amina ya gina shi.

Shiryawa su ka yi shi da Amina zasu ƙauye In da Inna.

Muhammad Ya ce "Amina dan Allah idan mu ka je ki saka baki ko Inna za ta dawo nan da zama."

Ta ce "Toh shi ke nan zanyi maganar in sha Allah."

Kama hanya suka yi sai ƙarfe 2 suka isa zo kaga murna wajen Inna saboda ganin sirikarta ma sha Allah.

A'ishah ta ce "aunty bara na kawo maki abinci saboda na san kin sha hanya."

Hutawa suka yi Sannan aka zo fira da dare Amina ta ce "Inna Dan Allah dan darajar Annabi Muhammad s a w, Inna ki bimu mu tafi tare wallahi gidan ba daÉ—i dayake ba kowa acikin shi amma idan ki ka je zan samu mahaifiya a cikin gidan dan Allah kar kice a a Inna."

Inna ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un yanzun ƙara ta ka kai mata ne shine ka wani kawo min ita ashe dan ku cuceni ne kura ba ni da gari na, kuma kurasa da wa zaku haɗa ni sai da wan da ya fi ni haba dan Allah."

Muhammad ya ce "Haba Inna ni ban San da za ta yi wannan maganar ba ai da ba zan zo da ita ba dan Allah ki yi hakuri, kuma yanzun Inna ya za ki yi."

"Kai É—an nan ka ji tsoron Allah sai ka ce ba da kai aka haÉ—a baki ba."

Amina ta ce "Inna yanzun ba zan samu wannan alfarma ba, shi ke nan amma gaskiya ban ji daÉ—i ba wallahi Inna."

Ke yar nan ai ba yanda na iya saboda kin haÉ—a ni da Allah har da Annabi Muhammad s a w, ai dole zan biku.

Saura ƙiris Muhammad ya rungume Amina a ga ban Inna akan daɗi.

Ya ce "Inna gobe zamu tafi ko?."

Ta ce "A a ni kam ba zan je gobe ba sai dai ku ta fi da Ibrahim da A'ishah."

Amina ta ce "Haba Inna ba yan kin ce min za ki je kuma yanzun ki ce a a dan Allah ki yi hakuri Inna", Amina yi tayi kamar za ta yi kuka ganin haka ya sa.

Inna ta ce "toh shi ke nan na yarda amma ai sai na shirya kaya na ko."

Amina ta ce "a a Inna akwai komai a can."

Toh shi ke nan zan je ban kwana saboda tafiyar tazo min a bazata.

Toh shi ke nan Inna na gode sosai da ki ka yarda.

Maƙota Inna ta je ta yi ma su sai wata rana.

WASHEGARI

Tun da safe su Inna suka kama hanyar Kano, A'ishah kam sai surutu ta ke bu gawa idan mota ta ga ni mai kyau sai ta yi magana da haka dai har suka isa gidan su.

Inna ta ce "Yanzun yaron nan kai ne mai gidan Allah Mustapha da kana raye da yanzun muna tare cikin gidan yaron ka", hawaye ne suka shiga anbaliya a fuskar ta.

Ibrahim ya ce "Haba Inna Dan Allah ki yi hakuri ki dai na wannan kukan ai farin ciki za ki yi saboda Allah ya nuna ma ki ranar da yaronki ya gina gida kuma gaki cikin shi sai ki godewa Allah."

Inna dan Allah ki yi hakuri wallahi mutuwa bata da daÉ—i ko ta tsofa bale yanzun da Allah ya nuna maki cewa yaranki sun girma har gaki a cikin gidan shi dan Allah ki dai na kukan nan kin ji Inna. Cewar Amina.

Muhammad ya ce "Inna mu shiga da ga ciki kinga A'ishah kuka za ta yi, ganin kina kuka dan Allah ki bar haka nan Inna idan ba so kike muma mu yi kukan ba."

Hannun ta Ibrahim ya ja sai cikin gida, cikin gidan ma sha Allah.

Part É—in ta da ban da nasu gidan dai ga baki É—aya part 6, part É—in Amina, part É—in Ibrahim idan ya tashi nashi auran, sannan part É—in Inna, part É—in yaran su na mata da ban na maza da ban, toh É—ayan ban san na meye ba.

Part É—in Inna Amina ta nuna mata sannan ta haÉ—a mata ruwan wanka ta ce "Inna ga ruwan wanka can kije ki yi wankan."

Toh kawai Inna ta ce ta na jin wani sabon al'amari a jikin ta.

Amina in da mijinta ta je ta haÉ—a ma sa ruwan wanka sannan ta ce "Mijina ka je ka yi wanka sai warin dauÉ—a ka ke yi ta faÉ—i maganar ta na dariya."

Ya ce "Amina ban san da wane baki zan gode maki ba saboda wannan abin da ki ka min na gode sosai mata ta Allah ya sa ka da alkairi."

Hmm kar ka manta nima mahaifiya ta ce fa dan na yi wannan abin ai ba komai ba ne, ni dai ka je ka yi wanka dan Allah.

Rungume ta ya yi ya fa ra shafata ni dai na ce nayi nan na rufe ƙofa na yi tafiya ta .

Inna ce ta fito da ga wanka ta tarar da kayan ta a waje ta ce "A'ishah me yasa kika É—auko min kaya eyye."

Kai Inna bani bace aunty ce tace nace idan ki ka zo ki sa ka su .

Humm kawai ta ce.

WASHEGARI

By
Sha'awa marubuciya✍️✍️
WhatsApp number08084277827☎️

RASHIDA PART 6

📝
Amina ta ce "A a Maryam ba du ka suke É—aya ba sannan me su ka yi da kike faÉ—ar wannan maganar akan su?."

Maryam ta ce "Amina Ibrahim ya ci amana ta, Ibrahim ya yaudaran, Ibrahim bai yarda da Allah ba, ku ma wallahi a gidan mu zan kwana dan ba zan kwana ta re da shi."

Muhammad ya ce "Ibrahim me kayiwa yarinyar mutane ne da har ta ke faÉ—an wannan maganar akan ka?."

Ibrahim ya ce "Wallahi yaya na ga ji da rashin haihuwar nan ina bukatar na sa mi Æ´an yarana nima."

Muhammad ya ce "Anya Ibrahim kai ne wai saboda Ibrahim ɗin da na sa ni ba irin wannan na yanzun ba ne, ok idan na fahimta so ka ke ka ƙara aure ko?."

Ibrahim ya ce "Eh.

Maryam ta shi ki je É—akin ki zan je da shi wajen Inna.

Maryam ta ce "Dan Allah Yaya kar ka kai ƙarar shi wallahi bana son na ji ana ma sa faɗa saboda ina son shi."

Muhammad ya ce "Maryam wacce irin mata ce ke mutum na son rabaki biyu ina son nagyara abin kina son lalata shi?."

"Dan Allah ka yi hakuri Yaya cewar Maryam.

Rashid ya ga Umman shi na kuka ya zo ku sa da ita ya ce "Umma waye ya dakeki na rama ma ki?." Duk cikin gwalancin shi ya ke yin maganar.

Rungume shi sosai Maryam ta yi ta na kuka abin tausayi.

Ganin haka shima yafara kukan.

Muhammad ya je ya kira Inna tazo ta tarar da Maryam na kuka ita da Rashid.

Inna ta ce "innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, me zan gani ne amma kai Ibrahim wallahi sai hakkin yarinyar nan ya bi ka, saboda Allah wannan abin ita ke bawa kan ta ne ka san lokacin da na ke yarinya kamar ta?."

Kamin shiru kabani amsa mana.

Ibrahim ya ce "A a Inna."

Ta ce "toh lokacin da nake yarinya kamar ta na shekara 5 ban Haihu ba sai da ga baya Allah ya ba ni Ku, sannan yanzun akan rashin haihuwa wai za ka Rusawa yarinya rayuwa."

Maryam ta ce "Dan Allah Inna ki barshi kawai ya yi auran idan dai zai samu abin da ya ke so kawai ki barshi ba komai, nima ina son na ga yaran shi Allah ya ba ka mace ta gari Allah ya sa auran ne alkairi a gare mu."

Amina ta ce "Amma Ibrahim wallahi ka ban mamaki yanzun duk yadda Maryam ke son ka kai ma kake son ta amma wai za ka yi ma ta kishiya haba Ibrahim."

Maryam ta ce "Amina dan Allah ki dai na faÉ—ar haka ni ina mai farin ciki da auran nan kawai matar da zai auran ce ban san halin ta ba, wallahi Amina kishiya idan ba mai rabaka da mijinka ba ne, ko mai rabaka da lafiyar ka ba ne, ko mai rusamaka rayuwa ba, ai abar su ce ke dai kawai Allah ya sa mai zuciya É—aya ce."
Chapter 8 · 0% Book details