← Book details Rashida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 17

Sashe 16

Rashida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke dallah yiwa mutane shiru kin cika mana kunne da surutu, ya kina fama da warin baki duk kin haukata falon nan da wari" Rashid ya faÉ—a.

"Uban nan kane masu warin baki ba daini ba wallahi."

"Kai kaci Uwarka ka ta shi ka bar nan kamin naci mutuncin ka" Mama ta faÉ—a.

Dariya ya yi sannan
"Allah ya ba ki hakuri Mama, na daina."

Abba ya ce.

"Dan Allah Maryam ki yi hakuri ki ya fe min, sunce Æ´an uwanki ne, kuma sun san duk abin da nake miki dan Allah ki yi hakuri."

"Ba komai Wallahi ai kai mijina ne, yanzun kai ne Uwata kai ne ubana Abban yara, dan haka na yafe maka, ba komai Allah ya yafe mana gaba É—aya."

"Ameen ya Allah 🤲,"

"Mommy ina maganar da muka yi dake ne ban ji Abba sunce komai ba" Rashid ya faÉ—a yana murmushi.

"Dan Allah ka kyaleni bana son surutun nan Please."

"Toh shi ke nan sai anjima zan tuna miki."

Daddy ya ce.

"Maryam shiga da shi ciki dan Allah dan naga yana bukatar kulawa sosai."

"Toh Yaya."

"Wallahi ni zan tafi da shi kamarya ta É—auke shi bayan É—akina yake ba nata ba."

"Yi hakuri Balkisu jeki da shi toh."

"Kuma ku ta shi ku je ku kwanta sai da safen ku."

Kiran Rufa'i aka yi a waya yana dubawa ya ga Nafisat tsaki ya yi sannan ya É—aga kiran.

"Masoyi na barka da dare da fatan kana lafiya?."

"Lafiya ƙalau wai me ya sa kika tsani yin sallama ne?."

"Ayya yi hakuri na manta ne wallahi amma daga yau in sha Allah zan yi sallama."

"Ok shi ke nan ba damuwa meke tafe da ke ne cikin daren nan."

"Wallahi haka kawai na ji ba zan iya kwanciya ba sai na ji zazzaƙar muryar masoyina."

"Ok toh shi ke nan yanzun ai kinji ko?."

"A a ban gama ji ba gaskiya."

Fisge wayar Ummi ta yi tana kiran.

"Aunty ina wuni."

"Lafiya ƙalau amma wace ce ke?."

"Ni ƙanwar sa ce mana, amma nice amaryar da zai yi, bayan auran ku."

"Kutmar ubancan dama kishiya yake son yi mini dan zalunci."

"Eh mana nice ma nan shine nace yabani wayar dan mu saba da juna."

Dariya su Mama ke yi sosai.

"Ai wallahi bai isa ba sai dai a fasa auran nan, kuma gaskiya ba zan iya bar miki shi ba wallahi."

Umma ta fisge wayar ta miƙa wa Rufa'i.

"Zan kwanta sai da safe zan kiraki."

"Dan Allah ka bani minti biyu please."

"Ina jinki."

"Dan Allah wacece wannan da muka yi wayar da ita?."

"Ƙanwa ta ce."

"Laaa Fatima ce amma take haukata ni."

"Ba Fatima bace Ummi ce."

"Ummi kuma yarinyar kishiyar Mommy, amma gaskiya matar nan bata kyautatawa Mommy, kullum fa Mommy ta ce sai da je gun boka, duk ta asirce ku."

Umma mutuwar zaune ta yi saboda wayar a hashfirin ta ke.

"Ke dallah yi min shiru wane ubanki ne, ko uwarki ya faÉ—a miki cewa Umma na zuwa gun boka."

"Wallahi Mommy ka ce ta faÉ—a ba ni ba."

"Toh gobe idan Allah ya kaimu ki shirya da safe zanzo na É—auke ki, na kawo ki, gidan ki wuni, sannan za ki san mai biyan bokayen."

"Toh shi ke nan sai gobe amma ban ji daÉ—in zagi da ka yi min ba" É—iff ta yanke wayar.

Shima sai daga baya ya ji ba daÉ—i.

Haka kowa ya ta shi dan kwanciya.

Rashid mamaki yake wai shi zai auri wannan mitsitsiyar yarinyar.

Wata zuciyar ta ce ma sa ai tana da abin da kake so a jikinta sai mi dan ka aure ta.

Da haka ya bar tunanin har bacci ya yi gaba da shi.

"Wai yanzun ana nufin nace zan aure Yaya Rashid? toh me zanyi da shi wannan ɗan baƙin rai, gaskiya ba zai yiwu ba, bana son shi kuma ba zan so shi ba."

Amma fa yana da halin kirki sai dai rayuwar sa ce bata min ba, haka dai tai ta tunanin ta, ba mai bata amsa.

Kwanciya ta yi ita ma sai bacci.

"Ke dai Hajara wallahi na haÉ—a yaran nan aure kinga dole aikin mu zai yi aikin akan shi", Balkisu ke faÉ—an hakan.

"Hahaha ai dama ki kwantar da hankalin ne kawai ba za ki yi ba, amma ai wannan ɗan sauƙi ne."

"Haka ne kam sai da safe bacci nake ji sosai saboda yau hanawa idona bacci nayi."

"Toh shi ke nan sai da safe."

WA SHE GARI

Kowa ya fito dan cin abinci, kowa dainnin tebur ya nufa.

Mama da Umma kujerar su na kallon juna, Momy da Ma'aruf suma haka sai A'ishah da Rufa'i, sai Rashid da Ummi, Abba da Daddy.

Mommy ta kalli Rashid ta yi murmushi.

Shima murmushin ya yi ma ta dan ya san da magana a bakin ta.

Gyaran murya Mommy ta yi sannan ta ce.

"Yaya Muhammad dama Rashid ne ya ce wai dan Allah ku yi ma sa aure da wuri, wai wallahi ya matsu bai yi auran ba, amma nace ma sa ya bari sai a haÉ—e dana Æ´an uwansa gabaki É—aya."

"Toh pah Rashid dama aure kake so amma ba ka faÉ—a ba tun da sai yanzun, ai sai ka citar da kanka."

Mama da Umma sun san ƙarya ne takewa Rashid amma suka yi shiru dan jin abin da zai faɗa.

"Daddy ai naga aure ba haramun bane kuma dole duk namiji zai buƙaci yin sa, dan nima na buƙata ai ba laifi bane."

"Toh shi ke nan zamu saka ranar nan ba da jimawa ba in sha Allah kaima Ma'aruf ka shirya har ma kai Rufa'i."

"A a su nake ayi na Rufa'i kamin nasu."

"Eh dayake ke ce uban shi ba ai dole za ki sanar damu abin da ya dace da su."

Dariya Rashid ya yi sannan ya ce .

"Abba kai ba za ka ce komai ba ne ka yi shiru ko duk abin da Mommy ta ce shine za ka bi."

"Ai dolen shi saboda shi ya san wacece Balkisu saura kai."

"Kai Rashid ko ba a son ka, Allah ya sa kai aka fara haifuwa, idan ma ba ka yi kudi ba, ka san dangi" Rashid ya faÉ—a yana dariya.

"Haka dai ya kamata, mai gona ya kori biri da kan sa, Rashid kamin ƙarami da sa in sa, saboda a tafin hannun na katashi, amma idan za ka iya ja dani bismillah ka fili ga mai doki."

"Idan babba bai ji kunyar hawan jakki ba, jakki ba zai kunyar kada shi ba, kuma mu zuba mu gani ni da ke Mommy."

"Rashid ya isa haka mahaifiyar ka ce fa."

"Ga mahaifiya ta nan zaune, wannan sai dai sharan mahaifa ba dai mahaifiya ba."

"Rashid nace ya isa kabar wannan maganar haka nan ta isa ka ji ni Ko?."

"Allah ya ba ki hakuri yake mahaifiyata na daina, ba zan sake magana ba sai in ke ce kika ce nayi."

"Toh shi ke nan, ku ta shi zuwa aikin ku musamman ma kai Rashid mai aikin likita, amma kana wasa da aikin naka."

"Ummana yau zan je aiki ai in sha Allah, kawai addu'a nake son ki yi min dan maƙiya suna kallona."

"Toh wacece maƙiyar taka ba dai ni ba wallahi dan ka san karmami, kaikai da dussa duk arzikin gero ne."

"Sanadi ba ya kadan an kashe giwa da sanda, mai zurfin ido tun da wuri ya ke fara barci. Rashid ya faÉ—a.

Ummana sai na dawo zan je asibiti yau sai na dawo."cewar Rashid

"Toh ta shi zuwa sai kun dawo."

"Yaya dan Allah ka siyo min alawa"Ummi ta faÉ—awa Ma'aruf.

"Ba ki da aiki sai shan zaƙi Ummi kuma kinfi kowa sannan ilar shi."

"Eh dai naji kawai ka siyo min alawar."

RASHIDA

Sha'awanatu Faruk diggi diggi ✍️

WhatsApp number 08084277827☎️

22
"Mama kin ji abin da take faÉ—a dai ko?."

"Eh naji kawai ka siyo ma ta ba ruwan ka ."

"Idan ba ka ta shi ba na yi tafiya ta, dan iskanci ka na makarar da mutane, da surutun nan naka na tsiya."

"Mu je to É—an iska kawai."

Tsaki ya yi sannan ya yi tafiyar shi, Mama da kallon ta bi shi har ya ɓacewa ganinta.

"Lafiya wai? Kike kallon yarona haka, kuma kin ƙi yi ma sa magana, ai dacewa ya yi kina magana da shi, saboda dole akwai maganar da ba zai iya faɗa min ita ba, amma ke zai iya faɗa miki ita, dan Allah ki rage wannan abin, ki riƙa yin magana da shi kina tambayar matsalar shi, yanzun kin ga Balkisu ta saka shi a gaba dole yana da maganar da zai faɗa miki akai, dan Allah ki zauna ki tambaye meke damunshi."

"To shi ke nan amma....."

"Dakata dan Allah kar ki ce komai dan Allah kawai ki tambaye abin da ke damunshi, saboda ni na tambaye shi amma ya ce ba komai, kuma ba da gaske yake ba, dan na san idan yana cikin ɓacin rai, kuma na san farin cikin shi."

"Hummmm toh na ji idan ya dawo zan tambaye shi."

"Dan Allah Maman yara ki taimaka ki yi ma sa magana, sannan maganar auren shi da Ummi, idan ba ya so kar ki saka shi dole dan Allah, dan wallahi na ga kamar ba ya son ta."

Da haka suka cigaba da magana, suna cikin magana sai ga Balkisu ta na taunar cingam, ta na musu kallon banza, zama ta yi kusa da Umma ta na dannar hanci, ta na yamutsan fuska.

"Toh pah Balkisu yau wari kike ji ne?, naganki ki na dannar hanci ko kin sa ma mana baby ne", Mama ta faÉ—a amma ta san abin da take nufi kawai ta fakaice ta hanyar wannan tambayar.

"Gaskiya yau falon nan ba daÉ—i kamar ba ayi shara ba, sai wari yake ko dai masu warin ne a zaune a falon."

Umma dai shiru ta yi ta na kallon sarautar Allah yau wai ita ake cewa mai wari to warin mi take yi?, ko dai wulaƙancinne yazo da haka.
Chapter 16 · 0% Book details