← Book details Rashida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 17

Sashe 11

Rashida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amina ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, Ibrahim kai ne wai kuwa gaskiya ba kai ba ne, Ibrahim da na sa ni mai son Maryam sosai."

Maryam da ke ba kin ƙofa ta ce. "Ai na sa ni Ibrahim ba sai ka faɗa masu ba, kuma na gode sosai da sakayyar da kai min."

Cikin kuka ta ke maganar abin tausayi.

Muhammad fita ya yi ya kira Inna ya faÉ—a mata duk abin da ke faruwa.

Inna ta zo ta É—auke shi da mari ta ce "Sha-sha-shan banza mutumin banza, toh yadda ka yi mata nima na san za ka iya yi min shi."

Balkisu ta ce "Wai wane irin wulaƙanci ne wannan, a ga ba na a zo a na ciwa mijina mutunci toh wallahi ba zan yarda ba."

Mari ta ji a kuncenta da sauri ta dafe kuncin na ta .

Muhammad ne ya ce "Duk wulaƙancin ki ya tsaya a kan shi, idan ki ka ce za ki wulakanta, mahaifiya ta a ga ba na, toh wallahi komai zai iya faruwa."

Amina ta yi saurin riƙe shi ta ce. "Haba Daddyn yara bafa muharramar ka ba ce ba fa, kuma har ka iya ɗaga hannu ka dake ta?."

Wayar Maryam ce riƙe a hannun Rashid kiranta a ka yi sai kawai Rashid ya ɗaga kuma bai yi magana ba.

Maryam ta ce. "Dan Allah Yaya ka yi hakuri in dai a kai na ne wannan abin ke faruwa, wallahi na warware sosai jiki na ya ji sauƙi dan Allah mu ta fi."

Ya ce. "Maryam mu je part É—in Inna zan yi magana da ke."

"Toh" kawai ta ce.

Fita ya yi itama Maryam bayan shi ta bi.

Inna ta ce "Ka sa me ni a É—akina ina jiran ka."

Sannan su ka fito ita da Amina.

RASHIDA

PAGE NA 12

BY
SHA'AWANATU FARUK DIGGI✍️
WhatsApp number08084277827 ☎️

12

📝
Tashi ya yi da niyyar fita ta ce "Ina za ka je ne?."

Ya ce "Zan je wajen kiran Inna ne."

Ta ce "Ba za ka je ba."

Ya ce "Toh shi ke nan."

Zama ya yi sai bacci.

Kiran hajara ta yi ta ce "Hajara wallahi bokan aikin shi na kyau, ga shi sai juya dan iskan nan na ke yi, yanzun kuÉ—in sa na ke son na fara É—ibawa."

ÆŠaya bangaren ta ce "Ai Balkisu gara ki juya É—an iska, ai shi ma ya san ruwa ba sa'ar kwando ba ne."

Ta ce "Ke dai bari yanzun haka ana kan wata dirama a gidan nan, kuma ba zan ba shi hanyar zuwa can ba."

"Hahaha kai ƙawata shegiya ce ke wallahi."

Ta ce "Balkisu wai ya maganar Æ´ar iskar kishiyar nan taki ce, har yanzun ta na nan da addu'ar tan ne."

Ta ce "Ai ki barta wallahi ba zan kya le ta ba, kuma ba zan kyale yaranta ba, saboda suma ina jin kamar kishiyoyina ne."

Hajara ta ce "Gaskiya ne kinsan da zafi zafi a kan duke ƙarfe."

"Gaskiya ne kam" cewar Balkisu

Sallama su ka yi.

Amina ji ta yi cikin ta na mata ciwo amma ba ta yi magana ba.

Maryam ta ce "Amina meke damunki ki ne naga kamar ba Kya jin daÉ—i?."

Ta ce "Maryam cikina ne na ke jin yana min ciwo sosai."

Inna ta ce "Ayya ko naƙodan ce?."

Muhammad ya ce "Naƙoda kuma Inna cikin wannan halin."

Amina ta ce "Maryam dan Allah ka ma min na tashi zan je É—akina."

Ta taimakon Maryam Amina ta isa É—akinta.

Tana shiga É—akin cikin ikon Allah ta haihu lafiya.

Maryam da gudu ta yi part É—in Inna ta ce "Inna Amina ta haihu."

Inna ta ce "Yanzun idan kika ji ciwo fa wannan gudun haka."

"Inna wallahi ina murna ne ban san yadda zan yi ba, saboda farin ciki Æ´a mace fa ta haifa."

Muhammad ya ce "Kai Maryam ki rage wannan abin, yanzun idan kika hallaka min Æ´arinya ko yaro fa?."

Cikin jin kunya ta ce "Yaya yi hakuri wallahi ina son Æ´a mace ne sosai da sosai."

"Ya ce "Toh Allah ya baki mai albarka."

Ta ce "Ameen Yaya na gode sosai."

Tashi su ka yi zuwa in da Amina ita da Balkisu su ka tarar zaune.

Balkisu ta ce "Maryam ko baki faÉ—a min ba toh na ji sai hakuri."

"Amma Balkisu yanzun nake da niyar kiranki, kawai dai na kira su Inna ne."

Ta ce "Amma ai na ga kamin ki kai ga resu sai kin wuce ni."

Maryam ta ce "Amina meki ke bukata yanzun?, dan Allah ki yi hakuri kwanciya nake son na yi."

Ibrahim ne ya shigo Inna ta lallai Muhammad ya ce

"Ibrahim Ina ki ran da Inna ta yi ma ne, ko kafi ƙarfin zuwa ne?."

Ya ce "Ni fa wallahi na gaji da wannan abin, kullum ana takurawa mutum."

Inna ta ce "Ai sai ka koma in da ba'a takura ma."

Su Ma'aruf ne su ka shigo É—akin su ka ga jariri, sai Ma'aruf ya ce "Laa Mama waye ya haihu?."

Balkisu ta ce "Ai Mamarka ce ta haihu."

Rufa'i ya ce "Laaa wallahi Mama ta na da kyau sosai."

Rashid ya ce "Umma sai yaushe za ki haifa min ƙanwa ne?."

Umman ta shi ta ce "Yarona sai lokacin fitowar shi ya yi."

Ya ce "Shi ke nan."

BAYAN SATI ÆŠAYA

Anyi suna yarinya ta ce sunan Goggonta A'ishah ma sha Allah.

Har da A'ishah ta zo sunan dan sun dawo da tafiyar ta su ka yi .

A'ishah ta ce "Aunty Maryam wai Aunty Balkisu nan na da hankali?."

Ta ce "A'ishah saboda mii za ki kirata da maras hankali, kin ganki idan Yayanki ya ji ki, toh wallahi sai kunyi faÉ—a tam."

Ta ce "Yanzun aunty Saboda na ce mata maras hankali shine za mu samu matsalar?."

Ta ce "Eh sosai ma."

"Allah ya kyauta" kawai A'ishah ta ce

Amina ce ta kira Maryam ta ce "Ta zo ta karɓi A'ishah."

A'ishah ta ce "Wallahi aunty ni zan karɓe ta, saboda yanzun ba zama na ke ba tafiya zan yi na barki da ita."

RASHIDA

SHA'AWANATU FARUK DIGGI ✍️
WhatsApp number0808427727 ☎️

13

📝
"Toh shi ke nan É—auke ta É—in ba damuwa."

"Yauwa aunty na."

Wata yarin ce tafi toh rike da lemo ta ce "Mama wai ina so Yaya Rashid ne?."

Umma.
"Su Rashid na can lambo."

Mama.
"Ba ki iya gaisuwa ba ne?."

"Na manta ne ina wuni Umma."

Umma.
"Ba damuwa yi tafiyar ki Æ´ar albarka."

Mama.
"Wallahi aunty na rasa laifin me na yi
wa Allah da ya bani wannan yarinyar, bata dubin kowa da idon rahama, aunty wallahi har mahaifin ta bata bari ba, ya yi dukanta har ya gaji ya daina."

Umma.
"A'ishah ki yi hakuri kici gaba da yi mata addu'a in sha Allah za ta nutsu da yarda Allah, ki yi addu'a ki riƙa yawan yin sadaka, shi ma ya riƙa fitar da Zakka in sha Allah,Allah zai cire mata wannan abin."

"Toh shi ke nan aunty na gode sosai, shi ya sa nake son faÉ—a maki damuwa ta saboda kina bani shawara mai amfani."

"Hahaha toh ai nima yarinya tace saboda ai dole zan baki shawara, saboda nima ban san wace irin yarinya zai ban ba ko yaro."

"Na gode sosai Allah ya saka da alkairi Allah ya mayar maki hankalin Yaya."

"Ameen".

Inna su ka ji a bayan su ta na faÉ—in toh mata da miji ai sai ku tashi kuje dubin Balkisu, ta haihu amma bakwa wajen.

Umma ta ce.
"Inna me ta haifa ne?".

Inna.
"Yarinya ce".

"Toh ma sha Allah."

Tashi sukayi dan zuwa in da Balkisu.

"Assalamualaikum".

"Waalaikumussalam".

"Balkisu a she kin haihu bamu sa ni ba, muna can muna shan fira."

Balkisu.
"Ai dole zaku barni ni É—aya tunda ni ba sona ake yi ba daga ke har su Innar."

A'ishah.
"Dakata Balkisu karki sa ke ki zagi mahaifiyata a gabana, dan wallahi na fiki rashin mutunci, idan kika sa ke zagin ta wallahi sai naje har gidan tsofinki naci mutuncin su."

Balkisu kuka ta saka ta ce.
Yanzun A'ishah ni kike zagi saboda nace Maryam ta kawo min ruwa."

Ibrahim.
Ya kwashe A'ishah da mari sai da ta yi tingil tingil za ta faÉ—i.

Umma ta ce.
"Haba Abban yara mene ne haka daga faÉ—an gaskiya sai duka, Inna ce fa take ciwa mutunci, kuma kake sa ran A'ishah ta barta."

Ibrahim.
"Wallahi kema zan É—auke ki da mari idan ba ki bar wajen nan ba."

Umma.
"Ai da ka bala'i wallahi dan ba zan kwanta ka dakeni akan kishiya ba, ko kishiyar wacce bata san darajar mahaifan ta ba bale ta san na mahaifan wani."

ÆŠago hannu ya yi ta niyar sharara mata mari sai ya ji saukan mari a kumatunsa.

Inna.
"Yanzun kana nufin za ka daketa akan Balki?, lallai yau ka nuna min kai ba Ibrahim É—ina bane, saboda Ibrahim É—ina ba ragoh bane."

Balkisu.
"Yanzun kana nufin kyale ta za ka yi marin ka fa ta yi."

Ibrahim.
"Inna yanzun ni kika mara saboda wannan bagi dajiyar Æ´ar talaka?."

Umma.
"Ibrahim yau kaine ke kirana da Æ´ar talaka?, na gode sosai Allah ya saka da alkairi."

Fita ta yi daga É—akin, É—akinta taje ta É—auki mayafin ta tana fita A'ishah da Amina na kawowa.

Amina.
"Umman yara ina zuwa haka, ba dai tafiya za ki yi ba?."

Umma.
"Wallahi tafiya zan yi kuma ba zan dawo ba sai ya ne meni da kansa sannan zan dawo."

A'ishah.
"Haba aunty dama haka ne take so fa kenan kina nufin taci galaba akan ki."

Umma.
"A'ishah Amina ba galaba ta yi akaina ba kawai ina son in ni santa kaina da shi ne ."

Amina.
"Humm haka kika ga yafi maki."

"Eh"

"Toh shi ke nan ki tafi kawai".

Tafiya ta yi A'ishah da Amina sai kuka suke yi.

Amma Maryam Ma'aruf fa idan ya dawo me zamu ce ma sa.

Maryam.
"Dan Allah karki tura min shi, ya yi zaman shi in da kike, ga su Rashid da Rufa'i nan."

RASHIDA

BY
SHA'AWANATU FARUK DIGGI ✍️
WhatsApp number08084277827☎️

14

📝
Ga su Rashid da Rufa'i nan sai ya zauna in da suke.

Cikin kuka ta ja hanun Maryam tana cewa
Chapter 11 · 0% Book details