← Book details Rashida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 17

Sashe 2

Rashida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wallahi Yaya fita za mu yi ne za mu je gidan wata ƙawata ne.

"Ok mu ma fita za mu yi, ko zo muje mu ajiye ku a gidan ko". cewar Rufa'i.

Fatima da A'ishah kam baki har kunne saboda daÉ—i.

Mama ta ce "kai ku tashi ku bar É—akin nan mai ku ka zo yi ne ehhe?".

"Ayya mama yi hakuri ina wuni mun sa me ki lafiya suka faÉ—a a tare".

"Humm." kawai Mama ta ce sannan ta du bi Ma'aruf ta ce "ina za ku ne yanzun wannan wanka haka ko dai an sama mana sirika ne?."

Hahaha "kai Mama sirika Kuma yanzun ai har yanzun yara ne mu. cewar Ma'aruf".

Rufa'i ya ce "Mama ai idan muka samu matar aure ke ce zamu fara faÉ—awa, amma yanzun kin ga yara ne mu yanzun haka Umma ce ta yi mana wanka fa".

Dariya sosai su Ummi ke yi shi kam gogan naku har ya san da re saboda kyau da ya ga Ummi ta kara yi ma sa ya ce ma sha Allah, bai san maganar ta fito fili ba.

Sai ji ya yi Rufa'i ya ce "aboki menene ma sha Allah ko ka samu budurwar ne.

Fuske wa ya yi ya ce "ina ruwan ka É—an sa ido kawai", ya ta shi ya yi tafiyar shi ya yi ko Kaka basu gaida ba suka yi tafiyar su

Su Ummi na a bayansu su ka isa a harabar gidan wajen ajiye motoci suka je.

Rashid ne zai yi Driving saboda ha ka Ma'aruf da Rufa'i su ka koma ba ya A'ishah da Fatima bayan suka shi ga a ka bar Ummi a wa je...

Rashid ya watsa ma ta kallan banza da idanunsa ma su rikitarwa rai a ɗan ɓace ya ce "wai wanne irin wulaƙanci ne ana jiran ki kin share mutane sha-sha-shar banza wallahi sai na yi tafiya na?".

"Am... Yaya ban san in da zan shiga ba ne, kuma Yaya Rufa'i sun shige baya".

"Ai sai ki hau kan su ki zauna banzar yariyar kawai, shi wannan kujerar ba abin zama bane ko?".

Saurin shiga gaban motar tayi ba shiri tun ba gama gyara zamanta ba dan ko marfin motar bata rufe ba yaja motar a tsiyace aiko ta kame shi sosai tana kuka.

Ma'aruf ya ce "haba Rashid idan ka hallaka min ƙanwa fa wanne irin baƙin halin wannan ka yi parking ɗin motar nan wallahi", cikin fushi yake yin maganar saboda sosai hakan ya ɓata ma sa rai.

Parking ya yi ya kama hannun Ummi ya jefar da ita a kasa sannan ya ce "kan wannan jakar za ka É—aga min murya toh wallah..." Bai bari ya Ida maganar ba ya katse shi da faÉ—in.

dallacan ana jaki bayanka ne kuma wallahi ka sa ni duk abin da ya sa mi Ummi sai na rama ma ta sha-sha-shan banza kawai mara imani", ya na faɗan haka ya fita daga motar Ranshi a ɓace.

Rufa'i ma fita ya yi daga motar shima Ranshi ba daÉ—i.

Tashinta ya yi ya shigar da ita cikin gida koda suka shiga gidan a falo suka tarar da su Umma.

Ta shi Mama ta yi ta ce "innalillahi wa'inna ilaihin raji'un mai yasa mai ta ne haka?" ta faÉ—a cikin san jin abin da ya faru.

Amsarta Mama ta yi ai ta na taɓin jikin ta ta ji shi zafi sosai ga Ma'aruf sai huci yake ganin haka yasa tayi shiru har zuwa komai ya lafa.

Rashid ta kira kan yazu ya duba ta sai ya ce ai ba ya gida ya fito Unguwa ne, haka dole Mama ta kira likita ta faÉ—a ma sa abin da ke faruwa ya ce ta bashi minti 30 yana zuwa, dole haka Mama ta cigaba da jiran zuwan likita.

Rashid tafiyar shi ya yi amma zuciyar shi ba daÉ—i.

Aiko likitan bai fi minti 30 ɗin ba yaƙaraso, jikin ta ya duba ya ce zazzaɓi ne mai ƙarfi ya kamata, maganin ya ba ta ya yi tafiyar.

Rashid ba shi ya dawo gida ba sai dare, ya ba shiga ɗakin su ya tarar da Ma'aruf da Rufa'i su na maganar wulaƙancin Rashid saboda ya yi yawa.

"Assalamualaikum"

"Waalaikamussalam" suka amsa ma sa a ta re.

"Ma'aruf kira yaran can su kawo min abinci saboda ba zan iya zuwa dainning ba".

Ma'aruf ta shi ya yi yaje ya kwanta abinshi.

Rashid ya ce "wai ba da kai na ke Magana ba ne ehhe bana son wulakancin Nan fa"?.

Mtsww banza kawai tun da gani É—an aikin ka ba ai dole zan kira ma ka su kuma kasani wallahi-wallahi-wallahi idan yau baka barni na huta ba duk abin da nayi ma kai kaja banza jaki.

Shima kanshi yasan baiyi dai-dai ba dan haka ya shiga bawa Ma'aruf hakuri.

Shi dai Rufa'i sai bin su yake da idanu sannan ya ce "Rashid ka san ba ka yi gaskiya ba saboda ko ba komai Ma'aruf É—an uwanta ne kuma Yayanta kana wulakanta ta a gaban shi, amma baya Mu sa ma ka haka ba ya na nufin jin tsoro ba, a a girmama juna ne amma gaskiya nima yau ka ban haushi sosai.

RASHIDA

BY
SHA'AWANATU FARUK DIGGI✍️✍️
08084277827☎️📱

PAGE NA BIYU 2

📝
Rashid ya ni sa cikin muryar ne man afuwa ya ce "haba Ma'aruf ka yi hakuri dan Allah na san ƙanwar kace, amma wallahi yarinyar ba ta ji ne saboda su Umma duk sun sangarta ta amma dai kayi hakuri ɗan uwana".

Ma'aruf ta shi ya yi ya yi tafiyar shi part É—in Mama.

Shiga ya yi sallama É—auke a bakin sa "Assalamualaikum"

Mama ce zaune ta na lazumi ta amsa ma sa sallamar
"waalaikamussalam"

Zama ya yi tare da cewa "Mama ina wuni"?.

Amsawa ta yi ta ce "kawuni lafiya Ma'aruf"?.

"Lafiya ƙalau Alhamdulillahi" Mama ina Ummi ta ji sauƙi kowa?.

Eh kam ta ji sauƙi sosai ma yanzun su ka fita ina tunanin ko su na part ɗin Ummansu ne.

Toh shi ke nan zan wuce sai da safee.

Da ka ta kaji Ma'aruf mai yasa mai Ummi ne ɗazun saboda lafiya ƙalau ku ka fita a ɗakin nan sai ga shi ka kawo min ita ba lafiya mai ke faruwa ne ka faɗa min gaskiya?.

Mama ba komai kawai kin san shi lafiya ba ya zama a jikin ɗan adam dole ne wani lokacin za ka ji zazzaɓin kamar yadda ta yi ɗin nan, ko dai ma wani ki ke zargi a kai ne Mama ?. Ya faɗa ya na dariya.

Mama ta ce "ok ai na yi tunanin ko ɗan baƙin halin can ne ya dake ta dan nasan halin shi kullum fuska a haɗe".

Ma'aruf ya ce "kai Mama wai mai ya sa ki ke kiran mu da ɗan baƙin rai ne haba ni kam tafiya ma zanyi sai anjima?.

Mama ta ce "au saboda da nace ɗan baƙin rai ne zai saka ka tafiya?.

Tashi ya yi ya ce "Mama zan wuce sai mun haÉ—u a dainnin".

Toh shi ke nan sai na sauko.

Toh Mama sai anjima.

Yana fita É—akin Umma ya shiga a can ya tarar da su A'ishah A'ishah suka haÉ—a baki wajen kiran"Yaya ina wuni?.

Amsawa masu ya yi ya ce " lafiya ƙalau A'ishah ina Umma ne"?. Ya tambaya.

"Yaya ta na toilet ne cewar Ummi.

Fatima sannu ko ansha kyau amma fita ba ta samu ba.

Fatima ta ce "wallahi dai Yaya gashi saurayina ya ce zai zo anjima yaga wanka tun da ban fita ba kaga ko ai su Ummi suka yi asarar wankan su". Ta faɗa cike da shaƙiyanci.

Shikam tuni ya ji kamar ta duka ma sa wani abun mai nauyin gaske cikin jarumta ya ce "to ashe yaran Umma sun girma har samari ne da ku kuna ƙananin nan". ya faɗa cikin nauyin murya.

Ummi ta ce "Yaya wallahi ƙarya ta keyi Bama da samari".

Idan ma suna da samarin mai za ka yi ne ehhe, maganar Umma suka ji aiko saurin É—ago kansa ya yi ya ce "Umma ina wuni"?.

Umma ta ce "ban san in da ya ke ba tashi kabar ɗakin nan tunkan ranka ya ɓaci kazo ka takurawa yara".

Laaaa Umma waye ya ce ya takura mana ne Umma. cewar Fatima.

Fatima karɓi wannan zagin naki ne idan nasake magana kika ce ba haka bane sai na ɓataranki.

Hakuri suka bata sannan suka kama hanyar zuwa part É—in Mama.

Mama ta ce "kai ma tashi kabani wuri ko ba za ka je masalaci bane ana kiran sallah ka wani kafe ni da idanuwa"?.

Yi hakuri ban ji ba ne wallah bara nayi Alwala idan na je sallah kawai zanyi.

A ina za ka yi Alwalar?.

Umma a toilet É—inki idan naje sallah kawai zanyi.

Umma ta ce " wallahi ba ka isa ba ka je can ai akwai kayan alwala sai ka yi Alwalar a can".

Ya ce "toh shi ke nan Umma sai anjima".

Yana fita ya ci karo da su Rashid amma bai tsaya ba kawai ya yi tafiyar shi abin shi, tare suka isa masallacin dake ƙofar gidan su.

Magarib suka idar amma ba su su ka ta shi ba sai da aka idar da isha'i Sannan su ka shiga gidan amma har lokacin Ma'aruf bai kula Rashid É—in ba.

A falo suka tarar da mutanen gidan saboda su ma sun idar da ta su sallar.

Shaga falon su ka yi bakin su É—auke da sallama "Assalamualaikum".

Mutanen falon su ka amsa da ko "waalaikumussalam".

Gai da iyayen nasu suka yi sannan su ka zauna.

Ashe mutumen kan hankalin shi ya kar ka ta a wajen Ummi saboda shigarta ba ƙaramin kyau ta yi ba, riga da wando ne na Pakistan a jikinta.

Ita ko jikinta ya ba ta cewa ana kallon ta ai ko ido huÉ—u suka yi haÉ—e fuska ya yi kamar ba shine ke kallon ta ba ya dallah ma ta harara, ka sa da kai kawai ta yi jikinta har rawa yake yi.

Umma ta ce "Rashid ku tashi mu je dainnin kafin Ummi ta fara yiwa mutane ehun abinci ta ke so".

Hahaha dariya su ka sa ka ma ta tako har da kukan ta wai su dai na ma ta da dariya.
Chapter 2 · 0% Book details