← Book details Rashida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 17

Sashe 17

Rashida Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Haba Momy ke kullum sai takura rayuwar Umma kike, kuma Umma ba ruwan ta dake, amma kullum sai kin tsokaneta, kuma ta yi Magana Abba yabi bayanki ya ce ita ce mara gaskiya, ba yan kuma ita ce mai gaskiyar", Fatima ta faÉ—a cikin takaicin samun mahaifiya irin wannan.

"Fatima kar na sake jin maganar ki a nan, idan ba haka ba sai na saɓa miki", Umma ta faɗa dan ba garma ba ne yarinya ƙarama tana yiwa iyayenta rashin ƙunya ko da mahaukaciya ce tun da ta haife ta ai ta zama mahaifiyar ta."

"Amma Umma..."

"Bana son jin komai daga gare ki, kuma ku bar nan kamin naci mutuncin ku."

"Lailahailallahu Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, yanzun Fatima uwar wata tafi ni kike nufi ko mi?, ni za ki dubi idona kina faÉ—a min cewa wai ba ruwanta dani, sai dai ni ke neman ta rigima."

"Maryam gaskiyar maganar Fatima ce tun ta shin su har yanzun ba wanda ya ji kina neman rigima da ita, sai dai ita ta nemeki, sannan kuma ko a gaban yara sai ta nuna halin ta, ya za ayi ƴaranta su ji daɗi kullum sai dai a ce mahaifiyar ku ce ba tada gaskiya, ai wannan ba daɗi bane kuma ita ma kanta zubarwa kanta ne take da mutunci dan in ba zubewar girma ba, yaro ƙarami kamar Yaronki ba zai raina ta ba" Mama ta faɗa cikin takaicin Momy.

"Ba zubarwar mutunci ba ne kawai kin san kowa da halinshi, sannan kowa da halinshi zai zauna, dan haka ni zan shiga da ga ciki sai anjiman ku, idan ina nan wallahi yau ba na tunanin zan jure wannan kalar wulakancin."

"Ki yi hakuri dan Allah Maryam, ki nuna ma ta cewa ke ba yarinya bace, kin girme ma ta, saboda abin da take yi ko yaro ƙarami ba ya yin shi, kina ji wai Fatima ke buɗan baki ta faɗawa Uwa gaskiya anji kunya dai wallahi."

"Ai kece mai kunya bani idan ba munafurci ba ina ruwanki na shiga tsakanina da ita, yau ko Inna zata shiga tsakanina da kishiyata bale ke banza."

"Ke ce banzar ba su ke dai wallahi kin yi asara ta duniya, aiko kana faɗa ana wulaƙantaka amma kullum sai ka yi."

"Dakata Inna bafa haifata kika yi ba dan haka ba za ki zo kina min wulaƙanci ba, ina kallonki wallahi ba ki kai min can ba."

"Ta fuce da saninki sannan Umma da Mama duk abin da kika kirasu da shi na ji kijira tsammani."

Su Fatima jin murya Rashid ya sa suka fito da gudu.

Suna fitowa ya suka ji ƙarashin zancan shi.

Ido ya zuba wa Ummi ganin haka ya sa ta yi in da Mama.

Ni nafi ƙarfin faɗa da kai sai dai waccan karyar da ka ɗauka Uwa.

Ba Rashid har Umma sai da maganar ta dake kunnen ta.

Rashid kallon Rufa'i ya yi dan ba ya son ciwa Uwar shi mutunci a gaban shi.

Rufa'i ya gane abin da Rashid ke nufi dan haka ya yi tafiyar shi.

"Momy da kata karki sake kin ran Ummana da karya, ana wata karyar bayanki ne, ku...."

Umma bata bari ta ƙarasa ba ta ɗauke ta da mari sai da ta faɗawa kujera.

"Bana hana miki magana da manya haka kina Æ´a mace ba, sha-sha-shar wannan da zan miki gobe sai ya na yau dan ban sameki da kyau ba."

Rashid da gudu ya ƙarasa in da dake ya tallaɓo fuskar ta haka, Mama ta da katar da shi da faɗin.

"Kai mai zaka yi haka da wani uban gudu idan ka taɓa sai ranka ya ɓaci."

"Am...Am..da..ma.... Mama abu zan É—auka ."

"A ina yake abin da za ka É—auka É—in?."

"Am....am...."

can ya hangi cingam É—in take hannun Ummi marin da Umma ta yi ma ta ya sa ya faÉ—i.

"Ka yi shiru sai am...am... Kake min."

"Mama cingam zan É—auka fa."

Dugawa ya yi sai tin in da take ya ce .

"Ba ki ji ciwo ba dai ko? Sannu ki yi haƙura akan ta marin nan zai sauka, ba dai ita ce sila ba ko ki kwantar da hankalin."

Da ido Ummi ta ba shi ganin yaƙi janye idon shi ya sa ta janye nata saboda wani kwarjini idanuwan shi ke ma ta.

"Har yanzun É—aukan cingam É—inne?."

"Hm..hum..eh ban gan shi ba ne sai yanzun."

Ta shi ya yi ita dai Ummi da ita ta bi shi .

"Kika sa aka mari matata a gabana ko?, to ki sa ni wannan marin ba zai tafi a banza ba , kuma ni ba zan mareki ba, amma hmmm ba sai na faÉ—a ba ma aiii."

"Rashid zonan."

"Umma lafiya dai ku nima mari na za ki yi."

"Eh idan baka zo sai kaci ƙaniyar ka."

Yana zuwa kunnen shi ta ja suka shige É—akinta .

Alhamdulillah Alhamdulillahi Alhamdulillahi

Duka duka anan na kawo ƙarshen na bati
Duk mai bukatar complete sai ya siya 500 ne ba yawa
Ga number na
08084277827
Ko
08080304152
Chapter 17 · 0% Book details