← Book details Rashida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 17

Sashe 4

Rashida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Falon ya shiga ya ƙara gaida iyayen nasu sannan ya zauna a kasan ƙafafun Abba.

Abba ya ce "inna ina wuni mun sa me ki lafiya"?.

Inna ta ce "lafiya ƙalau Iro barkanku da fita jirgi lafiya".

Yauwa barka dai Inna cewar Daddy.

Ummi ta ce Abba mu je dainnin ko dan ni kam yunwa nake ji.

Umma ta ce "ba in da zashi sai sun yi wanka tukunna sannan ai maganar cin abinci", sannan Balkisu ki je ki yi wanka ke ma ki zo mu ci abinci.

Balkisu ta ce "uhmm ni ai sai na gyara É—aki na dan nasan ba gyara min aka yi ba".

Mama ta ce "haba Balkisu ya za'ayi ace kuna ta fe mu ƙi gyara maki ɗakin dan Allah kiriƙa tauna magana kamin ki fitar da ita ".

Balkisu ta ce "atoh ni kam nasani dan naga ba a murnar dawo wa ta".

Abba ya ce "wai Balkisu mai yasa ke kullum fitina ce kawai ke ma ki daÉ—i yanzun yaushe rabon da mu yi zama da yaran mu da sauran Æ´an uwanki yanzun gashi mun samu dama kina shirin warga za ta haba dan Allah ".

Abban yara ki yi hakuri dan Allah mu je ka yi wanka sai ku ci abinci, Ummi ku je ra mana abincin a dainnin É—in.

Ƙin tashi ya yi hanu ta sa ta kama hannun shi kamar yaro su ka shiga ciki .

Ummi ta ce "Umma mu na nan fa ko kin manta ne"?.

Mama ta ce "kai Ummi kin cika sa ido", fa ta na maganar ta na dariya saboda ita abin ya ba ta dariya.

Mama ta ce "Daddyn yara ta shi mu je ka yi wankan kai ma ko sai na goya ka ne".

Hahaha su Ma'aruf su ka sa ka dariya.

Rufa'i ya ce "kai Mama mu ma Allah yabamu matan da za su yi mana ha ka dan naga ko ƙunyar mu Umma ba ta ji ba kema Mama ha ka".

Abba ya ce "ku na nufin ba ko tsaida matan aure ba shi ke nan zan ba da ku sadaka ga mai bukata ".

Ma'aruf ya ce "haba Daddy ka san mu yara ne har yanzun ba mu san dai-dai ba da ba dai-dai ba saboda yara ne mu dan Allah ku yi hakuri Daddy har mu girma Please".

Mama ta ce "ai ba ku isa auran ba amma ku ka san Allah ya ba ku matan aure irin mu".

Dariya su Ummi ke yi sosai .

Fatima ta ce " Mama jiya fa Yaya Ma'aruf cewa ya yi shi kam aure ya ke so dan Allah na bashi ƙawata Ihsan".

Ma'aruf ya ce "wallahi Mama ba gaskiya bane ina ma naga ƙawar ta da zance inaso".

Dariya su ka sa ka sosai har da Rashid sai da ya dara.

Mama ta ce "Daddyn yara ta shi muje tun kan su fito".

Ta shi ya yi su ka yi shigewar su É—akin Mama.

Ma'aruf ya ce 'ke Fatima ni za ki wa sharri a gun Daddy saboda ki na son a yi sadaka na ko".

Fatima ta ce "haba Yaya ai wasa ce na ke yi ai ni nafi da son ka sama mana aunty Mai kyau da hankali".

Rufa'i ya ce "ka san mai za ka yi ka rama abokina"?.

Ma'aruf ya ce "a a sai ka faÉ—a".
Rufa'i ya ce "ka cewa Daddy ai Fatima ta ce ta na sonka kuma kai za ta aura idan babu kai ba za ta iya rayuwa ba", nan ta ke Daddy zai yi amanna da ha ka shi ke nan ka rama abin da ta yi ma ka.

Yaya dan Allah ka yi hakuri wallahi ba zan sa ke ba yau idan ka faÉ—i maganar nan ai nasan ba zanyi sati a gidan nan ba dan Allah ka yi hakuri na rantse da Allah ba zan sa ke ba. Cewar Fatima kamar za ta yi kuka.

Dariya su Ummi su ka sa ka ma ta Ummi kam kan dariya har hawaye ta ke yi.

Ma'aruf da Rufa'i ma dariya su ke ma ta sosai shima Rashid É—in ya na murmusawa sakamakon dariyar da Ummi ke yi.

Balkisu ta na shiga É—akin ta tarar da shi fes-fes-fes kiran Hajara ta yi a waya ta ce ma ta "sun iso a Nigeria yanzun ha ka ta na gida ".

Hajara ta ce "toh shi ke nan sai na zo zan faÉ—a ma ki abin da Boka ya ce".

Toh ta ce "sai kin zo É—in ina jiran ki fa Hajara " yanke wayar ta yi.

Wanka ta yi ta canza kaya sannan ta fito falo ta tarar da su Ummi sai dariya su ke yi.

Ummi ta ce "kai ma Yaya Rufa'i sai mu ce kai ka ce ka na son A'ishah shi ke nan mu kam musha shagali a gidan nan wallahi".

Rufa'i ya ce "ai da A'ishah za ta kashe ni wallahi wannan Æ´ar Bala'in zan aura.

Su ka suka dariya har da Rashid.

Momy ta ce "yau nishaÉ—i kawai ku ke yi toh na ji kamai kai Ma'aruf zance kai ka ce ka na son Fatima, kai ma Rufa'i ka ce ka na son A'ishah, kai ma Rashid ka ce ka na son Ummi duk ku bari Abban ku yazo sai na faÉ—a ma su".

Rashid ya ji gaban shi ya ba da tim, sai da ya dan rufe idanunshi kaÉ—an kamin ya biÉ—e a kan Ummi.

Ummi ta ji kamar Momy ta zuba ma ta ruwan zafi ta ce "Momy dan Allah ki yi hakuri wallahi ba ha ka ba ne kawai mu na faÉ—a ne amma ba gaskiya ba ne dan Allah". ta na maganar ta na hawaye.

Momy ta ce a zuciyar ta dole tun da ta ga Ummi ba ta son ana haÉ—a ta da Rashid dole ne ita za ta yi shiga da fice sai an É—aura auren Ummi da Rashid duk a zuciyar ta ke zan cen nan.

A fili ta ce "mai ya sa ki ke kuka ne Ƴarinyata ai basai kinyi min a sarar hawayen nan na ki ma su daraja ba kawai faɗa na ke yi amma bazan faɗawa Abban ku ba kinji ƴata hankalin ya kwanta, Fatima kawo min ruwan sanyi ta sha ko ranta zai yi sanyi.

Fatima ruwa ta kawowa Ummi tasha sannan hankalin ta ya dawo kan ta.

Su Umma su ka fito, ba su jima ba su Mama su ka fito Umma ta ce "su je dainnin Ummi wajen tsakanin Abba da Daddy ta kai kujeran ta ta zauna.

Umma ta ce "Ummi sa ka wa kowa abincin", Abba ya ce "ba za ta sakawa kowa ba sai dai kar su ci", haka Umma ta tashi zuwa sakawa kowa abinci.

FARKON LABARIN

Wani dan karamin ƙauye ne mai suna gada a jahar sokoto.

Wata mata ce mai kimanin shekaru 24 ta na aiki a tsakar gida.

Wata mata ce mai kimanin shekaru 55 tana aikin masifa ta ce "ke Rashida wai wannan abin aikine ki ke yi haka a bu kamar ba ki da jini a jiki tun da ki ka ki haihuwa toh wallahi aiki yanzun ki ka fara".

Iya dan Allah ki yi hakuri bana son musu da ke saboda ke mahaifiyata ce amma kin san da rai da mutuwa da haihuwa duk suna ga Allah

Yee-yee kuka Iya ta saka tana cewa Rashida yau ni ki ke zagi lallai yau kin tabbatar min cewa ke ba tagari bace saboda ko uwar ki ba ki bari bale ni uwar miji tana maganar ne tana kuka sosai har da fece majina.

Rashida ta ce "haba Iya yaushe na zageki wallahi ban zage ki ba dan Allah ki yi hakuri ". tana maganar ne tana kuka ita ma.

Wani matashi ne ya shigo É—auke da sallama a bakin sa "Assalamualaikum" Iya Mai yasamai ki ne ehhe, Rashida Mai yasami Iya ne naga tana kuka"?.

Ai dole za ka tambayi uwarka tun da ni kam banza ce ba ni na haife ka ba kuma ka sa ni wallahi na gaji zama da wannan juyar dole ka zaɓa ko ni ko ita.

Ita dai Rashida kuka kawai take yi saboda da mutum ba shi ba kan shi cikin da sai ta bawa kanta.

Ya ce "Iya dan Allah ki yi hakuri ki bani É—an lokaci in sha Allahu za ki ga jikan ki amma dan Allah ki yi hakuri yanzun wallahi bazan iyawa Rashida kishiya ba saboda ina son ta sosai".

Toh ni za ka faÉ—awa cewa kana sonta lallai Mustapha dole za ka yi min yan da ta ke so.

Ita dai Rashida kuka kawai take yi da taga abin yaƙici yaƙican yewa ya sa ta bar wajen da gudu ta na kuka.

Mustapha dai gabaki É—aya hankalin shi ya tashi saboda ya na son Rashida sosai.

Bin Rashida ya yi É—aki ya na ba ta hakuri ya ce "Rashida dan Allah ki yi hakuri wallahi Ni ma na gaji da wannan abin da Iya ke yi ma ki kuma nasan bakya jin daÉ—i amma ha ka za ki yi hakuri dan Allah".

RASHIDA

By
Sha'awanatu faruk diggi✍️
Sha'awa marubuciya✍️

Wtspp 08084277827☎️📱

PART 4

📝
Amma fa cewa ta yi dole cikin mu ka zaɓi ɗaya ko ita ko ni yanzun dan Allah saboda ban sa mu haihuwa da wuri ba ne za ta tsane ni har ha ka, ai ba ni ke ba wa kai na kuma shirun da haihuwa ta yi min ba shi zai sa Allah ya manta da ni ba Kum.... Kuka ya ci ƙarfin ta ya sa ba ta ƙarasa maganar ba.

Nisawa Mustapha ya yi ya ce "ni dai ba zan gaji wajen ba ki hakuri kuma da ki ke maganar cewa wai na zaɓa wallahi bazan sake ki ba saboda ina son ki sosai dan Allah Rashida ki dai na sa ka damuwa a ranki.

Toh shi ke nan ba na son yin musu da kai mijina ka yi hakuri na dai na amma dan Allah idan ta buƙaci ka sake ni dan Allah kar ka yi ya yayya da ita saboda ba na son fushin iyayye akan mijina.
Chapter 4 · 0% Book details