← Book details Rashida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 17

Sashe 5

Rashida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hahaha toh shi ke nan amma fa ba na fata ki ka san ko na yi ajiya a cikin cikin nan na ki.

Hahaha dariya ta yi sosai sannan ta ce "toh Allah ya sa da gaske ne mijina, mijina ina son ka ina ƙaunar ka."

Matata ina son ki ina kaunar ki ina ma ki son da idan Iya ta matsa rabuwa na ta ke toh wallahi za ta yi biyu babu bu.

Rufe ma sa baki ta yi sannan ta ce " haba mijina mai ya sa ka ke faÉ—an wannan maganar dan Allah ka dai na in sha Allah a tare zamu yi rayuwa har lokacin da Allah zai bamu yara".

Rungume ta ya yi sosai a jikin shi ya ce "ina son ki matata" ai da ga nan na fito na bar ma su dakin saboda um a bar shi kawai.

A kwana a tashi a sarar mai rai yau Rashida ta shi da matsanancin ciwon ciki abu kaɗan ta ci sai amai, Mustapha ya ga ciwon ya yi yawa ya ɗauke ta zuwa ɗan ƙaramin asibiti likita ya yi yawan da ya ke yi ya ce idan za ta iya tashi ta je ta yo fitsari ya bata ƴar ruba ya ce ciki zata yi fitsarin ta je tayo ta ba shi ya yi awon da ya ke yi ya ce "ta na da aure ne"?.

Mustapha ya ce " eh".

Likitan ya ce "ina mijinta"?.

Mustapha ya ce "likita ga ni ko wa ni abun ne ke damun ta saboda wallahi ta ji jiki sosai dan Allah kar ka ce min ta na da matsala ne likita".

Likitan ya ce "kwantar da hankalin ka abokina ba abin da ke damun matar ka ta na nan lafiya, congratulations abokina matar ka na dauke da cikin wata biyu.

Mustapha ya ce "mai ka ce likita ban ji da kyau ba dan Allah ka sa ke faÉ—a min wallahi kunne na wani abun ya ji da ban"?.

Hahaha dariya likitan ya yi ya ce "abokina na ce matar ka na É—auke da juna biyu na wata biyu".

Mustapha sujada ya yi ya na wa Allah godiya, sannan ya ce "likita da mai zan saka maka wallahi da mai kuÉ—i na ke ta yau zaka sha kyauta ta musamman saboda wannan albishir É—in da kai min".

Likitan ya ce "akwai abin da za ka bani amatsayin tukuici".

Mustapha ya ce "likita kafaɗa min menene shi har in baifi ƙarfi na ba zan ba ka shi in sha Allah".

Likitan ya ce "abota kawai nake son mu yi idan ka amince saboda wallahi kabirge ni sosai ina son namiji mai irin halayyar ka".

Mustapha ya ce "yau kam tazo min a Sa'a Allah na gode maka da wannan alkairin da ka ke nuna min, na amince in sha Allah ba zanci amanar ka ba sai dai idan kai kaci tawa amanar".

Likitan ya ce "abokina na gode sosai nima saboda wannan abin da kace min yasa na ƙara jinka a rai na, Allah yabawa matar ka lafiya Allah ya sauke ta lafiya abokina".

Tashi ya yi likitan ya ce mu je na raka ka saboda bana son iska ya ta ɓaka, hahaha dariya su ka gabaki ɗaya.

Barin asibitin su ka yi sai gida su na shiga Iya ta tasu su da bala'i sunje sunyi zamansu a can.

Rashida ta je wucewa ɗaki sai Iya ta riƙe ma ta hijab ta ce "ai daga nan gidan ubanki za ki koma dan nagaji da wahalar min yaro da ki ke yi ".

Mustapha ya ce "Iya ba dai haihuwa ce matsalar ba toh shi ke nan tazo ƙarshe in sha Allah, yanzun daga asibiti muke kuma sunce ta na ɗauke da cikin wata biyu".

Ciki fa kace Mustapha Rashidar ce mai É—auke da cikin ko aure ka yi ban sa ni ba?.

Iya Rashidar dai ce mai É—auke da cikin yanzun kam ai sai ki nuna ma ta soyayyar da ba ta samu ba tun da.

Allah sarki Rashida Æ´ar albarka Allah ya maki albarka Allah ya rabaki lafiya dan darajar Annabi Muhammad s a w ameen ya Allah.

Ameen ya Allahu Iya cewar Mustapha.

Iya ta ce "ƴata sannu kin ji mai zan dafa maki yanzun eh dan nasan ki na buƙatar wani abun ta ɓawa"?

Iya ba komai Na gode sosai yanzun ba na jin yunwa bacci daina ke ji.

Toh shi ke nan Æ´ata ki je ki kwanta ai nasan kina bukatar hutawa.

Iya toh yanzun ya maganar ƙara auren kisama min mata kawai .

Iya ta ce "Mustapha ai yanzun kam ba zancen ƙara auren dama jikokina na ke son ga ni shi ya sa wallahi nace sai ka yi aure amma yanzun kam ba wannan zancen".

Toh shi ke nan bara na shiga ciki sai na fito.

Ɗakin ya shiga ya tarar da Rashida na riƙe da cikin ta tana kuka.

Ya ce "Rashida lafiya daina ga ki na kuka ko wani abun ya faru dan Allah ki faÉ—a min"?

Cikin kukan ta ce "ba komai mijina kawai ina tunanin maganar Iya ne kenan idan ba wannan cikin ba yau rabamu za ta yi".

Haba Rashida kawai Iya na faÉ—a ne ba gaskiya bane ki dai na wannan tunanin ba mai rabamu in sha Allah mu na ta re da ke har abada.

"Allah ya nufa".

A kwana a tashi sai yaro ya za ma babba .

Rashida na ga ni da ƙatan cikin ta sai wa ni ni shi take yi da alama na ƙuda ce tazo ma ta ta ce "Iya Iya ki na ina cikina zai zube".

Iya taji ehun ya yi yawa taje ta leƙa sai taga Rashida a yashe a kasa.

Ta ce "Rashida Meya same ki ne ha ka ko naƙudan ce"? tazo aiko ta taimakon Iya ta haihu ɗanta namiji murna wajen Iya ba a magana.

Ruwan wankan mai jego Iya ta haɗawa Rashida taje ta yi wanka sannan ta zauna, Iya ta ce "ƙarfe shi ki bashi madarar shi yasha".

Rashida ta ce "Iya kibari har Mustapha ya zo sai na bashi madarar dan Allah Iya".

Iya ta ce "yau ni naga ta kaina toh idan yazo shine zai bawa jaririn mamarshi ne".

Haka ba dan tasu ba tabawa yaron madarar shi, tana cikin bashi madarar sai ga Mustapha ya ce "Rashida kice kuwa nake gani da jariri a hanu?.

Iya ta ce "eh itace ko da wani abun ne"?.

A a kawai na tambaya ne ya ce "Iya dan Allah ruwa nakeso zan bawa yaron wani abun ne".

Toh shi ke nan bara na ibu ruwan ta na fita ya zauna a kusa da Rashida ya ce "wai yanzun ni ne na zama uba amma kamar a mafarki".

Ruwa Iya ta kawo ya ce ai ya gama abin da zai yi .

SATI ÆŠAYA
Yau ne ranar suna yaro yaci sunan Muhammad.

Haka dai rayuwa ta ci ga ba da gudana .

Rashida na gani da wani ƙatun cikin ta ta na zaune baƙin murhu ta na hura wuta.

Wani yaro ne É—an kimanin shekaru 4 ya ce "Inna banga jaka ta ba kuma a makaranta dukan litti a ke yi"?.

Rashida ta ce "toh ni kam ina nasan in da ka yada jakar ka yaron nan kawai ka duba a cikin jakar mahaifin ka".

Dubawa ya yi sai ko ya ganta ya É—auka sai makaranta.

Ya na fita ita ko Rashida naƙudar ta tashi da kyar ta samu ta shiga ɗaki ta na shiga ta na haihu ɗanta namiji, Iya ta kira ko da Iya ke shaga ɗaki ta tarar da jariri, aiko daɗi har kunne.

Waje taje ta ce akira ma ta Mustapha yana shigowa Iya ta ce bani abin da za ka bani na faÉ—in haihuwa dan matar ka ta haihu É—a namiji..

Kamin Iya ta rufe baki har ya shige É—aki.

BAYAN SATI

ÆŠa yaci sunan Ibrahim an sha shagali sosai Mustapha ya faÉ—awa likita haihuwar matar shi dan ha ka likita yazo suna .

BAYAN SHEKARU 5

Bayan shekara 5 wasu yara ne nagani sun dawo daga school ɗayan ba zai wuce shekara 9 ba, ɗayan ma bazai wuce shekara 5 da rabi ba mai shekaru 9 ne riƙe da mai shekaru 5 su na tafiya hankali ƙwance gwanin birgewa.

Wa ni ƙaramin gida na ga sun shiga wata mata ce tsugunne ta na fama da wuta su ka "Assalamualaikum" Inna sannu da gida su ka cewa matar ɗago kan da zata yi sai naga Rashida na ce toh su Rashida manya .

Ta ce "a a Æ´an makaranta har kun dawo"?.

Su ka "ce mata eh Inna".

Rashida ta ce "Ibrahim nawa ya hanya Allah ya sa dai malaman ku ba su dake ka ba"?.

"Eh Inna" ya ce

Rashida ta ce "kai yaron nan ku je ku cire kayan sai ku zo ga abincin ku".

Toh wai ina Iya ne.

Mustapha ya shigo bakin sa É—auke da sallama "Assalamualaikum".

"Waalaikamussalam" ta amsa ma sa ta ce "sannu da zuwa malam" saboda yanzun karantas suwa ya ke yi.

Yauwa barka da gida kawai ya ce ya yi tafiyar shi.

Bin shi ta yi a É—akin ta ce "malam lafiya na ganka ha ka dan Allah ka yi hakuri Allah yabamu ita kuma shi ya amshi abarsa".

Ni sawa ya yi ya ce "wallahi Rashida ba ki san yadda mutuwar Iya ta tsaya min a rai ba saboda itace kawai na ke kalla na ji daÉ—i".

Ayya Allah sarki Iya Allah ya gafarta mata ni daina ce.

BAYAN SHEKARU 7

wa ta Æ´ar tsohowa na gani kwance da alama ba tada lafiya wata yarinya na a kusa da ita yarinyar ta ce "Inna wai ina su Yaya suka yi ne har yanzun basu dawo ba kuma yunwa nake ji"?.

Wacce aka kira da Inna ta ce "A'ishah ki yi hakuri zasu dawo in sha Allah kuma za su sama ma ku abincin da zaku ci kinji".

"Assalamualaikum".

"Waalaikamussalam" Æ´ar tsohowar ta faÉ—a

Babban cikin Æ´an samarin ya ce "Inna ya jikin"?.

Sannan ƙaramin ya ce "Inna kin ji sauƙi"?.

Ta ce "eh naji sauƙi sosai sai dai abin da ba a rasa ba".
Chapter 5 · 0% Book details