← Book details Rashida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 17

Sashe 6

Rashida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inna dan Allah ki fitar da mutuwar nan ta Baba a ranki yau fa shekara 2 amma kullum sai ki yi kuka ga shi ke ba lafiya ba. Cewar babban.

Uhmm toh meka ke son na yi ne idan ban yi kuka meka ke son na yi yanzun ha ka ga ƙanwar ku nan ta ce yunwa ta ke ji kuma ga shi naga kamar baku samu komai ba.

A a Inna mun samu abinci ga shi kwano É—aya ne dai ba yawa.

Ta shi ta yi ta ce "Allah ya yi ma ku albarka Allah yabaku sana'a mai albarka".

Muhammad ya ce "Inna mai zai ha na ki bari naje Kano ne man rabona ko Allah zai sa na samu dan Allah Inna Kar ki ce a a dan Allah".

Humm me yasa ka ce kar na hana ka zuwa bayan kasan bana son kuna nesa da ni mahaifana sun tafi sun barni Iya ta tafi ta barni mahaifin ku ya tafi ya barni ya ka ke son nayi ne.

Ƙaramin saurayin ya ce "Inna ki bari Yaya yaje wata kila ƙarshen waharmu tazo ƙarshe dan Allah ki yarda ita shi yatafi ai Inna ina tare da ke".

Shi ke nan toh yaushe za ka tafi ne.
Eh to Inna duk ranar da ki ka ce tayi maki ni Ashirye nake.

Toh shi ke nan sai na gani sai na faÉ—a maka kuma Kanada kuÉ—in tafiya ne.

Mustapha ya ce "a a Inna amma ai ba zasu yi wuya ba saboda akwai wata Æ´ar wahala wai sona take sai nace ma ta tafiya zan yi in sha Allah zan samu kuÉ—in mota".

A a ni kam ban yarda da wannan shawarar ba ga filin gadon ku nan ka siyar da rabi nasan kuÉ—in zasu yi ma ka .

Toh shi ke nan Inna zan faɗawa Baba idi in sha Allah sai ya yi min waƙilci .

Toh shi ke nan Allah yaba da sa'a Allah ya sa ayi a Sa'a .

Ameen ya rabbin alamina.

BAYAN SHEKARA 2

Rashida ce zaune ita da A'ishah su na fira A'ishah ta ce "Inna sai yaushe zamu koma birni dan naji Yaya ya ce wai Yaya na birni ya siya gida a can zamu koma da zama"?.

A a gidan da ya siya ai wanda zai sa ka auntn ki ne ko bakya son ya yi aure.

Laaaa dama Inna Yaya aure zai yi shine ya ce min wai can zamu koma da zama?.

A a sai ya yi aure zuwa sannan ya ƙara samun kwanciyar hankali.

"Assalamualaikum" a a Inna kina nan da Æ´ar ki ko?.

"Waalaikamussalam" Toh kai kam ai ka girma ba ka son zama tare da Ni".

A a wallahi Inna kawai bana son zama ne lokacin biyan kuɗin maganar ya yi ne kuma kin san ƙurota zasu yi.

Haka ne kam toh Allah ya sanya alkairin amma ka ji Yayanka yau kuwa.

Eh Inna ya na ma shigowa gobe in sha Allah.

Yeeeee Yaya na birni zai zo Allah ya sa ya siyo min abin daÉ—i birni.

Kai kedai bakya barin shirme toh Allah ya kawo shi lafiya.

Ameen kawai ya ce.

A Kano

Muhammad gadi ya ke a wani babban gida duk wata ana biyan shi dubu 20 goma ya kai gida goma kuma yaba da ajiya ga Æ´ar mai gidan, har yasa mu kuÉ—i masu yawa ya siya siminti da yashi har da fili, budurwar san ye da atamfa ta ce "Yaya ga abincin ka".

Muhammad ya ce "Toh Hajiya na gode sosai Allah ya sa ka da alkairi Allah ya ba ki miji na gari Hajiya".

Ta ce "Ameen Yaya amma ai Allah ya bani sai dai idan shine ya ce ba ya sona".

Ta ce "Ah Alhamdulillahi ce har kin samu amma ba wanda yazo gidan nan dan banga wanda ya taɓa zuwa ya ce akira ma sa ke ba sai dai auntyn ki".

Ta ce "Yaya kaine ina son ka ina ƙaunar dan Allah karka ce ba ka sona wallahi zan iya cutuwa".

Amma Hajiya ai ke ba sa'ata ba ce saboda ni talaka ne sosai kuma banada karatu mai zurfi dan Allah ki yi hakuri amma bazan iya ba Hajiya.

Ta ce toh shi ke nan idan na mutu dan Allah ka min wannan alfarmar kazo kan gawata ka ce kana so na ko zan ji salama.

Ya ce "Haba Amina dan Allah ki dai na wannan maganar ba da amfani ga".

Da gudu ta bar wajen sai É—akinta kuka take yi sosai kamar ranta zai fita.

Mamartace ta ce "Amina me yasa meki ne naga kin shigo ki na kuka kifaÉ—a min mana"?.

Mama Yaya ya ce ba ya sona wallahi Mama idan ban aure shi ba, ba zan rayu ba dan wallahi guba zan sha na mutu kuwa ya huta cikin kuka ta ke wannan maganar.

Mama ta ce "Yanzun saboda Muhammad mai gadi ki ke wannan uban kukan ki kwantar da hankali in sha Allah Muhammad bai da mata sai ke kema bakyada miji sai Muhammad kin ji Æ´ata".

Amina ta ce "Mama kimin alƙawarin cewa Muhammad zai auran"?.

Mama ta ce "Na yi maki alƙawarin Muhammad na ki ne kibari mahaifin ki yazo sai na faɗa ma sa".

Ta shi ta yi taga toilet ta É—auro alwala tazo ta yi nafila raka'a biyu dan neman samu masoyan ta.

Shi ko Muhammad Ibrahim ya kira ya ce "Ibrahim ina cikin damuwa".
Ibrahim ya ce"Yaya meke faruwa ne"?.
Muhammad ya ce "Wallahi yarinyar gidan ce wai ta ce tana sona ni kuma gaskiya banada lokacin aure yanzun saboda su nake na gina gida harda kai da yaran da zamu haifa nan gaba, amma yanzun duk shirina zai lallace ne kuma wallahi yarinyar ta ce zata kashe kanta idan ban amince ba ya zan yi Ibrahim"?.

Ibrahim ya ce "Yaya ka amince kawai har in kana sonta saboda buri baya cika sai an shawuya dan Allah ka amince kawai".

Ibrahim idan na ce maka bana sonta toh wallahi nayi ma ƙarya ina sonta dan yarinyar mutum niyar kirki ce.

Toh shi ke nan ka amince kawai mukam musha shagali abin mu kaga A'ishah kullum kwaÉ—ayin komawa birni ta ke Inna ta ce ba Inna da zata sai ka yi aure tukuna.

Toh shi ke nan Allah yazaɓa abin da yafi Zama alkairin.
Ameen ya Allah cewar Ibrahim.
Yanke wayar ya yi sakamakon hon É—in da akeyi.

Get ya buÉ—e mai gidan ne shiga ya yi shima ya rufe gidan.
Ya ce "Alhaji Barka da shigowa".

Alhaji ya ce " Yauwa barka da gida Muhammad".

Gida ya shiga ya tarar da Amina a falo ya ce "Mamana lafiya daina ganki ke ɗaya", shiru ya ke ji hakan ya sashi zuwa kan kujerar ya zauna ya ta ɓa ta sannan ta dawo hayyacin ta.

Ta ce "Alhaji Barka da zuwa".
Ya ce "Amina meke damunki ne tun É—azun nake kan ki ina maki magana amma shiru".

Laa Alhaji ba komai kawai bana jin daÉ—i ne.

Sannu da zuwa Alhaji an dawo lafiya?.
Lafiya ƙalau Maman Amina .

Mu je kayi wanka sannan ka ci abinci sai mu yi maganar.

Wace irin magana ce wannan?.

Magana ce akan Amina .
Amina kuma kizo ki zauna sai mu yi maganar kawai nayi wanka daga baya.

Haba Alhaji kaj.., bai bari ta ƙarasa ba ya ce "Ina jin ki faɗa min menene ke damunta"?.
Alhaji wai yarinyar nan ta rasa wa zataso sai Muhammad mai gadi.

Muhammad mai gadi kuma?.

Eh shi dai har guba ta ce zata sha in da ba a aura mata shiba sai da na ce mata na yi ma ta alƙawarin aura ma ta shi.

Ai wannan abin farin ciki ne Hadiza saboda wallahi yaron na da hankali da nutsuwa nima na kwaÉ—ayi ba shi Aminar sai dai nayi tunanin ko ba za ta amince ba.

Toh ai shi ke nan yazo gidan sauƙi kiran min ita Amina, Amina "na'am" Mama zo in ji Alhaji.

"Alhaji gani".
Kiramin Muhammad.
Alhaji ka aiki Mama ta kira maka shi dan Allah.
Ya ce "Amina na ce ki kira min Muhammad".

Toh kawai ta ce sannan ta tafi kiran shi.

Ta ce "wai kazo in ji Alhaji".
Ya ce "yau ba ko Yaya kawai kazo in ji Alhaji".

Toh kai Yayana ne da zanci gaba da kiran ka da Yaya aikin banza kawai.
Tafiyar ta ta yi shi ko bayanta yabi dan jin kiran da Alhaji ke yi ma sa.

RASHIDA

By
SHA'AWANATU FARUK DIGGI ✍️
Sha'awa marubuciya ✍️

WhatsApp number 08084277827☎️

PAGE NA BIYAR 5

📝
Uhmm toh meka ke son na yi ne idan ban yi kuka meka ke son na yi yanzun ha ka ga ƙanwar ku nan ta ce yunwa ta ke ji kuma ga shi naga kamar baku samu komai ba.

A a Inna mun samu abinci ga shi kwano É—aya ne dai ba yawa.

Ta shi ta yi ta ce "Allah ya yi maku albarka Allah yaba ku sana'a mai albarka."

Muhammad ya ce "Inna me zai ha na ki bari na je Kano ne man rabona ko Allah zai sa na samu dan Allah Inna Kar ki ce a a dan Allah."

"Humm me yasa ka ce kar na ha na ka zuwa bayan kasan bana son kuna nesa da ni mahaifana sun tafi sun barni Iya ta tafi ta barni mahaifin ku ya tafi ya barni ya ka ke son nayi ne."

Ƙara min saurayin ya ce "Inna ki bari Yaya yaje wata kila ƙarshen wahar mu tazo ƙarshe dan Allah ki yarda ita shi ya tafi ai Inna ina tare da ke."

"Shi ke nan toh yaushe za ka tafi ne.
Eh to Inna duk ranar da ki ka ce ta yi maki ni a shirye nake."

"Toh shi ke nan sai na gani, sai na faÉ—a maka, kuma Kana ma da kuÉ—in tafiyar ne."

Mustapha ya ce "A a Inna amma ai ba za su yi wuya ba saboda akwai wata Æ´ar wahala wai su na take, sai nace mata tafiya zan yi in sha Allah zan samu kuÉ—in mota."
Chapter 6 · 0% Book details