← Book details Rashida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 17

Sashe 14

Rashida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lafiya ƙalau."

Kafe shi da idanuwa Nafisa ta yi shiko yana ji a jikin shi ana kallon shi team ne a gaban shi hannun ya sa ya É—auki kofin kamar sha zai yi sai ya zuba mata shi a idanuwanta Aiko ihu ta hauyi ba Rufa'i har Ma'aruf duk sun ruÉ—e amma shi kam ko a jikin shi.

Mamar ta ce ta fito da gudu tana tambayar me ya sa Meta ne?.

Rashid har yanzun yana zaune abin shi sai danna waya yake yi.

Mamar Nafisa ta ce "wai me ya sa Meta ne ina magana kun min shiru?."

"Yanzun mu kai ta asibiti please."

"Abokina Dan Allah ka duba min ita ka taimaka min."Rufa'i ya faÉ—a

"Wallahi ba zan taɓi wannan abin ba kuma tafiya zan yi, idan ku ka gama ku tari abin hawa."

Haka ko ya yi tafiyar shi ya yi kan hanyar ta zuwa gida tsallake titi ya hangi Fatima da A'ishah har da Ummi.

Parking ya yi ya tsallaka titin da ƙafa yana zuwa ya ji Ummi ta ce

"Ai kai ka ɗaine ba ƙari sauran maza duk mata ne tana dariya sosai."

Ranshi ya kai ƙololuwar ɓaci fuskar nan kamar wani zaki haka ya tunkari saurayin .

Saurayin na tsaye kawai ya ji an taɓa shi .

"Lafiya dai malam?." Saurayin ya tambaya.

Naushi Rashid ya aikawa saurayin Fatima kuka take yi sosai

"Yaya dan Allah ka yi hakuri wallahi ba saurayin ta bane, saurayina ne dan Allah ka yi hakuri."

Yana huci yana ƙari ran maza yaɓaci .

"Me ya sa naji tana kiran shi da shi ka ɗaine dan iskanci, kema zamu haɗu a gidan, ku wuce mu je gidan ko sai na ɓallaku anan."

Mamaki ya cika cikin Ummi toh akan mi zai yi faÉ—a akan nace shi ka É—aine toh ina ruwan shi.

Shiga motar suka yi su duka a baya ya ce tun da Driving sune ba.

Fatima ta fita ta dawo gaba harara ya cilla mata dole ta fita suka ce Ummi ta koma gaba, fita ta yi ta zauna jan motar ya yi a tsiyace da sauri Ummi ta faÉ—a jikin shi tana kuka tana faÉ—in

"Dan Allah Yaya ka yi hakuri ban yi maka laifin komai ba, dan Allah ka rage gudu wallahi tsoro nake ji."

Ƙara gudun motar ya yi saura kaɗan ya buge mai machin.

Ƙara riƙe shi ta yi sosai tana magiya amma a banza, sai da suka shiga kwanar gidan su sannan ya rage gudu.

Hon ya yi mai gaɗi ya ɓude gidan a guje ya shiga da motar a cikin gidan saura ƙiris ya taka ƙafar mai gadi.

Parking ya yi a wajen parking lot su Fatima a guje suka fita a motar, kamin ta fita tuni ya sa kawa motar key jan marfin motar ta yi da niyar buÉ—ewa, amma ta ji shi rufe duban shi ta yi tana kuka har da majina.

"Waye shi wancan É—an iskan yaron?."

"Yaya wallahi saurayin Fatima ne."

"Za ki faɗa min gaskiya ko sai na ɓallaki a cikin motar nan."

"Wallahi Yaya saurayin Fatima."

A jiyar zuciya ya sauƙe mai nauyin gaske har Ummi sai da taji.

"Toh ki kiyaye idan ba haka ba, toh wallahi sai na ɓallaki idan na sake ganin ki da wani saurayin."

"Yaya bana da saurayi fa kuma ba mai sona ba mai kulani."

"Akwai masu sonki kawai su nuna ne basa iyawa, saboda haka idan kika kula so wallahi wallahi wallahi kin ji na rantse ko sai na rabaki da kowaye."

"Toh ba zan kula kowa ba wallahi dan Allah ka ɓuɗe min na fita."

"Cinye ki zan yi ne da kika matsu kibar motar?."

"A a Yaya yi hakuri."

Buɗe mata motar ya yi da sauri ta ɓude zata fita taji an riƙe mata mayafi, da sauri ta kai duban ta gareshi wani kallo ya ke mata da ita ma kan ta bata san kallon mene ne ba.

"Yaya dan Allah ka sake ni wallahi fitsari nake ji."

"Yi hakuri jeki sai mun haÉ—u."

"Toh ."

RASHIDA

Sha'awa marubuciya diggi ✍️
number08084277827

20

Fita ta yi daga motar saboda ga ba ki É—aya ta kasa gane me maganganun shi ke nufi.

Tana shiga gidan su Fatima suka saka mata dariya suna faÉ—an .

"Wai me Yaya ke nufi ko dai ko dai?, hummm da abin yaba da citta🤪."

"Ko dai ko dai mii zonan dan Ubanki Fatima."

Suka ji an faÉ—a daga bayan su aii da gudu Ummi ta shige É—akin Mama.

Murmushi Rashid ya yi saboda ba ƙaramin dariya ta ba shi ba.

Mama na zaune ta ji mutum ya faÉ—a kanta da sauri da ta shi yana salati.

"Ummi mai ke faruwa ne haka?, ke da waye kuma haka?, ki faÉ—a min mana, duk lokaci É—aya ta yi ma ta waÉ—an nan tambayoyin.

Shiru Ummi ta yi saboda bata da amsar tambayoyin nan na Mama.

Rashid ya nufi in da Fatima da A'ishah suke ai su na ganin haka suka rugu a guje sai É—akin Mama.

"Ashe ƙaryar iskanci kuke yi da kun tsaya."

"Bana son ta mutu amma ina son a haukatar min da ita, saboda matar ta isheni wallahi ga yaran nan duk ita suke so, sai abin da ta ce suke yi." Mommy ce ke waya da alama da Hajara ta ke wayar.

"Hahaha kar ki damu ba kince tana da ciwon zuciya ba, toh a nan ne zamu samu abin da muke so."

"Toh shi ke nan nawa zan tura miki yanzun, dan kin san saunan can ya rage sakin hanu."

"Ba komai ki tura ko nawa ne ma, zan ma sa bayani, amma dole ne wani lokacin kije da kanki."

"Eh nima ina son yin hakan amma ki bari zamu yi magana da ga baya."

"Toh shi ke nan sai anjima."

"Wai mai ke faruwa ne?, na ganku hakan kamar an jeho min ku."

"Mama ba komai kawai wulaƙanci suke ji da shi wallahi."

"Toh ina kayan da ku ka siyo mana ne?."

"Mama wallahi Yaya ne ya koro mu, wai har da kiran idan ya sa ke ginin mu da samari sai ya ɓallamu."

"Ai dama na san ba zai wuce kan shi ba, saboda kullum shine ke takura maku a gidan nan."

"Wallahi kam Mama haka ne."

"Assalamualaikum."

"Waalaikimussalam"

"Ina wuni Mama?."

"Lafiya"

"Mama dama so na ke mu yi wata magana dake dan Allah."

"Ina mahaifiyarka kaje can ku yi maganar."

"Haba Mama wannan maganar ai sirrin ne tsakani na da ke."

"Kai ku bar É—akin nan ku ta shi ko na zane ku yanzun."

"Allah yabaka hakuri Yaya" cewar A'ishah.

"Babu in da zaku je kuna nan."

"Shi ke nan Mama sai anjima."

"Zan je wajen Ummana kuma za ta kulani , in sha Allah za ta fahimce ni" cikin ɓacin rai ya bar ɗakin.

"Mama zan je na yi wanka."

"Ke kun manta su Yaya Rufa'i sun je zance kuwa."

Gaban A'ishah sai da ya buga sosai.

"Laaaa wallahi na manta mu je mu yi wanka, sai mu je su bamu labarin" Ummi ta faÉ—a tana dariya.

"A'ishah mene ne naji kinyi shiru lafiya dai, ko har yanzun ba ki hakura bane" cewar Mama.

Dariya da bata kai ciki ba A'ishah ta yi dan ɓuye abin da ke ranta.

"Ba komai ai na hakura Mama, yanzun a matsayin Yayana nake kallon shi, ba saurayina ba."

"Toh Allah ya maku albarka."

"Ameen ya Allah 🤲".

Da dare ana zaune sai Ummi ta kalli Fatima da A'ishah suka yi dariya sannan Ummi ta ce .

"Yaya Ma'aruf ku bamu labarin auntyn mu mana dan Allah, tun É—azun sai rabon ido muke amma kun yi shiru."

"Ai nima tun É—azun su na ke jira amma sun yi min shiru, ko dai baku da gaskiya ne" Umma ke faÉ—ar maganar.

Hahaha 🤣 dariya suke yi idan suka kalli Rashid, dan ba ƙaramin dariya ya basu ba lokacin.

Ganin rashin mutunci da suke sun ma sa ne ya sa ya kaima Rufa'i duka.

"Wai me ya sa ku ke ma sa dariya ne haka?."

"Umma bari mu baku labarin zuwan mu zance", hahaha 🤣 suna maganar suna dariya.

Labari suka ba su kabba abin da suka rage masu .

Dariya suka shiga yi har Mama sai da tadara saboda abin da Rashid ya tsiyanta a gidan.

Ummi kan dariya har wani hawaye take yi.

Umma ta ce.

"Yanzun Rashid abin da ka yi a gidan mutane kenan, ai dana sa ni da ban barka kaje ba", ta faÉ—a tana dariya.

Kiran wayar Ma'aruf aka yi amma yana dubawa ya ga sabuwar number É—agawa ya yi sai ya ce

"waye?".

Tacan bangaren aka ce

"Ruƙayyat ce."

Ta shi ya yi niyar yi amma Ummi ta dafe shi wai ba in da zai je sai dai ya yi wayar a gaban su.

"Hello Rayyan yakake ina gida idan na fita zan kira ka."

Dariya suka saka ma sa wai Rayyan.

Rufa'i ya yiwa Ummi alama da ido ta amshe wayar da mace yake waya, iko da sauri ta amshe wayar.

"Hello auntymu yakike ya gida ya su Umma."

Ma'aruf ya ce.

"Amma dai Wallahi baka da mutunci Rufa'i, yanzun ga shi ko magana bamu yi amma ka wani zo sai faÉ—awa mutane ku ke yi."

Abba ne da Daddy suka shigo dama su suke jira dan su ci abinci.

"Ah ah Æ´ar Daddy dariya mi ake yi haka ne?, ko waya ce ake yi da sirikina?."

Dariya ta yi sosai sannan ta faÉ—i cewa.

"Ai budurwar Yaya ce."

"Toh zu mu je dainnin."

"Wace ce budurwar ta shi, idan dai har ma ta min ba toh ba zai aure ta ba, kuma sai Rufa'i ya yi aure ko shima zai yi."

"Abin da ba zai yiwu ba kenan dukan su rana É—aya ne zan aurar da su, amma kai Rashid wace ce yarinyar da kake so saboda rana É—aya ne zan aurar da ku."

Ƙasa da kai kawai Rashid ya yi saboda ya san ba wacce yake so.

"Ai Rashid kunya ne da shi, shi ya sa bai faÉ—a maku ba, amma jiya ya same ni ya faÉ—a min cewa...... Yana son Ummi da aure."
Chapter 14 · 0% Book details