← Book details Rashida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 17

Sashe 7

Rashida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A a ni kam ban yarda da wannan shawarar ba ga filin gadon ku nan ka siyar da rabi na san kuÉ—in zasu yi ma ka .

Toh shi ke nan Inna zan faɗawa Baba idi in sha Allah sai ya yi min waƙilci .

Toh shi ke nan Allah yaba da sa'a Allah ya sa ayi a Sa'a .

Ameen ya rabbin alamina.

BAYAN SHEKARA 2

Rashida ce zaune ita da A'ishah su na fira A'ishah ta ce "Inna sai yaushe za mu koma birni dan na ji Yaya ya ce wai Yaya na birni ya siya gida a can za mu koma da zama?."

"A a gidan da ya siya ai wanda zai sa ka auntn ki ne ko ba kya son ya yi aure."

"Laaaa dama Inna Yaya aure zai yi shi ne ya ce min wai can za mu koma da zama?."

"A a sai ya yi aure zuwa sannan ya ƙara samun kwanciyar hankali."

"Assalamualaikum a a Inna kina nan da Æ´ar ki ko?."

"Waalaikamussalam toh kai kam ai ka girma ba ka son zama tare da Ni."

"A a wallahi Inna kawai bana son zama ne lokacin biyan kuÉ—in makarantar ya yi ne kuma kin san kurota zasu yi.

"Haka ne kam toh Allah ya sanya alkairin amma ka ji Yayanka yau kuwa."

"Eh Inna ya na ma shigowa gobe in sha Allah."

"Yeeeee Yaya na birni zai zo Allah ya sa ya siyo min abin daÉ—i birni."

"Kai ke dai ba kya barin shirme toh Allah ya kawo shi lafiya."

"Ameen kawai ya ce."

A Kano

Muhammad gadi ya ke a wani babban gida duk wata ana biyan shi dubu 20 goma ya kai gida goma kuma yaba da ajiya ga Æ´ar mai gidan, har ya sa mu kuÉ—i ma su yawa ya siya siminti da yashi har da fili, budurwar san ye da atamfa ta ce "Yaya ga abincin ka."

Muhammad ya ce "Toh Hajiya na gode sosai Allah ya sa ka da alkairi Allah ya ba ki miji na gari Hajiya."

Ta ce "Ameen Yaya amma ai Allah ya bani sai dai idan shine ya ce ba ya sona".

Ya ce "Ah Alhamdulillahi ki ce har kin samu amma ba wanda yazo gidan nan dan ban ga wanda yata ɓazuwa ya ce akira ma sa ke ba sai dai auntyn ki."

Ta ce "Yaya kai ne ina son ka ina ƙaunar dan Allah karka ce ba ka sona wallahi zan iya cutuwa."

Amma Hajiya ai ke ba sa'ata ba ce saboda ni talaka ne sosai kuma bana da karatu mai zurfi dan Allah ki yi hakuri amma bazan iya ba Hajiya.

Ta ce "Toh shi ke nan idan na mutu dan Allah ka min wannan alfarmar kazo kan gawata ka ce kana so na ko zan ji salama."

Ya ce "Haba Amina dan Allah ki dai na wannan maganar ba ta da amfani ga."

Da gudu ta bar wajen sai É—akinta kuka take yi sosai kamar ranta zai fita.

Mamar ta ce, ta ce "Amina me yasa meki ne naga kin shigo ki na kuka ki faÉ—a min mana?."

"Mama Yaya ya ce ba ya sona wallahi Mama idan ban aure shi ba bazan rayu ba dan wallahi guba zan sha na mutu kuwa ya huta cikin kuka ta ke wannan maganar."

Mama ta ce "Yanzun saboda Muhammad mai gadi ki ke wannan uban kukan ki kwantar da hankali in sha Allah Muhammad bai da mata sai ke kema ba kya da miji sai Muhammad kin ji Æ´ata."

Amina ta ce "Mama kimin alƙawarin cewa Muhammad zai auran?."

Mama ta ce "Na yi maki alƙawarin Muhammad na ki ne kibari mahaifin ki yazo sai na faɗa ma sa."

Ta shi ta yi tashi ga toilet ta É—auro alwala tazo na yi nafila raka'a biyu dan neman samu masoyan ta.

Shi ko Muhammad Ibrahim ya kira ya ce "Ibrahim ina cikin damuwa."

Ibrahim ya ce"Yaya meke faruwa ne?."

Muhammad ya ce "Wallahi yarinyar gidan ce wai ta na sona ni kuma, gaskiya bana da lokacin aure yanzun saboda so nake na gina gida harda kai, da yaran da za mu haifa nan gaba, amma yanzun duk shirina zai lallace ne ku ma wallahi yarinyar ta ce za ta kashe kanta idan ban amince ba ya zan yi Ibrahim?."

Ibrahim ya ce "Yaya ka amince kawai har in kana son ta saboda buri ba ya cika sai an shawuya dan Allah ka amince kawai."

"Ibrahim idan na ce maka bana son ta toh wallahi na yi ma ƙarya ina son ta dan yarinyar mutum niyar kirki ce."

"Toh shi ke nan ka amince kawai mu kam musha shagali abin mu, kaga A'ishah kullum kwaÉ—a yin koma wa birni ta ke Inna ta ce ba Inna da za ta sai ka yi aure tukuna."

"Toh shi ke nan Allah yaza ɓa abin da yafi Zama alkairin.
Ameen ya Allah cewar Ibrahim.
Yanke wayar ya yi sakamakon hon É—in da a ke yi."

Get ya buÉ—e mai gidan ne shiga ya yi shi ma ya rufe gidan.
Ya ce "Alhaji Barka da shigowa".

Alhaji ya ce " yauwa barka da gida Muhammad".

Gida ya shiga ya tarar da Amina a falo ya ce "Mamana lafiya daina ganki ke ɗaya", shiru ya ke ji hakan ya sa shi zuwa kan kujerar ya zauna ya ta ɓa ta sannan ta dawo hayyacin ta.

Ta ce "Alhaji Barka da zuwa."
Ya ce "Amina me ke damunki ne tun É—azun nake kan ki ina maki magana amma shiru."

"Laa Alhaji ba komai kawai bana jin daÉ—i ne."

"Sannu da zuwa Alhaji an dawo lafiya?."

"Lafiya ƙalau Maman Amina ."

"Mu je ka yi wanka sannan ka ci abinci sai mu yi maganar."

"Wace irin magana ce wannan?."

Magana ce akan Amina .

Amina kuma kizo ki zauna sai mu yi maganar kawai na yi wanka daga baya.

Haba Alhaji kaj.., bai bari ta ƙarasa ba ya ce "Ina jin ki faɗa min menene ke damunta?."

"Alhaji wai yarinyar nan ta rasa wa za ta so sai Muhammad mai gadi."

Muhammad mai gadi kuma?.

"Eh shi dai har guba ta ce za ta sha, in dai ba a aura mata shiba sai da na ce mata na yi mata alƙawarin aura mata shi."

Muhammad ya ce "Ai wannan abin farin ciki ne Hadiza saboda wallahi yaron na da hankali da nutsuwa, ni ma na kwaÉ—ayi ba shi Aminar sai dai na yi tunanin ko ba za ta amince ba."

Toh ai shi ke nan yazo gidan sauƙi kira min ita Amina,Mama kiran Amina ta yi.

Amina ta ce "na'am"

"Mama zo", in ji Alhaji.

"Alhaji gani."

Kiramin Muhammad.

Amina ta ce "Alhaji ka aiki Mama ta kira ma ka shi dan Allah."

Ya ce "Amina na ce ki kira min Muhammad."

Toh kawai ta ce sannan ta tafi kiran shi.

Ta ce "wai kazo in ji Alhaji."

Ya ce "yau ba ko Yaya kawai kazo in ji Alhaji."

Toh kai Yayana ne da zanci gaba da kiran ka da Yaya aikin banza kawai.

Tafiyar ta ta yi shi ko bayanta yabi dan jin kiran da Alhaji ke yi ma sa.

"Assalamualaikum ya ce "zan iya shigowa Alhaji."

"Waalaikamussalam ya ce eh."
Shiga ya yi ya tarar da Amina zaune a ƙasa .

Alhaji ya ce "Muhammad ka san me yasa na kiraka?."

Muhammad ya ce "A a Alhaji sai ka faÉ—a."

Alhaji ya ce "Wata alfarma na ke son ka yi min idan zan samu."

"Alhaji alfarma kuma ai kawai ka faÉ—a cikawa ne nawa."

A a Muhammad alfarma dai da ka ji na ce shi ne za ka min.

Toh shi ke nan Alhaji ina ji .

Toh Muhammad da farko dai ba dole akan wannan abin idan ba ka sonta kawai ka faÉ—a min.

Alhaji ya ce "Ina son ka auri Amina idan babu damuwa, kuma idan kana son ta idan ba ka son ta toh dan Allah kar ka takura kanka ka ji Muhammad."

Gaban Muhammad ne faÉ—i ya É—aga kai ya na kallon Amina ita ma shi take kallo tana son jin abin da zai ce.

Ya ce "Shi ke nan Alhaji na amince zan auri Amina sai dai ni ba mai kuÉ—i ba ne talaka ne ni sosai."

Alhaji ya ce "Muhammad da talaka da Mai kuÉ—i duk su na a hanun wa ye?."

Muhammad ya ce "Allah."

Alhaji ya ce "Toh saboda haka ka dai na maganar cewa wai kai talaka ne, halam ita bata san da cewa kai mai gadi ba ne amma ta ce tana sonka, ka ga ko ai kai ma mai kuÉ—i ne."

Amina ta ce "Da gaske Muhammad ka amince za ka aure ni na ji daÉ—i sosai wallahi Alhaji na gode Allah ya sa ka da alkairi."

Mama ta ce "Yanzun kam Amina sai a fasa shan guba ko?."

Rufe idanuwanta ta yi ta ce "Ai Mama shi ne ya ce bazai auran ba."

Dariya su ka yi ga ba ki É—aya sannan Alhaji ya ce "ya tashi ya tafi."

Fita ya yi sai wajen zaman sa kiran Ibrahim ya yi ya ce "Ibrahim an bani yarinyar fa yanzun da ga can na ke."

Ibrahim ya ce "Toh Yaya kai kace kana son ta ne ko ita tace tana sonka?."

"A a mahaifin ta ne ya kira ni wai dan Allah ya na son na auri yarinyar shi, amma kabari idan na shigo gobe sai mu yi maganar har da Inna."

"Toh shi ke nan sai ka shigo."

"Toh Inna dai na lafiya ko kuma ya karatun ka da na A'ishah komai ya na tafiya dai dai ko?."

"Eh Yaya Alhamdulillahi dan mun kusa rubuta jarabawar."

"Toh shi ke nan Allah ya ba da sa'a.
Ameen ya Allah."

WASHEGARI

Muhammad ya shirya cikin shaddar sa ma sha Allah, Amina ta ce "Yaya ka yi kyau sosai wallahi dan Allah zan bika mu je tare tun da ba can za ka kwana ba."

Ya ce "A a Amina ba zan je da ke ba saboda Inna za ta yi min faÉ—a ne."

"Toh shi ke nan sai ka dawo amma fa zan yi ke warka sosai."

Leda ce babba Amina ta ba da ta ce ya kaiwa Inna.
Chapter 7 · 0% Book details