← Book details Rashida Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 17

Sashe 1

Rashida Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

 RASHIDA

Bismillahir Rahmanir Rahim

Zamu fara da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai ya Allah yanda narafa wannan littafin Allah ka sa na gama shi lafiya

By
SHA'AWANATU FARUK DIGGI✍️✍️

08080304152☎️📱

PAGE NA ÆŠAYA 1

📝

Wa ni Babban gida ne shi ba za'a ce na ma su kuÉ—i ba kuma baza'a ce na talaka ba.

Gidan ya haɗu ba ƙarya wasu ƴan mata ne a zazzaune tsakar gidan su na aikin danna waya.
É—ayar na sanye da yellow atamfa da ratsin pink a jiki ta na chatting da wayar hannu ta.

Ɗayar na sanye da riga da skirt ƴan kanki ta na game hankali ƙwance.

ÆŠayar kuma jikinta sanye da Jersey, sai Wando wan da alamu sun nuna, kawai daddana wayar ta ke.

Wacce keda yellow É—in atamfa ce ta kalli mai ragi da skirt É—in tare da faÉ—in."Fatima wai menene na ji Kaka na faÉ—i ne kam?, na ji kamar ta na magana a kan Yaya Rufa'i.

Wacce ke da riga da skirt É—in ta ce "ashe dai ba bacci ki ke ba tun da har ki ka ji maganar da Kaka ta ke, A'ishah ai na san tun da a ka kawo rayuwar ki na san za ki farka".

Fatima bari wallahi ina son Yaya kamar na yi hauka.
Fatima ta ce "ke dai A'ishah ba ri soyayya ta yi wallahi sai dai wa su kam in bar su a ba ya". ta na maganar ne ta na kallon mai jersey É—in.

A'ishah ta ce "ke dai bar ta Kaka ta haÉ—a ta da Yaya Rashid ta kai karshen soyayya", hahaha su ka sa ka dariya.

Wacce ke san ye jersey ɗin ta ce "ɗan Allah ku bar ni na huta duk kun cika min kunne da surutun ku mtsww, kuma wallahi Allah ya tsaran da bakin ku wannan ɗan baƙin halin, za wani ce a haɗa ni da shi".

Fatima ta ce"ha ba Yayana ne fa kuma ki ke wa ni kiran shi da ɗan baƙin hali", ta na maganar ta na dariya.

Mai jersey ɗin ta ce "ni kam ba ra na yi tafiya na sai ku ci ga ba da in da ku ka tsaya", ta shi da yi da ni yar shiga falon gidan ta ci karo da mutum ƙamshin turarin shi ne ya sa ka ta ga ne ko wa ye ta ce "na shiga uku ni Ummi.

ÆŠauke ta da maruka ya yi har sau uku sannan ya wullar da ita a ka sa ji ka ke tim.

Ya ce "ke wacce irin mahaukaciya ce ke, bakya gani ne?,ko bakya ji ne?, kuma ko rai na ni ne ki ka yi ehhe?.

Cikin kuka ta ce "wallahi Yaya ba da niya na yi ma ka haka ba cikin falon zan shiga kawai..."

Bai bari ta ƙarasa maganar ba ya sa ke ɗauke da mari har 2 ya yi tafiyar shi.

Kuka ta ke ba kaÉ—an ba har Æ´an gidan sai dai suka fito su na tambayar ta lafiya?.

Wata mata ce kyakkyawa gaske haushe ya ishe ta, ta hau bala'i,ta ce "ai rainin wayo ne wannan".

Dan iskanci ana magana kin yi wa mutane banza ta yi kan ta gadan-gadan, ai ta na ganin ta yi kan ta ta shi ta yi bayan wata mata kyakkyawa ita ma.

"Daka ta Maryam mai za ki yi ne?, ba dai dukan ta za ki yi ba?,ba ki da tausayi ne kam eh?".

Amma ba ki ganin jama'ar da ke kan ta ana ma ta magana ta yi wa banza.

"Yarinyata faɗa min waye ya dake ki Rufa'i ne, ko Ma'aruf ne, ko ɗan baƙin halin can ne"?.

"Eh Mama Yaya ne wai na je shiga falo ne mu ka yi karo da shi, shine ya kwaÉ—amin maruka har sau biyar".

"Capp sau biyar fa ki ka ce?, wallahi ko yau sai ranshi yaɓaci a gidan nan, Rufa'i kira min shi".

"Ai ko ran da yawa zai ɓaci kenan" cewar Maryam.

Mai ki ke nufi da ran mutane da yawa zai ɓaci?.

Wallahi idan ki ka ɓatawa yarona rai sai na ɓata na wannan sha-sha-shar.

Mama hanun Ummi taja suka shige cikin gida É—akinta ta kai ta toilet ta shiga ruwa ma su zafi Mama ta haÉ—awa Ummi, sannan ta zo ta kama hanun Ummi su ka shiga toilet É—in, ta ce "ki yi wanka kinji yarinyata Allah ya miki albarka", toh kawai Ummi ta ce.

Shi ko Rashid su na can É—aki su na fira da Su Ma'aruf.

Ma'aruf ya ce " babban Yayanmu dan Allah ka yi wa su Mama magana idan aka tashi auren su A'ishah a bamu su wallahi Ni dai ina son Fatima sosai saboda Fatima akwai hankali ga nutsuwa uwa uba tarbiyya gaskiya Fatima maƙura ce", ta na maganar ya na murmushi.

Rufa'i ya ce "babban yaya ni ma ina son A'ishah sosai saboda A'ishah ta iya shagwaɓa ga hankali da sanin ya ka ma ta wallahi A'ishah idan ta na kiran Yayana sai naji kamar na sun baceta saboda ina son mace mai shagwaɓa".

Ma'aruf ya ce "ai Rufa'i shagwaɓa duniya ce wallahi bazaka san mace ba sai ka samu mai shagwaɓa saboda shagwaɓa duniya ce malam".

Rashid ya ce "kai dallah kumin shiru sha-sha-shan banza ko bakwa da magana sai ta yarannan idan son su ku ke yi kuje can ku faÉ—a masu mana amma kunzo kun cika min kunne da surutun banza".

Ma'aruf ya ce" kai malam wallahi idan soyayya ta ka ma ka bazata zo maka da sauƙi ba ga ra kabi komai a hankali naybe ita ma ta bika a hankali".

Rashid ya ce"Ma'aruf wallahi zanci uban ka É—an iska kawai ni za ka na wa maganar nan dan iskanci toh ka sa ni ba yarinyar da na ke ga ni a mace duk maza na ke gani a kayan mata har yanzun".

Ma'aruf ya ce" a a malam ka dai ce zakaci uwata ba dai ubana saboda Uwata ce sa'arka ba ubana ba", ya faÉ—i maganar ya na dariya.

Rashid sarai ya san Ma'aruf zagin sa ne ya yi amma sai ya basar, ya ci ga ba da abin da yake wato danna laptop É—in sa

Rufa'i ya ce "wai babban Yaya sai yaushe za ka fitar da matar aure ne kasan Kaka fa sarai za ta iya haÉ—a ka da Æ´ar banzar da tazo gidan nan wallahi yarinyar da gani ba ta da natsuwa".

Ma'aruf ya ce "wallahi ni kam yarinyar ga ba ki É—aya bata birge ni ba saboda ko shigarta ba ta ma su hankali ba ce

Rashid ya nisa ya ce "ku bar su kawai wallahi ni yanzun a haÉ—a ni da mace ban san mai zance ma ta ba saboda ga ba ki É—aya ban tsara yin aure a yanzun ba". kasan maike da mu na a yanzun wallahi na samu hanyar barin garin nan har komai ya lafa?".

"haba Yayanmu aure fa Rahama ne ba za ka san aure Rahama ne ba sai ka shiga da ga ciki, ka sa mu budurwa cikin Æ´an matan da ke sonka ka ga, ga Rufaida, Ilham,Rumaisa, A'ishah, musamman A'ishah yarinyar na son ka sosai wallahi", cewar Rufa'i.

Tsaki Rashid ya ja ya ce "wai mai ya sa a kullum zancen ku, ba zai wuce na mata ba ne ehhe, kun zo kun cika min kunne da surutun ku mtsww, kura sa wa zaku saka min a zancen sai ƴan iskan can"., cikin ɗaga murya ya ke maganar saboda sosai maganar ta ɓata ma sa rai , falon su ya zauna.

Ma'aruf ya ce "wai mai yasa ba ka san maganar aure ne Rashid ko ka san aure Rahama ne, ko dai ka na da Aljanu ne kariƙa sassauta ran ka mana bana son ɓacin ranka wallahi dan Allah ka yi hakuri ka je ka yi wanka mu fita na gaji da zaman gidan nan".

Rufa'i ya ce "ka yi hakuri my lovely brother ka yi hakuri muje na yi maka wankan sai na shirya ka na goya mu tafi kaji yayanmu".

Hahaha dariya maganar shi ta ba shi wai muje nayi ma ka wankan sai ka ce É—an shekara 2&3, cewar Rashid.

Idanuwa suka bishi da su su ma sun san É—an uwan su kyakkyawa ne dole Æ´an mata su haukace a kan shi, maza ma idan yana dariyar birge su yake ina ga mata.

Dariya ya dai na ganin duk sun saka ma sa idanu ya sa ya hade rai.

Yi hakuri brother ka je ka yi wanka mu na jiran ka fa.

Tsaki ya yi ya yi shigewar sa toilet.

Ma'aruf ya ce "wai ba ka fahimce wa ni abun da ga gare shi ba ni sai na ke ganin kamar akwai wacce yake so kawai ya faÉ—a ma ta ne ba zai ba".

Rufa'i ya ce "ka san halin shi aii irin su ne soyayya kewa kamun mahaukaciya.

"Bara na kira Ummi ta kawo mana abinci saboda yunwa nake ji, kiranta ya yi ya ce ta kawo musu abinci", ta ce "Yaya ba na jin daɗi ne ka cewa Fatima ta kai maku abincin, Ummi na ki muke so dan haka ki yi sauri tun ran ki bai ɓaci ba. ɗip wayar ta katse.

Ta shi ta yi ta je kitchen ta É—auki abincin ta kai ma su.

Ta ce "Assalamualaikum".

"Waalaikamussalam" suka amsa ma ta.

Ta na shiga ya na fitowa daga shi sai kajeren tawul a ƙogun shi duk rabin cinyar shi a waje.

Kallo É—aya ta yi tsoro da farga suka isar ma ta.

Shi ko kallon mamaki ya ke ma ta mai yasa yarinyar nan ta raina ni ne har ha ka.

Kamin ya gama tunanin shi tuni ta gudu ta bar É—akin.

Shiryawa ya yi su ka ci abinci suka fito zuwa inda iyayensu.

Part É—in Umma su ka fara zuwa suka gaida ta suka fito zuwa, part É—in Mama a can suka tarar da su Fatima Ma'aruf ya tsurawa Fatima idanu shi ko Rufa'i A'ishah ya ke kalla shi kam gogan naku ya ka sa ga ne meyasa Idan ya ga Ummi ya ke jin wani iri.

Ta na shirya saboda su ma fita zasu yi.

Ma'aruf ya ce " Ummin Mama ina zuwa wannan wanka haka".
Chapter 1 · 0% Book details