Sashe 9
Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na
girgiza kai ina wasa da hannu na nace
da...da...dama Abba cewa zanyi na... baka dama
kazaba min...mijin" . murmushi yayi yace yar
albarka kenan ni da kaina kai amma naji dadi
Insha Allah kuwa zan miki zabe na gari dazakiyi
alfahari da shi Akwai wani kanin abokina dama
ya dameni da maganar aure, . mutumin kirki ga
nutsuwa da kamala yana da iyali zakuyi daidai da
shi...sam ba na fahimtar sauran zancen don dai
naji da gani . nayi sai can naji yace shikenan
Ayshatu zaki iya tafiya Ubangiji yayi miki albarka
Adaddafe na mike nashige cikin gida Awani lungu
nashiga na zauna turus ina tunanin wace
tabargaza nasake ragargazowa,kaina.?Innalillahi
wa inna ilaihirraji'un nake ja, wannan shine ba
wan ba kanin Na dade ina kuka amma da na
shiga gida ko kallona Umma batayi ba hakan ya
sake tunzira zuciyata Na tabbatar yanzu ba ta ta
tawa tunda ta samu humaira yanzu wa zankaiwa
kukana? .
Ya usman ba ya nan yayi tafiya haka
na kwanta lamo ina tunanin wai ni zan auri
babban mutum mai iyali Duk wani shirye- Shirye
na bikin yan matan ya kankama don yanzu har
saura kwana uku Idan kaganni na rame nayi
fayau don yadda naji wai tare za ahada da
tariyata Hakan ne yake dagamin hankali Da
safiyar Ranar da za akama amaren Abba yakira ni
dakinsa kaina akasa yake Anan naji ya sanar dani
wai yau zaiyi bako da azahar . ."Ayshatu kiyi
masa tarba ta mutunci don babban mutum ne ba
naso kiyi abinda zai zubar da mutuncin gidan nan
daga kai kawai nayi hade dajin wani .
Nauyi
yadanne kirjina yana cewa tashi kije ki tanadar
masa abin saukar baki wannan karon kasa
amsawa nayi na mike da niyyar tafiya amma ina
sai daddafa bango nayi sai dai banyi aune ba
najini kasa ji kake yif. .
Ban farka ba sai agadon
asibiti na ganni ana yimin karin ruwa Nabude
idona jama'a ne birjik afilin dakin Gaba daya aka
shiga yimin sannu.
Ummana taka ma hannuna
cikin nata ta sake cewa sannu Aysha,ina yake yi
miki ciwo yanzu? girgiza kai nayi alamar bakomai
Abba,da yake gefe yace Allah karo afuwa Daidai
lolacin likita yashigo sanye da kayansa na likitoci
yaja hannun da ake min karin ruwan ya zare
robar da take sadar da ruwan zuwa cikin jijiya
sannan yamaida dubansa gare ni yace meke
damunki yanzu? .
Muryata adashe nace masa
"Bakomai" domin ba shida maganin da muwata
yasake aunani da abin awonsu na likitoci sannan
yadubi Abba yace ta samu sauki sosai kamar
yadda na ga ya maka ciwon nata yana tattare da
damuwa sakamakon bincikenmu yanuna ba ta
samu hawan jini ba amma dai ta rage damuwa
saboda nan gaba .
Ta iya samun hawan jinin
Abba ya daga kai yace Insha Allahu za a kula
daga haka ina kallo likitan ya saka kai yafice
Daidai lokacin mayataccen kamshin turaren Ustaz
ya mamaye asibitin hakan ya tabbatar min
dashine ya iso Hakan yasa nayi saurin lumshe
idona don ba na kaunar na ganshi ma Da sallama
yashigo dakin sannan naji muryar humaira hakan
yatabbatar min da cewa tare suke Da sauri
na,sake runtse idon don ita kanta ba na son
nagan ta Bayan gaishe da su Abba da ya yi ina
jin takunsa yakaraso bakin gadon danake anan
naji yace Bata farka ba haryanzu" Abba yace Ta
farka sai dai idan sake komawa tayi Humaira ta
karaso ta dafa kafada ta jinayi kamar namake
hannun ta amma na kyale ta sai dai zuciyata na
matukar tafarfasa har ban san sanda hawaye ya
silmiyo ta gefen kunci na ba Inajin Humaira tace
lah Abba mafarkin kuka ta ke yi?
Abba yace,wane
irin mafarkin kuka kuma ke dai humaira da
shiririta kike matsa in gani Abba yasa hannu ya
shafi hawayen yace da gaskiyarki sai daiba
mafarkin kuka take ba kuka take dagaske .
Wato
Aysha ba zaki cire damuwa daga ranki ba ko?
Ni
banga abinda akayi miki ba da ya tsunduma ki
cikin wannan damuwar Na san kina jina Humaira
tace Abba kayi mata ahankali babu mamaki
abubuwan da suka, faru da ne suke damunta
azuciya Abba ya girgiza kai to ai shikenan Allah
yayi mana magani Amma ya kamata kicire
damuwar nan tunda komai yariga yawuce Gaba
daya haushin maganganun su nakeji Don haka da
sauri na mike namayar da gashina da ya kwanta
agefen fuskata Ustaz yana gefe ya zubomin ido
wata harara na watsa masa Madadin naga
yahade rai sai na ga ya saki murmushi yace
aysha yajiki?
Banko amsa ba nashige toilet ban
san me zanyi aciki ba amma zaman toilet din yafi
min zama ina shakar kanshin Ustaz yana hadda
samin tunani iri-iri Ina shiga na saki kuka
ahankali mai tsuma.Zuciya Ba na so suji muryata
don haka natoshe bakin tsawon lokaci ina toilet
har umma tagaji ta shiga bugamin toilet din tana
fadin ke ayshatu lafiya? kifito ga mijin naki yazo"
wani bugun zuciya naji da karfi na kasa yunkurinnovels / NAGA RAYUWA book 3 part 11
NAGA RAYUWA book 3 part 11
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:17
Saboda ina tsoron ganin fuskar mijin nawa
mummuna ne? kyakkyawa ne?
Allah ne masani
Banbude ba sai da naji Umma tana cewa Ba kys
jine? nace ki bude ga mijin ki da abokansa nan
Da kyar na bude nace Umma miko min hijabina
janyoshi tayi tamiko min tas na goge idona don
inason bawa Ustaz mamaki zan nuna masa ina
son mijina nima turus... .
YAN UWA SORRY
WANNAN PAPER DIN COMPLETE YAYI DAMAGE
TO DAN HAKA MUN SALLAKESHI DON BAZAI
KARANTUBA .
Sai naji yace Gaskiya Alhaji Amarya
tayi Allah yasanya Alheri Inaji katon banzan yana
dashe baki yana "Amin-amin Nagode yalabbai"
sannan ya mike "Bara mu tafi na, ga kamar tana
so tahuta kasan marar lapiya ba kasafai yake son
hayaniya ba .
Amma yayannan naki yanada kirki
Ban ko kalle shi ba suka mike ya iso gurina ya
ajiye bandir.Din kudi na 500 yana fadin "To my
madam Allah yakaro lafiya" cikin wata
dasasshiyar murya ga kana nan ido wasu jajaye
mitsi-mitsi dasu sai fakadeden hanci baje, a
fuskar tamkar faranti Ya juya yasake dashe
gaftara- gaftaran hakoransa A zuciyata nace wai
Allah yayi halitta a nan!" .
"Amarya sai gani
nabiyu" Tamkar nace amaryar ubanka sai dai na
dauke kaina Jin buga kofar ne yatabba tar min da
fitarsu Hakan yasa na fashe da kuka Har ma na
rasa wane irin zafi Zuciyata take yi Da daddare
likita ya rubuta min sallama kasancewar an fara
gudanar da hidimar bikin gidan adinke yake da
jama'a wanda suka zo daga garinmu Potiskum
Ana ta yi min sannu ni dai na samu na shiga
dakinmu Nan din ma .
'yan mata ne aciki amma
cikin tunzura nace "Da Allah ku fita waje kuba ni
waje na kwanta" Ba su musa ba suka yimin
sannu suka fice falo na kwanta Daidai lokacin
Humaira ta shigo da gudu ta fada jikina tace
"Aysha sis,oyoyo, ashe an sallamo ki? amma naji
dadi bara na kira My Ahmad na gaya masa" wata
harara na watsa mata nace "ke ba na son
munafunci na ce miki ina nemansa ne? .
"Haba
Aysha sis, shifa yace idan an sallamo ki na kira
shi ya sake miki ya jiki" Girgiza kai kawai nayi
nace "Humaira fice a dakin nan tun kan cimiki
mutunci Keda Ahmad din"Ta zaro ido tace My
Ahmad din?
Tsaki naja nace "Ko uban Ahmad ne
banzaye munafukai" ganin yadda na matse ina
masifa ne hakan yasa Humaira ta fice sum-Sum
jikinta asanyaye Naja tsaki nace "munafukai
kawai ko kunya ba ta ji ba wani My Ahmad ko
gidan ubanwa yazama na ta?" jinayi anturo kofa
har najuyo zan banka ashar sai naga umma
ce,hakan ya sa nawa bakina linzami Umma
tazauna agefen gado ta ce "tashi Aysha magana
za miyi " Dakyar na mike ta zubo min ido kafin
tace .
"me ya farune?" Nace Name fa Umma?
"Yanzu 'yar uwarki taje,da kuka tana sanar dani
wai tafasa auren Ahmad saboda ta lura kina son
mijinki shin dagaske ne abinda ta fada?" Tamkar
nace "ba haka bane amma sai wata zuciyar ta
sanar da ni wannan ce dama ta takarshe hakan
yasa cikin matukar kunya da jin nauyi nace Eeh
Umma" Umma tazaro ido tace .
"Kina son sa fa
kika ce?" Na daga kai, sai naga Umma jikinta
yayi sanyi, tace "Aysha Kirufa mana asiri don
Allah kada kisa mu abakin duniya Ace duk sanda
muka tashi sha'ani sai wani abu ya faru tunda an
gama magana har ankarbi sadakin humaira to ki
bar mata Ustaz tunda tun farko ke kika ce
bakyason shi aka kuma biye miki yanzu kice
kuma kin dawo kina sonsa . wallahi kada na sake
jin zancen nan 'yar uwarki ce don kin rasa ta
samu bai kamata yazama abinda muwaba .
Ki
share hawayenki shima wannan mijin naki
maikudi ne kuma yanada kirki matarsa mutuwa
tayi wajen haihuwar dansu na takwas" Da, sauri
na zaro ido tace "takwas Umma? . wayyo na
shiga uku Abba ya rasa wanda zai ba wa aurena
sai wannan basamuden?" Umma tayi saurin cewa
"Rufemin baki kada ki tara min jama'a to sai me
don 'ya'yansa takwas ba tare dake za su
zaunaba suna wajen kakarsu, kuma ya ce ma
kuna auren Abu dhabi za ku wuce acan inda yake
gudanar da harkokinsa ba ki ga gidanki ba da
akaje gida tamfatsetse tamkar ba a duniya ba .
"
Runtse idona na yi ina jin Umma ta gama surutun
ta fita.
Tunani kawai na keyi ta yadda zan iya
zaman aure da wannan mutumin Ni maison miji
kyakkyawa na nunawa sa'a amma kudurar
ubangiji ta sauka akaina Kana ta ka ne Allah na
tasa kuma ayanzu na tabbatar ba duk abinda
kakeso kake samu ba sai wanda Allah yaso Ina
kallo Umma ta fice daga dakin zuciyata ina sake
tuna zancen Umma da take ta koda arzikin
mutumin wai har da cewa gida tamfatsetse
tamkar ba a duniya ba to ni ina ruwana .
Da
arzikinsa?
Na ja tsaki yafi a kirga.