← Book details Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 16

Sashe 16

Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ayau na
sake alfahari nakasan cewar ki matata da kika
santalo min kyakkyawan da" Daidai lokacin
Umma da Mami suka shigo mamaki ya kama ni
ganin mami ita da ta haihu jiya amma tafito
yau.Lallai na amince soyayyar gaskiya ce
tsakaninmu kowa sannu yakemun, Maman Ahmad
ta zo kafin asallatu asibitin yacika dan kam da
'yan'uwa da abokan arZiki Ahmad,kuwa sam
bakinsa yaki rufuwa.

Humaira ta dubeni cikin
murmushi ta ce, "Aysha sis yaron nan da Ya
ahmad yake kama ko kadan bai dauko ki ba
Lumshe idoovels / NAGA RAYUWA book 3 part 19 the end NAGA RAYUWA book 3 part 19 the end Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:35 .

Kawai nayi ta sake cewa "Ya aysha haihuwar da wahala?

Wata dariyace ta kufcemin ganin ta da turtsetsen cikinta nace "Ba bayani yarinya sai ranar da kikazo yin taki sannan zaki gane shayi ruwa ne." Murmushi tayi tace tana shafa cikinta "How I wish na bude ido naga babyn.Kawai akwance a gefena batare da na sha wahala ba yana inya inya." Gaba dayan dakin aka saka dariya ganin yadda Humaira ta tsorata sosai Mamina ce ta shigo bayan ta dawo daga wajen likitan mace jaruma tamkar ba ita ce ta haihu ba Ta miko min hannu hade da cewa "Mike mu tafi na amso sallama" Dakyar na mike don jikina kam bai karasa warwarewa ba, duk inda nabi idon Ahmad a kaina "sannu aysha" shine kawai Kalaman da yake jerowa "Hope dai ba inda yake miki ciwo" Na lumshe idona hade da kada kaina koda mukaje gida Hajiyar potiskum ce ta tilastawa Mami tafiya gida fada take tana sakewa "Maza yar albarka ki tafi gida kema fa danya ce sharaf." Murmushi Mami kawai takeyi ganin yadda hajiyar potiskum take nuna mata kulawa hakan ya tabbatar Mata da dinma . bacin rai.Yasanya ta wanke kafa taje har gidansu taci zarafinta.

To haka dai 'yan'uwa suka dunga nunamin kulawarsu.

An yanke shawarar hada sunana da taron sunan Mami za ayi.Inda za ayi ababban hall dina wato AYSHA IMAM KHALIL {A..K RESTAURANT}.

Ranar sunan da safe Ahmad ya sanar da sunan mahaifinsa aka saka wato,Sulaiman, hakan ya sa Humaira ta yi masa lakabi da AKBAR.

An taru sosai ashagalin taron sunan.

Manyan mutane sun halarci babban shagalin inda 'Ya'yan Mami suka ci suna NILFA da NAUFA.

Sunan Mamina da ummana aka saka Mun samu kyaututtuka sosai daga manyan mutane Ustazu na kuwa yana makale da ni tamkar wani zai kwace masa ni.

Tsummun idanunsa suna kaina.

Daren ranar sunan Ya Ahmad ya sameni adaki azaune agefen gado na jingina da gadon ina lumshe ido tsabar gajiya ce take nukurkusata Akbar nake bawa mama.

Fuskarsa adaure yake dubana Yana fareti atsakar dakin hakan ya dan razana ni.

Zuwa can ya zira hannu a aljihu ya miko min ambulan fara tas.

Gabana ne yafadi , narintse ido na ba ta re da nakarba ba .

A zuciyata nace "shikenan an kuma" karbi mana yana fada cikin dakakkiyar murya da tsawa Hannuna na rawa na karba na bude Addu'a nake kafin na karanta.

Abinda na gani ne yasaka ni mikewa ba shiri "Ni kuma da gaske Ya Ahmad?

Ka ba ni kamfanin sarrafa shinkafa?" Dariya ya saki yace "Da tsorata kika yi My Angel?" Na zube gwiwa ta akasa ina sake godiya.

Ya dago ni "Is enough Aysha, duk abinda nayi miki kin cancan ci fiye da hakan.

Da ni da dukiyata duka mallakarki ne.

Na yi miki wannan kyautar ne saboda jajircewa da kike wajen yimin biyayya akan duk abinda na umarce ki.

Kin cancanci sunan MACE TA GARI, MACE MUMINA mai share hawayen mijinta a kowane,yanayi wanda hakan yayi karanci awannan zamanin da mata suke daukan kansu sune a sama bayan Ubangiji yace "Arrijalu kawwamuna alannisa'u" Ya Zama dole mace tayarda itace akasan mijinta shine shugabanta, wanda matan yanzu sundauki hakan rashin wayewa da gidadanci BURIN MACE A ce ita take juya mijinta awannan zamanin babu asarar da ta wuce hakan.

Ba wayewa ba ce hakan . illa dabbanci da tabewa hade da rashin zurfaffan ilimin addini.

A bayyane take macen da ta ke aikata hakan tana jayayya da hukuncin Ubangiji ne da kuma koyi da yahudu da Nasara.

Da suke cewa "What man can do woman can do better".

Karya ce wannan da tsagwaron jahilci.shi ya sa nake godewa Allah da ya tsame min matata daga sahun wadannan mutanen.

Bayan wannan, yanzu fada min abinda kikeso." Na lumshe ido nace "Babu abinda nake so ka gama yimin komai yallabi sai abu daya kayimin Alkawarin ba za ka taba yimin kishiya ba." Cikin murmushi yace "Na yi miki alkawari Aysha ke kadai kin isheni rayuwa." Hawayen dadi ya sulmiyo min don Burina yagama cika nace .

"ALHAMDULILLAH"
Chapter 16 · 0% Book details