Sashe 3
Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AN KOMA
KOTU . ranar da za akoma kotu da wuri muka tafi
da sam bazanje ba sai dai nashirya naje saboda
inaso ayi komai akan idona mune asahun farko
akotun kotun ta dinke da jama'a kowa nason jin
karashen shari'ar ne yakawo shi ina hango
Ahmad yana ta sakar min murmushi ni kuwa
dauke kaina nayi tamkar banganshi ba wanda
rabon da naganshi tun ranar daya ritsani
aharabar gidanmu saboda koyazo bana fita ko
umma tace nafita rokon ta nake ince tabari na
huta Abba ma kuwa bai tilas taminba tsawon
mintuna .
Ashirin muka dauka akotun kafin alkali
Abbana yashigo yana, zuwa kotu ta samu
bakuncin shiru da kanshi yayi umarni afito masa
da,su shany wadanda aka tsare awani daki daya
bayan daya suka dunga fitowa Shany ce atsakiya
gaba dayansu cikin.Wasu dogayen hijabai dasuka
saukar musu har kasa ammafa fuskarsu ta nuna
bazaman dadi akayi akotunba Abbana yakalle su
daya bayan daya . sannan yace da jami'an tsaro
sufito da da mama Atine wacce akayi nasarar
kamo ta kwanaki biyu da suka wuce kanta akasa
tafito amma daga ganin ta ka ga cikakkiyar yar
duniya mutane kuwa suka zuba mata ido ciki
kuwa hardani da nake mamakin karfin hali irin
nata . nakuma yi tur da ita harcikin zuciyata Allah
dai yashirya musulmi Abbana yace kece Atine? ba
ta re dabata lokaci ko tsoro ba ta amsa da nice
Atine kinsan wadannan yaran dasuke gabanki?
Nan ma cikin comfidence ta amsa Nasan su."
Abbana yace mene ne hadinki dasu? dan tabe
baki tayi sannan tace akarkashin kulawata suke
karkashin kulawarki kamar ya? kina nufin
ya'yanki ko ya'yan yan uwanki . kike riko?
Anan
kam tsit tayi takuma sunkuyar dakanta azuciyata
nace munafuka Abbana yadan girgiza kai yace
malama atine muna sauraronki koko zargin,da
ake miki gaskiyane kamar yadda yaran suka ce
babu wata alaka atsakanin ku dukansu yan
tsintuwane? ta daga kai alamar eh yace kina
nufin dukkansu tsintarsu kikayi? to a ina? kuma
da yaushe? awanne gari kikatsinci har mutum 35
musamman waccen yarinyar danake hasashen jini
nace saboda matsananciyar kamar dasuke yi da
diyata,Aysha dasauri takai dubanta,kaina ta sake
mayar da dubanta akan yar rikonta Shany atake
naga tasaka,hannu tana yarfe.Gumi alamar rashin
gaskiya kuru-kuru yabayyana afuskarta .
Abbana
yadanyi rubutu sannan yadago yasake ce mata
malama atine kinyi shiru inason sanin labarin
wannan yarinyar shany da yadda kika sameta
gaskiyarki ce hanya mafi sauki dazata kubutar
dake karya kuwa itace zata tsunduma ki akogin
nadama matukar na,gano gaskiyar lamari
Ahankali ta dago kanta sanin cewa babu mai
kubutar da ita hakan yasata shiga rattabo bayani
"kamar yadda . ka fada dagaskene wadannan
yara tsintarsu nayi wasu kuma aasibiti nasamesu
shekaru da dama dasuka wuce nima karkashin
wata mata nake da sana'arta kenan .
FATAUCIN
YARA MATA . kai har da mazan ma idan tasamu
faraga "asibitoci takebi don samun yara marasa
galihu kodai shegu kokuma wadanda iyayensu
sukayi accident suka mutu akarasa danginsu
kokuma idan anhaifi yan biyu tayi cinikin daya da
nurses ko likitoci subata daya batare da mai
haihuwar ta saniba Nikaina a irin hakan tasameni
ma'ana ni shegiyace duk abinda takashe mana
muna yara to idan mungirma fanshewa take
akanmu kodai ta mayarmu karuwai kodai tayi
futaucin wasu zuwa wata kasar ta yadda za
adunga bata,kudi duk karshen wata wadanda
tamayar karuwai kuwa da zarar sungirma andaina
yayinsu ba ta samun komai atare dasu to sai ta
sallamesu sukama gabansu don takan fada ba a
aikin banxa akano .
A irin haka nima nafito Ne
acikin wadanda aka sallama nima nakama gidan
kaina saina tsunduma kaina cikin harkar da takeyi
na shahara sosai harnaso nafita nima asibiti nake
. zagayawa aduk cikin kasashen Nigeria wannan
yarinya da kake magana ina,matukar alfahari da
ita aduk cikin yarana saboda tana da kwazo da
basira wayo da hikima shiyasa bana manta
tarihinta .
A ASIBITI NA SAYO SHANY.... .
Gaba
daya naga abba yadago yana sake kallon ta
muryarsa na rawa yace mata wa...wanne...wane
asibitin? shiru tayi da alama,tatafi tunani sai can
tazaro wayarta,ta kunne tashiga bincike kotun
kuwa zuwa lokacin tuni tadau kace nace har
saida Alkali yatsawatar sannan Atine ta dago
kanta tace Na sa mota a .
NASHE SPECIALIST
HOSPITAL . aranar lahadi 17 gawatan july
shekarar1995..." gaba daya naga Abbana yazaro
ido umma kuwa arazane tamike tana nuna Atine
da yatsa muryarta na rawa,kincu.Cemu... .
tabbas wannan yatace jininace! ranar dana haifi
ayshata kenan kuma a asibitin nashe..." novels / NAGA RAYUWA book 3 part 4
NAGA RAYUWA book 3 part 4
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:04
Gaba daya hankalin jama'a yakoma kan umma
Abba ne yadaka tar da umma tahanyar yimata
umarni tazauna umma tazauna tanajan
"Innalillahi" Ni kaina bugun zuciyata alokacin
yakaru Abba yace Atine ina jinki Awajen wa kika
siyeta? likita? ko nurse? shiru tayi har saida
yadaka mata tsawa,sannan tace awajen likita ne
bisa jagorancin wata mata "wata mata wa?
yasunanta?
Abba yafada cikin matsanan cin
mamaki Girgiza kai tayi tace gaskiya na manta
saidai na bincika shiru .
Abba yayi yashiga
rubuce-rubuce sai can ya dago yace ina
tunanin.Tilas sai annemo matar nan sannan kotu
za ta san hukuncin dazata yanke matar ce da
likitan zasu tabbatar mana da shany diyar wace
ce don haka asakamakon haka kotu ta dage
zama zuwa nan da wata guda za atsare Atine har
zuwa lokacin kuma kotu ta ba da belin yarancan
tunda ga babbar me lefi ankama sai dai zasu biya
minista makudan kudaden da suka daukar masa
idan yana bukatar hakan koda muka isa gida
jikina asanyaye nake jan kafata ina lura da umma
ita ma nata jikin asan yaye yake matuka . har
raina ajagule yake gaba daya fatana daya kada
Allah yasa zargin danake yatabbata bakomai
kuwa nake tunani ba sai kada Allah yasa
MAMINA tana da hannu dumu-dumu acikin
wannan shari'a ba idan hakan ta faru ya
makomar mamina zata kasance? wasu hawaye
naji sun sulmiyo min. . haka na kwana da zancen
azuciyata da safe ma ko karyawa, banyiba
nasamu umma dazancen murmushi tayi tace ni
ma ina tsoron faruwar hakan sai,dai kunyi daya
da abbanki shima zargi da hasashen dasuka
shiga zuciyarsa kenan sai dai zankwabeki kamar
yadda na kwabe shi kada ku daga zan cen nan
wani yaji don ba lallaine tunanin yaxama gaskiya
ba amma ya,rantse idan dasaka hannun ta bazai
mata,sassauci ba" Ahankali naja numfashi hade
da furta kai jama'a duniya abar tsoro ce . wallahi
sam hankalina yagaza kwanciya saboda tsoron
kada akama mamina da wannan gundumemen
laifin hakan yasa nayi saurin shiga wanka ina
fitowa, ko mai bansha fa ba nazira doguwar riga
ta da hijab Adaki nataradda umma karya naimata
akancewa zanje gida nadebo wasu kayana bataki
ba sai dai tacewai natambayi mijina kamar
nafasa zuwa sai dai kawai,natura masa, text
nasanar dashi zanfita, banga amsa ba amma
haka nashir gama umma karya nace yace sai
nadawo .
Daga nan nasaka kai ko direba
bannemaba don ba na so asirina yatonu,hakan
yasa natare adaidaitasahu . . sai Nasarawa
gidandsu mamina da sauri nafada gate,din gidan
bayan na sallami mai adaidaita sahun A falo na
sami hajiya da mami wannan karon hajiya da
walwala fal afuskarta ta amsamin har mamaki
abin yabani mamina kuwa tashi tayi ta rungumo
ni tana fadar oyoyo ayshata . nidai murmushin
yake nake saki bayan munshiga daki mamina
tadubeni tana murmushi ayshata ya aka kare da
zaman kotu? wannan karon tun da naga kintsira
nace to mekuma zankoma nayi? dan murmushi
najefeta.Dashi "Aikuwa da kinsha kallo don
wannan yarinyar dai ana kyautata zaton nida ita
twins ne...." da sauri mami tazaro ido tace Inji
uban wa kuma?
Nagyara zama cike da mamakin
irin razanar da mamina tayi nace Inji matar data
rainesu ta shaida haka Don kuwa rana daya da
lokaci da asibitin da aka haife mu duk dayane
matar ta tabbatar siyenta tayi a asibitin bisa
jagorancin wata mata" Sake firgita tayi tace
What? kina nufin ta fadi sunan matar? . girgiza
kai nayi nace kodaya sai azama na gaba Abba
yace lallai anemo wannan matar da likitan don
sune za su . ba da tabbacin komai mamina
zagaye ta shiga yi a dakin idan ba idona ba ne
yagaya min sai naga kamar gumi take sai can
tace Allah ya kyauta amma hakan da mamaki
matukar gaske Ban dade sosai ba nabar gidansu
mami yanzu kamzuciyata ta aminta,da zargina
don haka na ratse wani lungu na sha kuka na
Innalillahi kawai naketa ja harna isa gida sai
danaje kofar gidan sannan na tuna karyar dana
shirgawa ummana nacewa, kaya zandebo don
haka dasauri najuya nanufi gidansu Asma'u Allah
yataima keni tana nan Nadebo kayanta sannan na
nafo hanyar gida Adai-dai sabon gidansa
nahango shi da wannan kodaddiyar matar tasa
da alama fita zasuyi haka, kawai sai naji wani iri
araina bansaniba ko kishi ne oho. .
Na sa kai zan
wuce ba tare da na kulasuba amma, namakaro
donjin Uztas nayi yana fadin yan mata ina kikaje?
Najuyo namasa wani irin kallo mai fassara kala-
kala gani nayi yasake wani fari yayi kyau fiye da
lokutan baya Ban saniba ko don yanzu hankalinsa
ya kwantane take naji wani kululu ya cake min
zuciya bansaniba ko kishine . kishin da ake fada
wucewa nayi ba ta re danace masa ko "A" ba
Babu abinda,yafi bani haushi saiganin danayi
Uztas kobi takaina bai sake yiba yakoma gurin
matarshi hakan yasa naji wasu zafafan hawaye
sun zubo min tabbas .