Sashe 8
Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma ta girgiza kai da alama
tana tunanin yadda za ta fuskanci Abba da
wannan maganar ne batace komai ba tamike
tatafi Nikuwa na rintse idona don kam zanfi son
barin kasar nan ko ba komai bazan san lokacin
da aka daura auren ba balle Zuciyata tayi kunci
Don yanzuma jinake tamkar ciwon zuciya zai
kama ni. .
Shiru har kwana biyu banji amsa daga
bakin Abba ba na tabbatar bai amince ba kenan
hakan ya sanyayar min da gwiwa Ina kallon,
Humaira kullum nanike da waya akunnenta na
san ba komai take ba sai hirar soyayya da Ahmad
hakan yasake bakanta min rai harnaji tamkar
nacanja daki sai dai hakan ba zata yiwu ba don
nasan kiri-kiri za ace BAKIN CIKI nake, . sai dai
kullum fa ina cikin uwar daki har umma tagaji da
tambaya ta taja,bakinta ta tsuke ina lura da ita
kullum tana kitchen tana koyawa yan matan
girke- girke ta tattara al'amarina ta saka agefe
Hakan yatabbatar min danayi .
Rashin UWA MAI
SO NA MAMINA Yau da daddare bayan mun
gama cin abinci har namike tsam zantafi Abba
yasa baki yaki rani Bina yayi da kallo yace
kishirya da wuri gobe akwai tafiya potiskum duk
na lura yanzu kintsiro da wani hali na zama ke
kadai ba tare da munsan laifin da aka yi miki ba"
Mikewa kawai nayi nace to Allah yakaimu sam
banso wannan tafiyar ba amma babu yadda zanyi
Da asuba babu wanda yakoma barci har humaira
da ta kusan raba dare tana waya,da ustaz Na
lura ustaz,har yafi sonta akaina saboda bini-bini
yayi mata waya ita kuma tamkar mayya kullum
tana makale da waya babu jan aji babu komai sai
wani rawar kai shiri suke haushinsu kawai nakeji
sosai araina suna ta caba kwalliya nikuwa wanka
kawai nayi nazira wata bakar doguwar riga
ta,mai na shafa kawai kai kace nidin matar
mamaci ce wacce take takaba karfe 9:00 muka
hau motar yaya usman na fada da sauri yaja mu
dani da matarsa yana yimin tsiyar ramar da yaga
nayi bayan hankali ya kwanta murmushi kawai
nayi masa ba tare da na tofa ba shi ma din bai
sake . cewa komai ba duk da na so yace din
kodon na gaya,masa abinda yake,sani rama sai
dai gani da zurfin ciki Ba kasafai nake iya fadar
matsalata ba ba tare da an tambaye ni ba Haka
har muka isa potiskum Ni dai ina zaune cikin
mota jigum sai yaya usman ko matarsa sun
sakoo ni azance sannan nake shiga sai gaf da
la'asar muka shiga garin potiskum din munriga
kowa isa Hajiya da sauri ta tareni cikin farin ciki
take cewa kaga baiwar Allah tun dazu nake zuba
idon ganinku Ayshatu fargabata daya dawane
idon zan dubeki?
Murmushi kawai nayi na
durkusa nagaishe ta Don ni dama ba sosai na
kware da wani wasan jika da kaka ba Ta kama ni
Zoki zauna nasake jaddada ban hakurina a
wajenki Duk da dai,kince kinyimin afuwa
Akunyace na zauna nace hajiya kibar maganar
tariga ta wuce Daidai lokacin Abba da Umma
suka shigo Abba dafada yashigo yana fadin ina
usmanun wai kai yaushe zakayi hankaline? . ina
ce har waya nayi maka akan cewa karage gudu
yaya usman yace Abba ai banyi wani gudu ba
Nan suka zauna suna gaisheta hajiya kuwa
bakinta .
A bude,take kallonmu,ni da humaira fadi
take Ba shakka ga zahiri nan babu bambanci ko
digo tsakanin ku Umma ta tuntsire da dariya tace
uhm-Uhum,da bambanci sosai Ayshatu bata da
kwaramniya humaira akwai dan banzan rawar kai
humaira ta zunbura baki tace kai umma nidin? ya
muhammad yace sosai ma kuwa kike da rawar
kai Abba yace humaira kam ba da ma humaira
kuwa gaba daya ta fara dire-diren kafa tana
kukan shagwaba ya faruk ne yakamo hannun ta
yace Quite my friend kada kiyi kuka rabu dasu Me
za ayi da mutum mai kunbiya-kumbiya?
Da abu
aransa ya fada yana kunshe dariya aciki Nakuwa
zabga masa,harara don na san dani yake. . ***
*** *** .
Kwana biyu mukayi a potiskum,bayan
munzagaye dangi muka dawo gida Nidai fara'ar
dole, nakeyi a kan babu yadda zanyi tunda muka
dawo Umma tafara zancen shirye-shiryen sa
ranarsu Don ance wai suhudu za a aurar su yaya
muhammad kowa daidaya guda uku kuma
malaman mu ne suka nemi aurensu don nuna
tausayawar su garesu Ranar laraba 'yan sa ranar
sukazo 'yangidan su Ahmad ne harda kanwarsa
khadija ta saka ni adaki tana tuhuma ta akan son
jin dalilin dayasa naki dan uwanta har aka
musanya masa da kanwata murmushi kawai nayi
na ce KADDARA CE! . zo kaga lefen humaira
akwatina goma sha biyu harda nasaka rana
kayane sosai dankar aciki tamkar ba asan ciwon
kudi ba wata uku aka saka cif Humaira sai rawar
kai take bini-bini ta daga waya kaji tana kashe
murya hade da,cewa my Only wannan iyayi da
take,shiyake dugunzuma min zuciya Nayi tunani
ita ko kunyata ba ta ji Nashige daki kuka kawai
nakeyi har zazzabi ya rufeni ruf ba ta re da sanin
komaiba sai ga shi nice har da kiran wayar Ustaz
amma sam yaki dagawa . sai rejecting call dina
yake Balle na bashi hakuri ya janye kudurinsa na
auren kanwata Yau da safe ko fita banyiba daga
daki maryam tashigo take sanar dani wai ana
kira na Afalon abba da kyar na mike nazira
hijabina na isa falon Abban shi da yan uwansa,da
suke yan maza har su baba yahya suke zaune
sun tasa kayan lefen humaira agabansu Allah ya
sa su ruguza maganar Auren... . na ayyana hakan
araina su kansu na san sunsan hakan baidace ba
sai dai sabanin haka ji na yi Baba yahya ya rufeni
da fada da nasiha yace "Yanzu Ayshatu saboda
wannan kaddara ta afku shike nan sai kice
kinrataye sunnar manzo {S.A.W} kice wai ke
abarki kitafi karatu waje? . to tur da wannan
shawara taki Adanginmu kaf ba mu bar maza sun
tafi waje karatu ba balle mubar mace kuma gata
daya da za muyi miki shine kifitar da miji kiyi
aure shine mutuncinki mutuncinmu mu ma yanzu
tunda Ahmad ba kyason sa wa kika tsayar? .
kasa ce musu komai nayi ruwan hawaye ya fa ra
ambaliya akuncina nace babu wanda na tsayar To
mun baki sati kifitar da miji tunda dai..ovels / NAGA RAYUWA book 3 part 10
NAGA RAYUWA book 3 part 10
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:14
Mijinki na baya ya sanar da mu bai dora miki
idda ba Tashi ki tafi Allah ya kawo nagari Da kyar
na ja jiki na isa daki "Na shiga uku" .
Nafada
ahankali Najawowa kaina masifa meya,kaini furta
ba na son Ustaz?
Nasan halinsu baba yahya sarai
da zafin rai tunda ya furta sai na fitar da miji abu
ne mawuyaci ya janye kaina yayi dum sakamakon
rasa mafita da nayi alokacin kam na san tabbas
na yi rashin uwa da da mami akusa, da duk
hakan ba ta sameniba ga shi ko kira lambar da
takira ni bana samunta Hakan yatabbatar min da
bayan mungama waya canja layi tayi Nasake
rintse idona wasu zafafan hawaye, suka zubomin
Da daddare kamar wasa na dau Ipad dina da
niyyar duba facebook ko whatsapp, wanda rabon
da na bude su harna manta sakon Mamina ne
yashigo ta Whatsapp da sabon account din data
bude kawai.Cewa tayi Aysha yakike? cikin
tsananin farin ciki na tura mata hoton dan aljani
mai alamar kuka akasa na rubuta;"Rayuwa ta
yimin zafi MAMINA, . saboda rashinki akusa dani
wallahi mami yanzu na tabbatar ni marainiyace
na rabu da, .
Ustaz an maye masa gurbina da
humaira kanwata kuma Allah mami inason sa
haryanzu Gashi Baba yahya ya rantse sai na fitar
da miji mami na rasa yadda zanyi kibani
shawara" .
Tsawon lokaci ina sauraron amsar
mami shiru har na fitar da ran samun amsar ta
saikuma ga sako ya shigo .
"Aysha kenan
haryanzu kinason Ustaz meyasa kika cuci kanki
wajen rabuwa dashi?" . cikin kuwa na sake rubuta
mata "mami wallahi kaddara da kuma son ja
masa aji." Dariya taturo min sannan taturo min
"kisami Abbanki ki sanar dashi ba ki da wani Zabi
yazaba miki miji da kansa idan yaji kince hakan
nasan zai fuskanci har yanzu kina son mijinki
idan yaso sai adawo da auren kanki."Murmushi
natura mata alamar jinjina cewa tayi kawai "Sai
da safe ina karatune" .
Daga haka ta bar online.
Kwanciya nayi akan gado ina dariya Na tabbata
shawarar nan ta mami tayi don haka nake Allah-
Allah safiya tayi Da azama na mike nashiga toilet
nayi alwala ina rokon Allah yasa abinda nake
nema yatabbata da sassafe nayi wanka na shiga
don tanadar, wa Abba hadadden .
Break fast
koyaji dadin amsa bukatata Da sauri ina ta
addu'a azuciyata ina kallonsu humaira suna jifana
da kallon mamaki ganin yadda nake sakin fara'a
a zuciyata kuwa fadi nake .
"yarinya kwaleleniki
mijina yafi karfin ki ko ta kaka sai na kwato shi" .
Ina yi ina wakar MAI SONA MAMINA Umma dai
murmushi kawai take yi dakaina nakaiwa Abba
breakfast bayan na gaishe shi cikin mamaki yake
cewa Ayshatu yau cutar tawarke ne naga kina
walwala? .
Murmushi nayi na sadda kai na kasa
Abba yasake cewa ko ansamo min surukine?
Nasake sunkuyar dakai nace "Dama Abba akan
zancen ne..." Da sauri yace sunce zasu turo ?