Sashe 14
Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sai karfe 8:00 na dare kowa ya baje sai ni
kadai don Ustaz ya tafi shopping.Sai alokacin na
fara jin tsoron gidan musamman da na ji motsin
kofa aibansan sanda na kudundune jikina ba
Hankalina bai kwanta ba har sai da naji sallamar
Ustaz jikinsa asanyaye ya zube ledojin da suke
hannunsa ya zauna agefen kujera ya kuma zuba
uban tagumi da duka hannayensa idonsa a
lumshe.
Da azama na mike na isa gareshi na
durkusa gabansa Dafa gwiwoyinsa na yi nace
Lafiya Ustaz.?
Baibude idon ba illa ya matse
hannayena cikin nasa Tsawon lokaci kafin ya
bude idon.
Araza ne,nadu be shi ganin yadda
idonsa ya,yi jajir nace "Na shiga uku Ustaz waye
ya mutu?" Ya hau girgiza kai "Ni namutu Aysha
wallahi na kashe kaina Bansan dalilin da,ya sa
mama ta tilasta min auren Hameedah ba Aysha
ba zan iya adalci tsakanin ku ba wallahi yau daya
da zanbarki ba kiji yadda zuciyata take bugu ba
ba na son nafada halakar Ubangiji don kuwa ya
umarce mu da muyi adalci atsakanin matanmu. .
Ya sanar damu idan har ba za muyi adalci ba
kada ma muyi biyun Aysha bazan iya adalci
tsakaninku da hameeda ba ya ya zanyi? ya sake
runtse ido Ni kaina hankalina yayi masifar tashi
don wallahi na manta da wata Hameeda Yanzu
kenan Ustaz raba mana kwana zai sunga yi?
Zaidunga zuwa da kin wata ba niba Zan bude ido
wata rana naga babu Ustaz agidan nan yana can
wajen wata yana nunamata soyayya kamar yadda
yake nuna min? na rintse idona kai ni ma wallahi
bazan iya ba ban san lokacin da na fara kuka
wiwi ba Ustaz ma kukan yake yi ahankali yana
kuma bubbuga bayana alamar rarrashi.
Daidai
lokacin wayarsa tayi kara alamar ana kira Amma
Ustaz yayi banza da wayar sai ni nasa hannu na
dauka "MY WIFE 2" Naga an saka da sauri na
ajiye masa wayar akan cinyarsa na kuma mike
nashige daki da gudu Na fada kan gado tsawon
lokaci sannan Ustaz ya biyo ni ya tsaya abakin
gadon ban san me yake tunani ba har zuwa
lokacin da ya hawo gadon ya dago fuskata na
rintse Ido "Ta shi Aysha magana zamuyi" Na
bude idona .
"Kiyi hakuri kowa da irin tasa
kaddarar mu.Tamu kaddarar kenan Zan tafi ga
wata dattijuwa nan da zata tayaki zama a falo na
miki kiyi ta jan Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un
Zan leko nagan ki gobe tunda sai jibi zandawo
nan Da kudi a drawer dakina ko zaki bukaci wani
abun" Rintse ido na sake yi na fashe da kuka
hade da damke hannunsa kada katafi Ustaz
wallahi in ka tafi zuciyata zata,iya fashewa.
"Babu abinda zuciyar ki za tayi Aysha don ba
akanki aka fara kishiy ba kiyi Nazari da hakan..."
Ina kallo Ustaz yajanye hannunsa ya tafi Wani
kukan ya sake kwacemin shi kenan ya tafi
wajenta A yau ba Ustazun Aysha bane Ustazun
hameeda ne kuka yaci karfina sosai tabbas kishi
bala'i ne sai a yau na sake jaddada hakan Ni ce
har karfe ukun dare ina kwance a haka sam na
kasa rintsawa Juyi kawai nake akan gadon ina
hango fuskar Ustaz yana ta zanga wa hameeda
soyayya kamar yadda yakemin na sake rintse
idona still hakan nake,sake gani Kawai ji nayi ina
furta kalmar"Na shiga uku yanzu haka zanyi
rayuwar aure da Ahmad duk .
Sanda zai tafi gurin
wata?
Na ji kamar zan mutu Anya hakan zata
yiwu?
Na dau wayata ina duba lokaci karfe
3:00na dare na ga ni Ban ji shakkar komai ba na
danna lambar mamina da niyyar kiranta Tsawon
lokaci tana ringin kafin Mamina ta dauka ji nayi
tace Aysha lapiya Atsahon daren nan?
Cikin
shisshikar kuka nace "Mamina na kasa barci
zuciyata ciwo take ga kaina yayi nauyi Cikin
kidima itama Mamin tace "Subhanallah!
Shi Ustaz
din yana ina?ya barki baku tafi asibiti ba?" Na
sake sakin kuka da karfi nace Mami ya tafi
wajenta Cikin kidima itama Mamin tace ita wa?
Na ce Mami Matarsa mana hameeda"Mami
tasaki nannauyan ajiyar zuciya tace "Wallahi
kinbani tsoro Idan na fahimci matsalarki Aysha
kishi ne ya kamata kuwa ki ajiye shi agefe duk da
ansan yana da ciwo amma yana zuwar wa
mutum a inda mutum yadau keshi idan kadau
keshi da zafi zaizo maka da Zafi, idan kuwa
kadau keshi da sauki sai ya zo maka asaukake
Don haka inaso ki dauke shi da sauki please and
please Aysha ki yi koyi dani da Ummanki, kada ki
ba mu kunya"
A novels / NAGA RAYUWA book 3 part 17
NAGA RAYUWA book 3 part 17
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:31
.
Na rintse ido nace"wallahi Mamina bazan iyaba,
kowacce mace da yadda Allah yayita ni Allah
yayini acikin mata masu tsananin kishi Ba zan
Iyaba mamina"Cikin tsawa mami tace "Zaki iya
aysha kowacce mace koya take har ta saba.
Haka ke wacce irin yarinyace mata nawa aka
yiwa kishiya suka zauna lafiya..." Fashewa
dakuka nayi ganin yadda Mami ta harziko Cikin
tattausan lafazi mami tace "aysha saurare ni kiyi
shiru haka maza ki tashi kije ki yi alwala kiyi
sallah zaki samu sauki azuciyarki kinji?maza
tashi aysha." To Nace sannan nabi shawarar
mami na mike nashiga toilet cikakkiyar alwala na
daura ina fitowa na fuskanci alkibla ina sallah ina
hawaye acikin sujjada na dade ina kaiwa Allah
kukana akan ya yaye min wannan matsanan cin
kishi koda na gama agurin na kwanta ina mayar
da ajiyar zuciya Tabbas wallahi kishi ciwo ne
babu maganinsa sai addu'a bansan lokacin da
barci ya daukeni ba Karar waya ne ya farkar dani
daga nannaiyan barcin da ya dauke ni ina kai
dubana kan screeb din wayar naga sunan
REALITY ya bayyana. .
Na san Ustaz ne nayi
tsaki naduba agogo karfe 5:45 yaje
yasha,soyayyarsa da barcinsa sai yanzu ya tuna
dani. idan har ya damu dani meyasa bai kirani ba
tun jiya?
Gaba daya kashe wayar nayi namike
nashiga toilet Ko da na idar da sallar barci ne ya
sake yin awon gaba, dani akan sallayar.
Shafar
fuskata da naji anyi shi ya sa nabude idona.
Ustaz ne zaune agabana ya zuba min ido cikin
tausayawa Ban mike daga wajen ba illa ma
dauke, kaina da nayi daga kansa na sake lumshe
idona Ji nayi yasaki ajiyar zuciya yace "Aysha kiyi
hakuri please ban san yadda zanyi ba Ni kaina sai
ajiya na sake yarda ba Zan iya adalci
atsakaninku ba Ina tare da hameeda ne kawai
amma ruhina kacokam yana kan aysha ko da na
kwanta juyi kawai nake ina tunaninki Gashi ba
damar kiranki don ina tare da ita Zai zama kamar
cin fuskane" Sake tunzira zuciyata yayi jin yace
wai yana tare da ita Wato yana sanar da ni tare
su ka kwana a daki daya.
Yakamo hannuna tashi
Aysha ba dai anan kika kwanaba akasa." Na
dauke kaina cikin tsiwa nace "ina ruwanka . dani,
tunda kai kayi kwanan farin ciki ka kwana a
luntsumemen gado tare da farin cikin ranka Ajiyar
Zuciya ya saki sannan ya saki murmushi yace
kwantar da hankalinki MY ANGEL!
Daga yau
Ahmad ya zama naki ke kadai banbar gidan ba
sai da NA SAKI HAMEEDA Wai don gulma kuma
sai nazaro ido nace Saki?
Ustaz why?
Yalakuce
min hanci "Kaji gulma Natabbatar har zuciyarki
cikin farin ciki kike" Na girgiza kai "Ko daya
Ustaz, ko ba komai Hameeda mace ce yar uwata
ba zanso abinda yafaru da ita yafaru daniba me
ya sa, ka sake ta Ustaz?
Da ka barni ahankali
zan saba", Ahmad ya dangirgiza kai "Ni ba zan
saba ba Aysha, sam ba zan saba da rashin adalci
ba koda Allah yace mu auri mace sama da daya
saida ya umarce mu da muyi adalci.
Idan nakasa
adalcin me kike zaton zai faru dani? tashi fa,zanyi
ranar lahira da shanyayyen barin jiki Me ya fi
hakan takaici? shiyasa na amince rabuwar mu
shine mafi alheri Tun daga mota da na fita, raina
abace yake har naje gidan babu fara'a afuskata
Hameeda na da kirki tatareni da abinci amma .
wallahi ko fuskarta ba na gani Kece kawai acikin
idona Har muka kwanta na kasa yi mata kulawa
irin ta aure duk da na lura da bukatarta kenan
"Shiyasa da safe na yanke shawarar rabuwa da
ita bayan na mallaka mata makudan dukiya da
gidaje sannan muka rabu kuma ta min
kyakkyawar fahimta haka iyayenta ni ma su
Abbana ba su yi fushi da ni ba don haka Ayshata
takwantar da hankalinta Ahmad na tane ita
kadai" Da safe na ga Mamina da ummana
mamaki ya kamani ganin, dukansu fuskarsu
ahade take gabana ya,shiga faduwa har ina hada
harshe wajen fadin "Lafiya Mam?" Ai kuwa ta
aiko min da wata harara hakan yasa na gumtse
bakina Cikin fada Umma tace "kin kyauta Ayshatu
saboda bakin kishinki shine kika sa sai da Ustaz
ya saki matarsa" Da sauri na zaro ido nace "Ni
kuma? wallahi Umma ba ruwana" Mami ciki zafin
rai tace karya kike Aysha ya mukayi dake jiya?
Babu ruwanta mami nida kaina na saki Hameeda
saboda ba na daga cikin wadanda za su iya rike
mata biyu.
Bazan iya adalci atsakanin wata
macen da aysha ba dakai na nayanke .