← Book details Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 16

Sashe 10

Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka aka shiga
gudanar da shagalin biki ni.Kuwa ba na shiga
kowace sabga koda yaushe ina daki akwance ina
ganin yadda wasu suke kallo na a dafe da alama
suna hasashen yadda nake yi wa 'yar'uwata
bakin ciki ne ni dai bin kowa nake da kallo
fuskata kuwa ta yi fayau ni kaina na san na rame
matuka da gaske.

Ranar da ya kama za akai
amare a ranar naji labarin wai, ni ma zanbi mijina
Abu- Dhabi, Hankalina ba karamin tashi yake yi
ba idan na tuno yadda mijin nawa yake Tunda
magriba na fara jin hayaniyar motoci Humaira ce
ta shigo da gudu ta, fada jikina ta rungume ni
tana wani kuka maitsuma zuciya Hakan ya sa ni
ma na saka kuka ba tare da na shirya hakan ba. .

A marairaice kanwar umma ta shigo, ta ja hannun
Humaira tana fadin "Kuyi hakuri haka rayuwar
mace ta ke takaitacciya ce agaban iyayenta" Ina
kallo takama humaira suka fice.Nasan shi kenan
na rasa Ustaz, har'abada zuciyata ta karye na
sake fashewa da kuka Gidan yayi tsit duk an
fashe,kai amare daga ni sai Umma ji nayi anturo .

Kofa an shigo In bude ido naga Abba ne da
Umma Abba yazauna abakin gadon cikin muryar
rarrashi yake sanar dani natashi naje mijina yazo
tafiya dani "Ayshatu ina sake baki hakuri akaro
na biyu akan duk abubuwan da suka,faru a baya.
.

Sannan ina miki nasiha da kibi mijinki sau da
kafa saboda ko ba komai aljannarki atafin kafarsa
take.

Na sani Ayshata mai biyayyace don Allah ko
da bakya sonsa kidaure kibishi.

Alhaji Danjuma
mutumin kirki ne" Da sauri na sake fashewa da
kuka jin sunan da Abba ya fa da wai Danjuma.

Kai daga ji ka san an rayu akauye. .

Umma tace
"To mene ne na kukan tunda ta faru ta kare.

Ubangiji ya ba ku zaman lafiya Tashi maza ki
kintsa yana jiranki a mota airport za ku tafi."
Cikin rarrashi Umma ta tilasta ni nashirya cikin
wata rantsattsiyar laffaya, fara.

Ta sha ado da
zare marun. kayan kam sun amshi jiki na caras
na fito tamkar 'yar tsana Na raya araina ina ma
gidan Ustaz za a kaini ba gidan wannan mutumin
ba." Da kyar nayi sallama da su ina kuka cikin
karaji yaya usman ya rike hannuna ya rakavels / NAGA RAYUWA book 3 part 12
NAGA RAYUWA book 3 part 12
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:19
Ni har bakin motar yana sake jaddada min na yi
hakuri duka rayuwa nawa ce.

Idan dan Adam yayi
duba da abubuwan zamanin baya da suka shude
zai gane rayuwar duniya ba,komai ba ce jin Yaya
usman kawai nake har ya bude bayan motar ya
saka ni yana rufe motar na sake fashewa da
kuka.

Daidai lokacin Danjummai ya juyo daga
kujerar gaban motar ta masu zaman banza sai ji
nayi ya ce "Shatu sai hakuri a,rabuwa da iyaye
akwai ciwo amma ga 'yanmata hakan yafi ciwo
ba ga ke da ba wannan ba ne aurenki
nafarko".Tsit nayi saboda jin haushin kalamansa
Ji don Allah ko hakan shine salon da ya dace
ararrashi amarya?

Sam babu riba ga auren
babban mutum.

Harmuka isa airport ban sake
tofa komai ba naja bakina na tsuke ina sake
taraddadin yadda zan zauna da wannan mutumin
Ina,jinsu suna ta shewa suna hirar kasuwancin su
Isarmu airport tayi dai-dai da lokacin da ake ta
kiran passenger ciki kuwa har da mu ana sanar
sauran mintoci kadan jirgi yatashi raina a bace
nake bin sahun mutuminda da za abani dama
nakashe wani shi zanfara kashewa .

Muna hawa
jirgin hancina yafara shakar kamshin Ustaz Nan
take na fara waiwaye awautata wai ko zanganshi
amma sam ban ganshi ba take na amince yawan
tunanin sa da nake yine yasa nafara jiyo kamshin
sa Bat na nemi mijin nawa Na rasa hakan ya sa
na fara waiwaye- waiwaye saboda ni sam ba
taba shiga jirgi nayi ba balle nasan ka idojinsa
Tsawon mintuna ina laluben mutumin amma ban
gan shi ba hakan ya tunzira zuciyata na sami
waje kawai na zauna ina fargabar yadda jirgi zai
daga ni sama na zama tamkar tsuntsu a sama
wani mutum ne yazo ya tsaya akaina tare da
sanar dani wai wajen sane,nazauna har yana
nuna min numbersa ajikin boarding pass.

Take
kwalla ta fara zubar min ganin yadda mijin nawa
kiri-Kiri zai saka adauke ni 'Yar kauye Murmushi
kawai na saki da furta kalmar"am sorry". shima
yasaki murmushi ya ce "Ba komai 'Yan mata
kiduba lambar sit dinki ajikin boarding pass dinki
Na daga kai na nawuce ina laluben lambar
kujerata Da sauri na isa wajen sai dai na tsaya
turus domin daf dawani mutum aka ajiyeni wata .

Lafiyayyiyar suit kuma daga jikinsa kamshin
turaren Ustaz yana fitowa ya rufe fuskarsa,da
wata magazine Mamaki ya kama ni nan na shiga
waiwaye ina tunanin INA MIJINA? haka na zauna
saboda ba na so adaukeni 'yar kauye Amma
kamshin da mutumin yake ya ta kura min saboda
kamshin.Turaren Ustaz Ahmad Tunda Nazauna
bai tan kamin ba Ni ma kuma ban kula shi ba Na
dai kaddara kawai barci yake ko kuma irin
miskilayen mutanen ne shi din jigum na zauna ina
ta addu'a a raina don kam a tsorace nae Dalili?
ban taba shiga jirgi ba wani sauti naji yana sanar
da mu muyi tightehing belt dinmu Gaba daya na
rikice don ban ma san inda belt din yake ba
Mutumin bai wani bude fuskarsa ba ya dana belt
dinsa alamar shidin kwararre ne Na rasa yadda
zan yi tamkar na tambaye shi amma, nafasa na
hakura kawai na cigaba da addu'a a raina Jinayi
kunnuwana sun yi dum dai-dai lokacin da jirgin
ya fincika zai daga ban san lokacin da na
kankame jikina ba ina salati jinayi wannan
mutumin kawai yayi caraf ya riko hannu na
Ahanzarce na juya zan masa .

Masifa duk da
tsoron da nakeji Cab ko kunsan WA NA GANI? .

Da sauri na ware idona don natabbatar shidin ne?
tabbas shine ustazuna . ya matse cikin wasu
marun din suit sun amshe shi sosai abinka da
farin mutum cikin matukar mamaki na zame
hannu na nace Ustaz me yakawo.Ka nan?

Ina
humaira?

Bai min magana ba sai zallar murmushi
kafin yace "Humaira tana gidan mijinta" Na sake
waro ido nace Wanene mijinta ban da kai da na
sani? .

" Ustaz ya lumshe ido kafin yace Ni ba
mijin Humaira ba ne ni mijin Ayshata ne" Wani
farin ciki ne ya,mamaye Zuciyata da sauri na ciji
kaina inaso na tabbatar ba mafarkin da na saba
ba ne Ustaz na,lura da ni ya jawo hannun ya
matse yace "Ba mafarki kike ba Aysha nine,Ustaz
dinki" Yakai min sumba a hannu sannan yace "Is
a long story bari muje gida kisha labari" .

Tuni
maganar jin tsoron jirgi ya sha ruwa saboda, ga
ni ga masoyina Ustaz dan gaske,Ban sake
magana ba illa sakin murmushi Shi ma
murmushin yake ya jawo ni gefen kafadar sa ya
kwantar akan kafadarsa Akunne ya rada min
"Aysha kiyi barci .

Na san kin dade baki yi barcin
farin ciki ba" Na saki murmushi don kam azahirin
gaskiya ya fada Wani annuri ne yake shiga
zuciyata na lumshe idona kamar mai barci sai dai
sam ba barcin nake ba zallar soyayyar Ustaz ce
take ratsa duk wani ilahirin jikina, .

Ina kuma
sake jaddada godiyata ga jalla ta'ala buwayi
gagara misali Da son na san yadda reshe ya juye
da mujiya al'amarin Allah kenan kana taka Allah
na tasa .Ta jalla itace gaskiya Azaton Ustaz barci
nake don haka bai tashe ni ba don ko da aka
kawo abinci ma karba kawai ya yi ya ajiye min
nikuma na yi lamo sam ba na son narabu da jikin
Ustaz Ina shakar kamshin sa mai sake
tsuma,soyayyar sa azuciyata sai asubar can garin
sannan muka isa Gaba daya Ahmad ya kankame
hannuna tamkar wani zai kwace ni awajensa
Wani rantsattsen hotel ya kama mana tamkar
aljannar duniya zuciya ta fari kal nake mayar da
kafata duk inda Ustaz, ya ajiye tasa Shikuwa sai
jifa na yake da wani salon murmushi Zama,yayi
abakin gadon hade da fadin "Wash,Allah " ya
lumshe,ido ni ma bin sa nayi .

Da ido lna masa
kallon zallar so Ustaz ya miko min hannu "Zo
Ayshat" Ba musu na isa,ga ustaz cikin ta kun,jan
hankali amma sam na ka sa,karasawa gareshi illa
narungume hannaye ina jifanshi da murmushi
shidin ma kashe ido yayi yace "mekenan aysha?

Ina fatan ba kunyata kike jiba? .

" Na dan makale
kafada alamar ba za niba Da sauri ya mike ya,iso
gareni "Why aysha?

Don Allah kada muyi haka da
ke kada ki disashe farin cikin danake shirin samu
atattare dake awannan daren Ayshata please
enough is enough komai ya wuce don
Allah"yafada yana langa be kai Ni kuwa sake
shagwabe fuska nayi nace Ustaz me ya sa kuka
wahalar dani kuka ki bayyana,gaskiya? murmushi
ya sake yi yace "Har na hango aysha a asibiti da
angonta tana muzurai" ya tuntsure da dariya
abinda ban taba ganin ustaz ya yi ba Don haka
nabishi da kallon mamaki kuma sosai dariyar ta
yi masa kyau ya sake bina da kallo "kina tuna
bama- baman hara rar da kika dunga aika min a
asibiti? . .

Na kwace fuskata zan fashe da kuka
Da sauri ya kamo hannu na "Come on Aysha,yau
ba .

Ranar kuka ba ce so nake kawai.na nu
namiki zallarso Aysha I am in need" ya fada yana
lumshe,ido Tare da janyo hannu na Nace "Ustaz
don Allah kabani labari" Da sauri cikin dushewar
murya yace "Ba zan iya komaiba yanzu sai na
samu,nutsuwa" Shiru nayi da ba kina don na lura
abin nasa ba sauki. . *** *** *** .

WAYEWAR GARI
A ABU DHABI .

Duk da sanyin asuba da yake
ratsowa ta window hakan bai sa na tashiba
Ustaz, tuni ya tashi ina ta jin motsinsa har.Bacci
ya sake dauke ni Diso-dison ruwa da yake
digomin akan fuskata, shiya sa na bude idona.
Chapter 10 · 0% Book details