← Book details Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 16

Sashe 15

Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shawarar
sakinta" Haka ya zauna ya dunga fahimtar da su
har suka fahimta Mami tace "Dama Abba ne yace
mu zo muyi mata fada, zata da hadin bakinta
amma yanzu mun fahimta, hakan shine adalci, a
wajen duk maza da zasu fahimci rashin adalci
babbar masifa da sun rabu da auren mata
matukar suka san ba za su iya adalci ba"Daga
haka suka mike Ustaz yace "Umma har zaku tafi
Tace "Dama abinda ya kawo mu kenan don
hankalin Abba ya tashi da ka sanar dashi ka rabu
Da matarka ya zata laifin Ayshatu ne" Ina kallo
suka shige motarsu suna daga min hannu sai a
lokacin wasu zafafan hawaye suka zubo min
tunanin duka al'amuran duniya yanzu ni zasu
zarga Ustaz na ji ta bayana ya hada ni da jikinsa
ya ziro hannu yana share min hawaye "Mene ne
na kuka My Angel? please stop it, I hate to see
you crying." Cikin wata salon murya yasanar dani
haka sannan yaja ni cikin gida yana sake
jaddada,min zazzafar kaunar da ya sabar dani
Ranar da nayi sati biyu da tarewa agidan
gwarzon mijina Ustaz Ahmad Sulaiman da wuri na
tashi, .

Na fara shiri don zaikaini ziyara.Zuciyata
cike da farin ciki don na dade ban fita ba, saboda
Ustaz ba ya son yawo don haka ya rokeni ma
nabar zancen karatu don shi sam ba ya sha'awar
koda yaushe mace tana zarya ahanya ya
mallakamin wasu manyan kamfaninsa guda biyu
da gidan mai guda daya duk ya sa aka mayar da
sunana akai.

Tsaf na fito cikin wata hadaddiyar
doguwar riga zubin misra, kalarta yelo ma adon
ja.

Na yi rolling da jan mayafi na yi kyau sosai,
abinka da mai shigar karamin ciki fatata ta yi
subul-subul tamkar bayan kifi don santsi Gidansu
muka fara zuwa, nan na ga soyayyar surika ashe
kawai surukai masu kirki.

Mahaifiyar sa ta
rungume ni sosai ajikinta da kanwarsa Khadija ita
ma nan da sati biyu za ta amarce.

Kayan motsa
baki kala-kala mama ta sa aka ajiye min.

Nakuwa ci sosai don kayan kwalama ne Sai
la'asar sannan muka bar gidan Daga nan kuwa
gidan Humaira muka wuce, don babu nisa sosai a
tsakaninsu.Humaira sarkin rawar kai sai tsalle
take da murnar ganina mahmud yana gaisheni ta
cafe da cewa .

"Darling ba kace ya bebinta ba"
Da sauri na zabga mata harara "Wallahi Humaira
sam ba ki da kunya" Ta tsuke baki "To kunyar wa
zanji a nan mahmud ko Ya Ahmad?" Nayi tsaki
hade da mikewa na kalli Ahmad ya hade rai tsaf
wai shi yazo gidan kaninsa.

Dariya ta so kubce
min don sam hade girar bai karbe shi ba Sai da
muka shiga mota na tuntsire da dariya nace
"Yaya babba manya, irin wannan tsare gida
haka?"Murmushi yayi yace "Usainan nan taki ce
akwai rawar kan tsiya" Duka gidan yayyena sai
da Ahmad ya kaini abinda ya ba ni mamaki bai
wuce yadda suke zaman lafiya da kishiyoyin su
ba tamkar 'YAN'UWAN JUNA.

Na ayyana
azuciyata Da ni ce bazan iya ba.

Daga nan sai
gidanmu karkaso kaga yadda na yi tsalle na
rukunkume Mami Umma ta dakamin Tsawa tace
"ke cikata ku har abada daga ke har uwar taki ba
za kuyi hankali ba, bayan ga yadda kuke ita ma
ba lafiyace da ita ba." Na waro ido ina kallon
umma cikin mamaki na ce "Mamin?

Dubifa yadda
tayi kiba Umma, amma kice ba ta da lafiya?"
Umma ta gallan harara To uwar maganaUWA novels / NAGA RAYUWA book 3 part 18
NAGA RAYUWA book 3 part 18
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:32
.

Kibar tata ce miki aka yi ta lafiyace?

Duk da
ban so gaya mikiba..." Cikin magiya Mami tafa
rokon Umma wai kada a gayamin na kuwa zaro
ido nace "Na shiga uku me kuke boye min wane
irin ciwo ne da,Mamina?" Ni sarkin hawaye tuni
na sake su kamar famfo Umma ta saki salati tace
"Yanzu Ayshatu kuka kike ke kam zanga lokacin
da girma zaizo miki" Cikin shesshekar kuka nace
"Don Allah Umma me ya same ta?" "Cikine da ita
sai ki taya ta da addu'a."Aikuwa ban san lokacin
da na saki dariya ba kuka yakoma dariya cikin
tsananin farin ciki na sake rungume MAMINA in
cewa "Alhadulillahi Allah na gode maka,da ka
amsa min tawa addu'ar Allah ya raba su
lafiya."Umma ma cikin fara'a take cewa "To me
ye na kukan aikin gama tun da kika godewa
Allah" Nace wallahi Umma kukan tsananin farin
ciki ne ni na sani Umma yau wallahi ba zan iya
barci ba." Umma Tace "Na sani aysha Na sake
cewa "Da fa na yanke shawarar da zarar na haihu
zan dankawa mami abinda na haifa ta raine shi
kamar yadda ta yi min Allah na gode maka Umma
tace Shine abin .

Godiya Sai da na bugawa Ustaz
waya atake agurin.

Cikin dariya nake shaida
masa shi din ma hamdala ya yi.

Da Abba yadawo
ma da fara'a nayi masa Murna shima dariya
kawai yake yana fadin "aysha kenan" Sai dare
UstaZ ya zo muka koma gida zuciyata fal da farin
ciki.

BAYAN WATANNI SHIDA Abubuwa da dama
sun faru sun wuce.

Ciki kuwa harda
matsananciyar kulawa, kauna da tausayi da Ustaz
yake yimin ganin ina dauke da cikin dansa ko
kwakkwaran motsi Ustaz ba ya so yaga na yi.

A
yanzu haka ma shirye-shiryen tafiyar mu Egypt
ake ni da mahaifiyarsa don yace ba zan haihu
anan kasar ba Har da Mami na yake shirya mana
tafiyar don ita awatan haihuwa ma take.

Kwance
kawai nake kaina yana wani azabar ciwo, cikina
yayi turtsitsi a gabana.

Kafafuwana sun yi luba-
luba, haka hanci na yayi muni sosai kai gaskiya
ciki ba karamin muzanta halittar mutum yakeyi ba
Ammafa wasu fes za ka gansu babu abinda ya
canja sai abinda ba za a rasa ba.

Jin motsi nayi
da kyar na juya sai naga Ustaz tsaye abayana
yana doka murmushi da alamun . tsananin farin
ciki a fuskarsa "Ayshatu My Angel, albishirinki?"
Cikin kaguwa da son sanin mene ne nace "GORO
fari katoto."madadin ya fada sai ya miko min
hannu,"kama ni kitashi ki ba ni goron" Na waro
ido sosai Ya kuwa tuntsire da dariya "Ayshatu kin
yi kyau sosai da cikin nan." Harara na watsa
masa don na san tsokana ta yake yi sannan ya
cigaba da wakar da yake min "'yar beauty mai
katon hanci 'yar beauty mai katon lebe." Gaba
daya na shagwabe fuska nace "Kaga ka ga Ustaz
ba na so" Shi ma kwaikwaya ta ya yi "Kin ga -
kinga aysha ina so" Na wurge shi da pillow ya
cafe yana murmushi hade da min wani fitinannen
kallo "I LOVE YOU MY WIFE.

Kin shagaltar dani
ban gaya miki albishir din ba MAMINKI TA
HAIHU" Da sauri na mike "Amma ka tsaya kana ja
min rai me ta haifa tashi ka kaini" Cikin mamaki
Ustaz yake kallona yace aysha ashe da kwarinki
kike langabewa, dubi yadda kika tashi ahanzarce
daga sanar da ke haihuwar Mami" Na kwabe
fuska nace Don Allah katashi ka kaini" Babu
musu ya mike ya zira min hijab dina .

Muka fice
daga gidan sai da muka shiga mota ya ce "Ba ki
ji me ta haifa ba" Na ce metahaifa?

'yan biyu
duka mata "SHUKURAN LILLAH" Nafada afili.

Ustaz ya saki murmushi yace su aysha anyi
kanne Da hawayena na shiga gidanmu ina
tunanin ashe za mu ga wannan lokacin aduniya
Tabbas Bahaushe bai yi karya ba da yace
Mahakurci mawadaci kuma BAYAN WUYA SAI
DADI.

Na zauna a gefen gadon ina kallon mamina
da fuskata cike taf da farin ciki sannan ahankali
itama hawayen ya zubo mata.

Umma ma
hawayen take Tace "kukan farin ciki kam ya zama
dole.

Allah kenan da ba ayi masa dole shiya ke
ba da haihuwa alokacin da yaga dama" Na dauki
'Yan biyun ina kallo kamar mu daya da su sak.

Wallahi tamkar yadda nake ina yarinya Da sauri
na dauki hotona babba da yake rataye a dakin
mami na kara a fuskarsu.

Cikin dariya mami tace
"Ba saikin kara ba, kamar ku daya" Abba yace
"Kwabo da Kwabo kuwa" Aka kwashe da dariya.

Kafin a ce Mene ne wannan? tuni gidan mu
yadinke da hayaniyar jama'a 'ya'ya da surukai da
jikoki. .

Kafewa na yi anan zan kwana, amma
Abba ya ce tilas na tafi gidana na dawo washe
gari.

Amota Ustaz yake sanar da ni wai bizarmu
tafito jibi za atafi Ni kuwa na zabga masa harara
cikin wasa nace "Ai kai ma ka san ko birnin
Lantsandan ne ba zan tafi ba ayi suna ba." "Kada
muyi haka da,ke aysha kin ga watan haihuwarki
ya kama, tun da dai ta haihun lafiya ba shikenan
ba" Allah Ustaz kada ma ka fara don babu inda
zani sai anyi suna Shiru yayi na lura ransa ne
yabaci duk da haka bazan sauka daga kan
ra'ayina ba.Har mukaje gida bai kula ni ba illa
yadebo min abinci ya ba ni a baki harda tausar
da ya saba min magana ce dai ta fatar baki ta
gagara. ***** ***** ***** Tsakar dare naji bayana
yayi wani irin amsawa ba shiri.Na mike jin
marata ta amsa.

Na daka wa Ustaz duka,shima a
razane ya farka, yana duba na yace "aysha
lafiya?Me ya faru?"Da kyar nace masa "Mutafi
asibiti yallabai, marata kamar za ta balle" Da
azama ya daukeni cak inata gumurzu Iya mai yi
mana aiki da ita muka tafi asibitin. .

Tsawon awa
guda a asibiti ina abu daya kafim Allah ya yanke
min na haifo santalelen yarona jajir da shi, gashi
har gaban goshi da kibarsa dumimi tamkar diyan
indiyawa.

K da idona ya haskomin yaron anfita da
shi wani farin ciki ne ya mamaye ni na tuna wai
wannan da na ne mallakina kai Allah na gode
maka "Alhamdulillah" na sake furtawa ahankali.

Ahmad na ga yaturo kofar yashigo bayan da
likitar tafita Cikin tsananin farin ciki ya dube ni
yana da fa goshina"sannu ayshata da wahala ko?

Ubangiji yasaka miki da mafificin alheri.
Chapter 15 · 0% Book details