← Book details Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 16

Sashe 6

Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah ya
kiyaye jinina yahadu da jinin shege kuma karya
take kaf zuri'armu ba karuwa ba dan'iska Don
haka ni ban amince da cewa hamidan yayi wa
kanwarta ciki ba sudai da suka gado iskancin sa
sunsan inda tayo ciki amma mu kam kaf
zuri'armu 'yan mutuncine Duk yadda Alhaji
yabulla sai matar nan ta bulla sam ta ki yarda
hamidan ne yayi wannan ta'asar Haka inaji ina
gani naja sangalalin kafata cikin mutuwar jiki
nakoma gida ina kuka Abu yabazu akauye nan da
nan aka shiga yimana gori ba shiri na hade
kayanmu muka yi kaura kano inda na kama mana
hayar daki awani gidan karuwai ta silar wannan
abubuwa dasuka,faru ni da kanwata muka
tsunduma kanmu acikin karuwanci kafin wani
mutum Alhaji muhammadu ya mayar damu
gidansa,mutum ne mai kudin gaske sai dai ba
ya,haihuwa . matarsa mutuniyar arziki yar garin
Bendel tayi mana rikon mutunci Daga,lokacin
nafara binciken yadda zanga Imamu . don daukar
fansa kwatsam ranar an Kai uwar dakinmu asibiti
na hango shi shi da matarsa bai ganeni ba kasan
cewar hijab nasaka da nikab nikuwa nan nashiga
bincike amma har na gano gurin family doctor
yake kai matarsa awo alokacin tsawon shekara
goma bansan ya shi a idona ba.Kawai zuciyata ta
rayamin DAUKAR FANSA wannan shine dalili"
Gaba daya kotun tadauki hayaniya Abbana
yadanyi murmushi don ya fuskanci daukacin
jama,a shi suke jin haushi .

"kina ganin yanzu
ramuwar da kikayi akaina batayi.Yawa ba?

'yafa
kika saka aka sace min sukutum sannan kika ba
da ita ga magajiyar karuwai ta koya mata
tarbiyya irin tata duk adalilin naki na aureki" Ya ja
ajiyar zuciya hakika kincuceni iya cuta fateema Ni
bazance miki komai ba sai dai Allah ya shiryeki
Akarshe daga yau shari'ar ta bar hannuna
takoma gun abokin aikina kasan cewa abin
yashigo da ni aciki kuma shine zai kawo karshen
wannan shari'ar" Daga haka Abbana yabuga
guduma jama'a suka furta kotu.

Nan da nan aka
fa ra watse,wa muma jikinmu asalube muka
mike,da niyyar.

RAYUWA book 3 part 7
NAGA RAYUWA book 3 part 7
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:09
Tafiya gida ummana kuwa tana hada ido da
shany take tasaki kuka Nasan radadin abinda
takeji Nikuwa,damuwata daya ce mamina yanzu
Abbana da wane idon zai kalli mamina
kai.Jama'ar gidanmu ma gaba daya me za suce
da ita? .

Duk da tarin zargin da akayi
marattabbas ancuceta ankuma zalunce ta shi
kansa na lura Abba na jikinsa amatukar sanyaye
yake don ko da yadawo gida sashen sa ya,shige
yakulle kofa Nikuwa idan na kalli yar'uwata
Shany sai naji tausayinta ya sake kwarara
azuciyata Don itama kuka take sosai tare da
sauran yan'Uwanta su shida. .

Ummana tana can
kuryar daki nayi sallama nashiga da kyar ta dago
idonta da yayi jajur takalleni na,zauna a gefenta
na ce Umma wai me yasa kuka damu kanku?

Ba
za ku yi hakuri ku gode wa Allah ba da ya
kaddara muku saduwa, da diyarku tun kuna raye?

Umma ta dago tana duba na Aysha Allah shi ne
abin godiya ba komai yake damu na ba sai yadda
wannan matar ta gurbata min tarbiyyar yarinya
yanzu ta ina kike tunanin zan fara gyaran
tarbiyyarta?

Abu na gaba da yake damuna shine
maminki . yanzu da wane ido Abbanki da
yayyenki zasu dubeta? wannan shine matsalata
Ajiyar zuciya naja nace Umma duk wannan mai
sauki ne tarbiyyar shany dai ki kaddara Allah
shine mai shiryarwa ki ci gaba da rokonsa ya da
fa miki awajen tarbiyyarta da ta sauran
yan'uwanta Mamina kuwa insha Allahu
matsalarta mai sauki ce Umma girgiza kai tayi
tace Bamai sauki bane fateema na da riko kuma
tadau zafi sosai a maganar nan ba ita kadaiba
ma gaba daya danginta kuma tabbas yakamata
su aikata hakan ko fiye da hakan don kam tabbas
an bata musu . shiru nayi don kam ni ma
shaidace da yadda yan gidan mamina suka dau
Zafi kuma tabbas yacancanta ayi hakan don an
bata musu Umma ta ja ajiyar zuciya kafin tace
Tashi kije kija yan'uwanki ajiki Aysha don Allah
musamman yar'uwarki duk da Abbanki yace zaisa
ayi tayi musu addu'a amma tarbiyyarsu kam sai
antashi tsaye.

Jikina asanyaye namike nafice
daga dakin don na lura Umma babu abinda yake
ta yar mata,da hankali sai yadda za ta daidaita
nutsuwar Shany ta dawo abar kwatance. .

Tabbas wannan matar tacuci iyayena kuma
wannan shi ake cewa ramuwar gayya wacce tafi
ta gayya zafi Nayi Alkawarin zantaimaka mata da
gyaran tarbiyyarsu Afalo natararsu gaba daya
suna zaune sunyi jugum-jugum sosai tausayinsu
ya,tsirga min na zauna kusa da Shany tare da
janyota jikina."Please! ya kamata ku cire damuwa
daga ranku haka tunda dai duniya ta shaida ba
ku da laifin komai tarbiyya akayi muku ahaka
kuma ita ta cuci kanta duk da itama tashi tayi ta
tsinci rayuwarta a haka amma bai kyautu ace ta
dora da nata mugayen halayen ba" Shany ta ja
ajiyar zuciya kafin kwalla ta,zuba sharr daga
idanunta tace Sister ina jin matukar bakin ciki
idan na tuna,rayuwata ta baya haka kawai banji
ba bangani ba don wata manufa aka rabani da
nagartattun.

Halaye na aka,kaini wata banzar
rayuwa banjiba banganiba wallahi Allah ya isa
bazan taba yafewa wadannan mutane ba Ta sake
fashewa,dakuka Ni kaina kukan ne yaci karfina
can daya daga cikin kawayenta tace Kukan dadi
kikeyi shany,saboda ke yanzu yar gata ce
kinsamu iyayenki. .

Mu a ina kike tunanin zamu
ga namu iyayen? shegu ne mu bamu sani ba
itama tafashe dakuka gaba daya gurin,sai muka
saka kuka, Daidai lokacin Umma tafito tana
sallallami yanzu mezan gani haka kuda zaku
godewa Allah da rayuwarku ba ta kare ahakaba
amma shine kuke kuka?, Dasauri ta fice nalura
itama Umma kukan takeyi da kyar na mike bayan
naji ana kwala kiran sallar la'asar nace musu
muje muyi sallah jikinsu asalube suka mike tare
da haramar alwala Abinda ya ba ni mamaki bai
wuce ganin yadda suke sallah ba gaba daya
dungurawa kawai sukeyi tausayinsu ya sake
kamani Don kam na tabbatar ba karamin gyara
suke nema a addininsu ba . nadauki damarar
koyar dasu sallah kafin komai da daddare gaba
daya muna zaune awajen da ake cin abinci bayan
angama Abba yadube mu yace masha Allah" kafin
ya karasa naji mayataccen kamshin Ahmad
yacika harabar gidanmu take nahade raina sosai
don ba na son abinda zai hada ni da Ahmad cikin
takunsa na isa yakaraso wajen yan matan Abba
kuwa, tuni suka zuba masa ido tsiyar namiji
maikyau kenan. .

Duk inda yashiga sai kallo Na
kaddara hakan araina har rige-rigen yimasa
sannu da zuwa sukeyi Shany da sauri tamike ta
shimfida masa darduma "Nagode" yace mata
cikin tausasshiyar murya sannan ya zauna ya
sake rankwafawa ya gaida su Abba yasa ke
jaddada musu murnarsa na bayyanar yarsu shany
Ni kuwa tuni nazare jikina nashige dakin umma
wai kuma sai naji ina kishin kallon da yan'Matan
Abba sukewa Ustaz Na zauna turus akan kujera
hade da dafe kunci inatunanin Ustaz da irin
tsananin kyan da yayi .

Yau shigar wata jallabiya
yayi dark-blue sai shaking take.

Ta kwanta lub
ajikin lallausar fatarsa wanda yala-yalan gashin
yakwanta ajikinta Asalin balarabe dole duk macen
da ta ganshi ta kyasa Atake na dokanta naji
Ustaz ya kirawo ni koda masifar da na saba na
zazzaga masa.

Sai dai shiru makatau take naji
wani abu ya tsaya azuciyata na tabbatar yanzu
Ustaz ya gama yayina Don haka kone mana ba
ya yi Shany ce tashigo dakin tana murmushi tace
"Sis,wannan ma dan' uwan mune?" Da sauri na
dago nawur ga mata wani kallo ina son .

Gane
me take nufi da tace hakan Ban hango komai
akwayar idontaba don haka hankalina yadan
kwanta Ahankali nace mata "MIJINA NE" amma a
da fa Takuwa bude ido tace Wow!

Amma meyasa
kikace a da kina nufin yanzu kun rabu?

Cikin
sanyin murya na fara sanar da ita labarin
Ustazuna kafin nagama kuwa tuni hawaye ya fara
zarya, akan kumatunta Da safe kuwa kasancewar
lahadi ce yawanci surukan gidanmu anan suke
wuni sai dare suke tafiya harda mazajensu da
'ya'yansu muna zaune na saka .khadija da
A.Nafisa matar ya usman atsakiya sai hira muke
cikin nishadi don ni sauran matan yayyena ba sa
gaba na don dana shiga halin da za a tausaya
min ba wacce ta kula dani tamkar khadija Abba
ne yashigo yana kiranmu nida 'yan matansa
Afalonsa muka zauna anan kuma muka tarar da
wasu matasa daga ganin su ka ga malamai don
yanayinsu ya nuna haka Abba ya nuna 'yan
matansa yace "Alhamdulillahi, gasu nan su
takwas ne nakeso kafahimtar dasu addini don
basu san komaiba game dashi malami daya
yagyara zama yace "Alhmdllh" sunana m.Kawu
kuma .

Zan dunga koya musu Alkur'ani zamu
soma daga fatiha insha,Allahu" Dayan ma
yagyara zama yace sunana M.Aminu zan koyar
daku fik'hu da hadith insha,Allah" haka dayanma
yagaba tar da kansa "sunana M.Amadu da yar
dar Allah zandauke ku darasin Sirah da tauhidi."
Abbana yasake gyara zama yace Alhmdllh nagode
Allah dama na sanar da su labarinku duka sun
kuma matukar tausaya muku da wannan dalili na
san insha,Allahu zasu jajirce wajen koyar daku. .

Ga aysha nan ma za ta sake tunasar daku
abubuwan da ba ku, gane ba kaina yana kasa na
dago inda muka hada ido da malm.Aminu yace
A'a Aysha tana gidane? . murmushi nayi da yake
na sansu malaman mune na tahfiz nasan
M.Aminu da tsokana Abbana yace Aysha ta ki
zaman aure yafada yana dariya Da,sauri na mike
nashige gida da gudu Don ba na son fadan
malamaina nasan su kamar yunwar cikina
musamman malam amadu Tun daga ranar Abba
yace adunga kiran shany da humaira tunda itama
sunanta Aysha bazai yiwuba mutashi a suna daya
sun kuma da ge sosai wajen karatu kuma duk
inda zasu hadda hijab . suke zuwa Sosai nake jin
kunyar haduwa da Mamina don haka haryanzu na
kasa Zuwa gidansu duk da ba ni nayi mata lefin
ba amma na ja janta tabargazar da Abbana yayi
mata Na jin jina mata laifin da ba nata ba
abinda,yafi komai ciwo arayuwa azarge ka da
abinda ba,ka aikata ba .
Chapter 6 · 0% Book details