← Book details Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 16

Sashe 7

Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar Lahadi sati biyu
da faruwar lamarin gaba daya muke zaune
aharabar gidanmu har da yayyena da matansu
kawai mukaji sallamar MAMINA kafin kace me
tuni yaya.farouk da yaya.Ali sukayi wani tsalle
suka gudu can bayan gida mamina ta shigo cikin
zumbulelen hijabi da nikab Da murna ta natashi
ina tsalle na rungumota ita din ma rungumo ni
tayi tana sakin murmushi Ummana ma da sauri
ta mike ta tarota cikin murmushi mai kama da
yake take fadin mamin Aysha kece da rana haka?

Ba tayi magana illa bi na da tayi da kallo tace .
aysha,wajenki nazo don tayaki murnar kubuta
daga kangin da kika shiga In kuma tayaki murnar
ganin yar'uwarki akarshe nayi miki sallama zan
tafi England karo karatu" Tuni hawaye suka
sulmiyo min daga idona nace novels / NAGA RAYUWA book 3 part 8
NAGA RAYUWA book 3 part 8
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:11
.

"Mamina kina nufin ba za ki dawo gidannan ba
kin.Rabu damu har abada?

Hannu ta saka tasha
remin hawayena kafin nata digon hawayen ya
dirgo akan kuncinta tace "Na rabu da kowa daya
dangance ki Aysha amma ke da usman bazan iya
rabuwa da ku ba Ina tare da ku a waya ko
lokacin da zanzo hutu ki kular min da kanki
Ayshata" .

Daga haka ta zame hannunta takuma
juya da azama da sassarfa Zata,wuce Umma
turus ta tsaya idonta na kwalla nikuwa da sauri
nabi mamina shima yaya usman ya fello da gudu
muka tsare mamin da magiya Daidai lokacin
Abba ya shawo kwana zaishigo sukayi ido biyu
da mamina Cikin sassarfa yajuya da azama yabar
gurin shi kansa nasan kunyar gamayyarsu da
mamina yake Mamina ta kalleni tayi murmushi
ahankali ta furta .

"SAI WATA RANA AYSHATU" .

Daga haka ta zame tafice Tuni na durkushe
awajen na saka kuka don sam gwiwata ta ka sa
daukana yaya usman yakama hannuna muka
shiga gida shi kansa na lura jikinsa yayi sanyi
sosai Abba naji yana kwalamin kira cikin sanyin
jiki na mike na isa falonsa Tarar dashi nayi
idonsa .

Yayi jajur da alama shima kukan yayi
yace Ayshatu mamin naki ta tafi? cikin sanyin
murya nace "Ta tafi Abba ta sanar dani cewa wai
karatu zata tafi England Amma Abba me yasa
bakaje biko ba?

Abba yaja ajiyar zuciya,yace
"Dalilai da dama Ayshatu ina matukar son
fateema amma ina jin kunyar.Tunka rar ta da
sunan biko Bayan tarin abubuwan da suka shude
da wane ido zandu bi mahaifinta? . mutanen
masu nagartar halaye ina jin kunya Aysha..."shiru
ni ma din nayi don kam akaf hasashena ban
hango mafitaba cikin dakiyar zuciya nace Abba
kadai jarraba tura manya nasan babanta mai
fahimta ne insha Allahu zai fuskance ka" Allah
yasa ayshatu tashi kije" jikina asanyaye na mike
na fice Amma ko dana shiga kasa katabus nayi
na roki yaya usman yakaini gidan mamina sai
dai,abin takaici anan take hajiyarta take sanar
dani sunwuce Abuja tacan ne jirginsu zai tashi
Hakan yasaka,na saka kuka don na tabbatar
yanzu kam mamina tayi min nisa musamman
idan ta auri wani mijin bai zama lallai ya bari
mu'amalar mu tayi nisa ba. . ******* ********
******* .

Wani lokaci ina kwance lamo akan
gadon Ummana matsanan cin tunanin Ustas ne
yadabaibaye min zuciyata kwana da kwanaki ban
samu labarin sa ba Hakan ya dan daga hankalina
hade da tunanin Ustaz yagaji da wulakan cin da
nake yarfa masa shiyasa ya ajiye ba tu na agefe
amma kuma ai har alokacin bai furta min kalmar
saki ba bai kuma aiko da takarda ba meya ke nufi
da jingine ni da ya yi? .

Ni kadai nake wannan
tuna nin Na rasa wazan tunkara da
wannan.Tambayar tawa gashi ni kuma jan'ajina
bazai bari na kirashi ba Fitowata daga wanka
kenan ina zaune da karamin towel ahannuna ina
tsane ruwan jikina Humaira tashigo da sauri
tamkar an cillo ta Na bi ta da kallo saboda,ta
inda muka bambanta kenan ita akwai dan banzan
rawar kai "Aysha Sis,kije Abba yana kira" Ina
zuwa shine zaki shigo kamar an cilloki har yanzu
kin gagara koyar sallama idan zaki shiga waje. .

Murmushi tayi ta fice da dan tsallenta, Nabi ta da
kallo ina mamakin yadda kullum ta Allah Humaira
acikin walwala da farin ciki take ba ruwanta da .

Miskilanci irin nawa Allah kenan mai halitta gashi
yayo mu iri daya amma sai ya bambanta mu
tabangaren halayya Na zira riga sannan nafita
falon Afalon natarar da duk samarin Abba ko nace
magidanta mamaki ya ka mani tare da tunanin
taron me ake ne gefe daya yan matan umma ne
sun za gayeta gaba daya cikin shigar mutunci
suke don yanzu sunyi matukar nutsuwa tamkar
ba wadannan tantiran na wancan lokacin ba Na
isa nazauna agefe ina fuskantar Abba da son
sanin dalilin kira na . .

Abba yabude da addu'a
kamar kowanne lokaci idan za.Ayi,taro sannan
yasake dubana yace "Aysha wannan taron naki
ne, so nake inji me kika yanke game da aurenki
ko kuwa har yanzu kina nan akan bakanki akaro
na uku bazan takura miki ba kamar yadda na
gaya miki wancan lokacin ra'ayinki zan bi" Ustaz
ya isheni yazo da kansa ya aiko,don haka yau
nasanar dasu zan fada musu abinda kika yanke"
Tamkar nace masa zankoma amma ina sai nayi
tuna nin yadda Ustaz ya yasar dani don haka,
dole ni ma inja ajina.

"Ina jinki"Abba ya fada Na
dago fuskata nace .

"Abba ba zan koma gidansa
ba karatu nakeso nayi..." Daidai lokacin Ustaz
yayi sallama da wannan mayataccen turaren nasa
Da sauri gaba na yahau bugu ganin azabar kyan
da ya yi Cikin jallabiya dark cofee 'yar Asalin sai
dai miskilanci na ya kawar da wannan kudurin Ina
so ayau na ga karshen miskilancin Ustaz na san
idan yaji ba nason sa hankalinsa ba karamin tashi
zai yi ba Cikin fara'a Abbana yace "yauwa dan
halak yanzu ake zancenka gwanda da Allah ya
kawoka Aysha sake maimaita abinda,kikace"
kaina akasa nace ."Abba ba na son sa karatu
nakeso nakoma akasar waje .

" Murmushi Abba
yayi yace to kaji kai Ahmad sai ka ba ta
takardarta ayanzu kuma ayau zansanar dakai na
maye maka gurbin Aysha da yar'uwarta
Humair..." Tuni hantar cikina ta kada tamkar na
janye batuna nazaro idona ganin Ustaz ya zaro
jotter da biro a aljihu ya shiga rubutu tsaf nade
na fahimtar me ake. .

Cewa gashi miskilancina
yahana namaganu karshe runtse idanuna nayi
daidai lokacin Ustaz yamika wa abba takardar
yana fadin .

"Abba nagode Allah yabar girma" .

"Ya juya yana kallon daukacin mutanen falon
yace ku yani murna,da wannan karamcin na
Abba" Abba yace Bakomai Ahmadu kaidin mutum
ne mai nagartar halaye sam ba zan so na,rasaka
cikin ZURI'ATA ba Tamkar wani maganadisu haka
idanuna suka game da idon Ustaz kawai sai naga
ya dagan hannu ya saki murmushi alamar .

SAI
WATA RANA .

Daga haka yayi wa Abba sallama
ya fice jikina asalube namike har juri nake ji
nashige gida zuciyata cunkushe da tunani
nakuma tabbatar da cewa wata makarkashiya
Ustaz yakullamin ya dai ga yanzu humaira tafi
kwanta,masa azuciya kenan da sake-sake sam
ba na ganin laifina nikuwa,ko son sa,zai kasheni
bazan taba nunawa na damuba sai dai hakan
yazama AJALINA .

Ji kake kut nahadiye wani abu
da ya tsayamin amakogwaro sai asannan hawaye
ya zuba akan kuncina zuciyata cunkushe da tarin
bakin ciki nadama da da na sani kuwa fal raina
Nafara jin haushin humaira tamkar itace tace ta
na sonsa Ban da ni jinin tace wallahi da sai nayi
mata abinda za ayi na damar hada ta da mijina
sai kuma nafara jin haushin kowa .

Agidan da
tunanin sun fi son humaira akaina Ni kam nasan
narasa MAI SO NA MAMINA .

Don haka wunin
ranar ban yi magana da kowa ba koda nayi sallar
asuba sake komawa barci nayi duk da ada ba na
komawa barci da yanmatan umma muke haduwa
mu gyara gida yau kam ko kallonsu banyiba balle
susa ka ran zanyimusu karin karatu kamar yadda
na saba duk Asabar din duniya Da humaira da
maryam da khadija muke kwana daki daya wani
lokacin kuma humaira ta tafi dakin Umma
sukuma sauran biyar din suna dakinsu da yake a
bangaren mami muke tare jin hargowar shirinsune
yasa nabude idona cike da jin haushin su nace
malamai kunda.Meni fa kunhana ni bacci .

Humaira tadiro,gadon ta haye bargon da nake
kwance nace ke meye haka?

Langabe kai tayi
tace "Am sorry Sis, kinmanta da batun komawa
kotun kiyi sauri kishirya kibisu bros ni Ustaz zanbi
wani kallo nazu ba mata ina shirin kunduma mata
ashar sai kuma natuna ita din wacece da kuma
matsayinta a wajena Tsaki naja nace kuje kawai
ba na jin dadi bazan samu zuwa ba daga haka
YUWA book 3 part 9
NAGA RAYUWA book 3 part 9
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 14:12
. ba na son wani Silly queastion ina kallo suka
fice sai ga Umma ta shigo maganar duniya nayi
shiru kamar mai barci don ba na son ta gane
yanayin da nake ciki Inaji tace .

"Humaira muje
takoma bacci ma" suka juya suka fice Nabi
bayansu da kallo ina sake jaddada jin haushin
humaira acikin zuciyata sai azahar suka dawo
inajiyo hayaniyar su umma nayi bulun-bukui
adaki inajin umma ta sake dawowa dakinta
dubeni wannan karon na bude idona har nayi
mata sannu da zuwa, cikin wata cunkushasshiyar
murya Umma da mamaki ta dubeni Aysha kalau
kike har yanzu kike kwance?,kaina ne yake ciwo
kunda wo umma?

Ta gyada kai mundawo Nace
ya shari'ar ta kaya angama kuwa?

Umma tace
shari'a angama tsaf an yanke wa fateema
hukuncin zaman gidan wakafi na shekara biyar ko
tarar miliyan biyar .Shikuwa doctor daurin shekara
biyar babu tara Atine kuwa daurin rai da rai tare
da tilasta mata wajen fadar inda,sauran
'yan'uwanta suke.

Najijjiga kai hade da fadin
hakan shine daidai da su ai umma " Umma tace
kowa haka yake fada amma Aysha anya babu .

Abinda yake damunki kuwa?

Na ce babu komai
Umma amma don Allah kiyiwa Abba batun
komawata makaranta inda hali gaskiya,nafison
nabar kasar nan?
Chapter 7 · 0% Book details