← Book details Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 16

Sashe 2

Naga Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abar
ikonka cefa? kana da dama ka aikata fiye da
hakan akaina..." Abba yadaga kai yace Na sani
kedin yar albarkace ubangiji yayi miki albarka ya
mike tashi muje dakin ummanki kiyi wanka kicire
wadannan tsinannun kayan murmushi nayi
namike Har a lokacin suna nan afarfajiyar
gidanmu Ahmad sai zabga min murmishi yakeyi
niko kodigon fara'a babu atare . dani na tattare
fuskata nahade dakin umma nafada natarar da ita
a toilet fitowa tayi tana murmushi tace kinshigo
Ayshatu shigo kiyi wanka nahada miki ruwan
wankan cikin tausasawar murya takemin magana
nima tausayi tabani hakan ya sa nace to
ummana Nafada ina murmushi Tunda nashiga
toilet din nake faman dirzar fatar jikina tamkar
Allah ya aiko ni,nacuda yakai sau ashirin gashin
kaina kuwa haka nadunga dirzarshi har umma
tagaji tafara bugamin kofar sannan nabude nafito
umma tace wai! lallai kin dirzu dubi yadda fatarki
harja take murmushi nayi nace Badoleba umma
sai sati fa ake wanka wallahi nikaina har bashi-
bashin kaina nakeji Umma cikin tausayawa tace. .

Mungode Allah de dakomai yazama sai labari
zama nayi agaban dressing mirror din umma
nadau wani Nuetrogena body oil ina shafawa
kasan cewar lokacin sanyine banyi wani make-up
ba umma takawo wata riga sabuwa light Orange
colour mai kyau tabani nasa ni kaina nasan nayi
kyau gawata iska tana kada ni tanashiga kofofin
jikina da kuwa dauda ta cikasu dankwalin rigar .
nadaura akaina sannan na fito falonmu har
alokacin mutane ne dan kam agidanmu dukkansu
yan Zuwa murna Allah yakiyaye gaba ne dai dai
lokacin ya usman yashigo,yanayinsa yanuna
yanuna yana cikin matukar farin ciki yazauna
yana dubana da dan murmushin gefen kumatu
yace Aysha kije inji mijinki wani kallo na zuba
masa nace "Ya usman miji kuma?Aini banida miji
ahalin yanzu umma tadan dubeni tace banganeba
Aysha ya,usman yamike yanafadin "Rabu da ita
umarni nabaki kije yana sitroom yana jiranki
idanma zaku rabu bai kamata kurabu
tahakaba"ban mikeba sai da umma tace Aysha
usman nefa yabaki umarni idan da amana kuwa
usmanu baicancanci hakan daga wajenki ba
dasauri namike jin furucin umma nayi saurin
ficewa tamkar bazanyi sallama sai dai nadaure
nayi sallamar ya amsa idanunsa. .

Acikinnawa
fuska ta daure nace masa lafiya malam gani ance
kana kira na yadago yana murmushi hade dacewa
to zauna mana my beautiful wife ba zama nazo
yiba malam inada abubuwan yi acikin gida kuma
kada kasake kirana matarka matarka tana gida .

"Aikin daki ke haryafi kiran mijinki muhimmanci
Aysha? kuma da kikace kada nakiraki matata
yaushe nacireki amatsayin matata?nawaro idona
ina harararsa ko baka cireni ba kwanan nan
zakaji sammaci don wallahi saika sakeni mikewa
yayi ya iso gabana yasunkuya yana duban
fuskata madam dina babu murmushin nan mai
sanya ni nishadi?wai me yafaru ne? yaufa ranar
murnace tsaki nayi nace kadameni madam dinka
nacan gidanka wannan dai Ayshatu ce aysha
mazinaciya,karuwa,maibin yan fashi dafatan
kagane yanzu lumshe idonsa yayi yace please
ayshata forget the past nayi danasani banyi masa
magana ba saima juyawa danayi nashige gida
don kam alokacin ba na maraba da ahmad
sulaiman .

Daddare kamar kowanne lokaci muna
zaune ayadda ake zaman cin abinci Abbane
yadubi umma "ina tsammanin wani al'amari game
da yarinyar nan maikama da aysha ina hasashen
ko daga tsatsonmu tafito don tsananin kamar ta
yi yawa kinsan kuma masu kamanceceniya da ita
adangi suna dayawa kasancewar ance dama da
kakarmu suke kama toshi,ne nake hasashen ko
ita . ma jininmuce don haka nake dada tsaurara
bincike akanshari'ar umma ajiyar zuciya tayi
sosai kafin tace ashe bani kadai wannan abu
yadama ba tsananin kamar yayi yawa kamar yan
biyun da ake kira IDENTICAL TWINS sai dai kuma
ai babu wanda yataba rasa yarsa adanginmu
Abba yaja gwauron numfashi gaskiya babu
wanda yataba rasa yarsa akaf zuri'armu ta
potiskum wallahi sosai nakejin yarinyar nan acikin
zuciyata tamkar yata kuma natausaya mata da
ita da yan uwanta matukar.Tausayawa . koda
anbincika ba zuri'ata bace nizan dauketa da
sauran yan uwanta da ba asamu danginsuba
umma tace gaskiya hakan yakamata kayi tunani
mai kyau ubangiji yataya ka riko nikuwa nasan
zancensu baishigeniba haushi yaringa bani dalili?
sune silar fadawata duk wani bala'i don haka
sam banji wani ko digon tausa yinsu ba .

KASHEGARI Tun danatashi naji zuciyata
takwadaita da son ganin mamina baiwar Allah
don haka bayan dana karya naroki umma tabarni
naje umma tace .

"ayshatu yar gidan mami nina
isa nahanaki zuwa gun maminki? kije amma dai
karki . dade tunda mutane suna zuwa miki murna
har namike tace aysha ki tambayi ahmad kinsan
hakkinsane yasan da fitarki gabadaya nabata
fuska nace umma wanne irin na tambayeshi
kuma? nifa umma wallahi bazan koma gidansaba
don haryanzu abinda yayi min banmanta ba
kobama hakaba nibana son zama da kishiya inje
inawani raba miji da ita baki umma tasaki tana
kallona tace tabdi bashakka aysha kanki daya
kuwa? . bazaki.Raba miji dawata ba to kinci
gidanku idanzaki sauke wannan tunanin banzan
tun wurima gwanda kisauke don ba inda zaikaiki
sai tashar wahala menene laifin ahmad dazakice
bazaki koma gidansa ba? naja kwafa nace umma
bakiji irin maganganun daya dunga dankaramin
ba duk akan laifi daba nawa ba sannan yayi min
kishiya,batare dasani naba mahaifiyarsa babu
tsanar dabata nunamin ba sannan yanzu ace
nakoma auren sa? .

Allah yakiyaye umma tace
duk naji aimuma iyayenki duk munmuki laifi
meyasa mu kika yafe mana? murmushi nayi nace
kudaban shi daban bari nayi sauri natafi ina isa
gidansu mami kamar kowanne lokaci hajiyarsu .
da kallon banza tatareni ko gaisuwata ma da
kyar ta amsa tana wani cin magani bankulata ba
illa ma cewa danayi mamina ta na nan? . hajiya
tawurgeni da wani kallon banza tace aysha
fatima ba uwarki bace sau nawa zangaya miki
banason ganin sillan kafafunki agidannan?

Nidin
ma kallo nawurgamata don tsohuwar tafara
kureni,naturobaki nace dadinta ba wajenki nazo
ba kuma wallahi babu wanda ya isa yace mmina
ba uwata bace,Allah ne ya hada bazamu rabuba
ehe! na mike,ina mata,dariya nahaye saman da
mamina take ina hawa na juyo ina dubanta tarike
haba tana fadin ba shakka nayi nata gwalo
nashige dakin mamina.WA novels / NAGA RAYUWA book 3 part 3
NAGA RAYUWA book 3 part 3
Posted by Bashir Sani Fesan on 24 Dec 2016 - 13:58
Wannan karon tsaf na sameta azaune tana
karanta wata mujalla bataji shigowata ba
kasancewar kofar abude take sai da taji nayi
tsalle ajikinta afirgice tamike tace Ho ho ho!
aysha sam bakya girma kwabe fuska nayi kamar
zanyi kuka nace mamina mekuma nayi? tajawoni,
jikinta tana cewa babu abinda kikayi sweet
daughter me yafito dake madadin kizauna kihuta
daga fitowarki jiya shine kika debo kapa kika taho
yau?.

Hawayene yazubo min daga idona mamina
tace subhanallah meya faru ayshatu?

Nace mami
na wallahi gidan babu dadi tun da babu ke Don
Allah mami yaushe zaki dawo gidanmu? .

Dif
naga mamina tayi da fuskarta tamkar dai ba ita
ba ce take annashuwa yanzu tace "aysha ni da
gidanku har abada babu sunan dana sakawa
gidanku illa BAKIN GIDA anyi min abinda ba ataba
yimin ba arayuwa kedin ma dandole nake kulaki
saboda kaunarki ajinina take daga Rabbil Izzati
idan ban da haka abinda akamin akanki yaci ace
tuni nayi watsi da al'amarinki tobazan iyaba
konayi kamar nafita harkarki sai naji nakasa jinki
nake tamkar kedin jini . nace wane irin cin
mutunci ne abbanki da zuri'arku basuyimin ba?
hattasu muhammad usmanu ne kawai bai zargeni
ba,kuma hargidan nan yazo yana bani hakuri don
haka babu abinda zance masa,sai kuwa
ummanku macece jaruma da ta dau duniya ba
komaiba don tabbas hakika yar uwa ta daukeni
har nan gidan tazo tana bani hakuri" shiru nayi
sosai nagaza,cewa mami komai don kam nida
kaina na sani anci zarafin,mami akan laifin da ba
nata ba Nadade sosai,don sai karfe uku natafi na
sake baiwa mami hakuri . murmushi kawai tayi ta
ce aysha ni da gidanku har abada" Banga,laifin ta
ba don kam anyi mata laifin dayaka mata tadau
kowane irin hukunci kamar.Yadda nima nasha
alwashin bazankoma gidan Ustaz ba don nima
yashaka min maganganu masu kama da kamshin
mutuwa ina isa gida natarar da galleliyar motar
Ustaz akofar gidanmu tsaki naja azuciyata nace
sarkin naci Baya cikin motar Aharabar gidan
nagansu azaune shi da ya farouk gaba daya basu
isheni kallo ba donsu kansu yayyen nawa bawani
kallon arziki nake,musu ba Adage nake kallonsu .

Dalili?lokacin da abin yafaru babu wani wanda
yabawa iyayena hakuri acikinsu sai ya usman
don haka gaisuwa ma dakyar nake gaishesu akan
tilas Har nawuce ya farouk yataso dasauri ya
biyo bayana Ahankali yakemin magana Aysha
kina kallon mijinki kika shareshi tundazu fa
wajenki yazo yana jiranki wani kallo na watsa
masa hakan yasa baici gaba da magana ba Nace
yaje yanemi matarsa amma bani ba don ni
nawuce tunaninsa daga, haka da azama najuya
zanshiga gida ji nayi an riko hannuna ko ba
afadaba nasan Ahmad ne don kuwa ga
mayataccen kamshin turarensa nan ya cika
hancina da azama nafuzge hannuna fuskata
ahade nawurga masa wani wulakantaccen kallo
nace for the last time malam kada kasake
yunkurin hakan..." mekike nufi? kina matsayin
matata kiyimin warnin akan jikinki? kada ki manta
fa mallakina ne yafada yana sake,wurgamin kallo
tsaki nayi nace kaidin wai wane irin sarkin
nacine.?

Sau nawa zangaya maka kabar kiran
aysha amtsayin matarka How I wish anaganin
zuciya nabude maka kaga matsananciyar tsanar
da nayi maka" .

Baki asake yadubeni da alama
yana mamakin kalamaina ne murmushi yasaka. .

Yace aysha kenan Ni kuma da ina da hali
danabude miki tawa sirrin zuciyar kin ga
soyayyarki zalla da tacika ta muryarsa atausashe
yasake cewa Allah ne yajarrabeni dasonki da ina
da iko da na rabu dake tunda hakan shi ne
burinki Ahankali yaja dabaya yafice ko kadan bai
bani tausayiba don ni din ma baitausa yamin ba
alokacin da nake neman ya a gajeni alokacin
yabude min faifan rashin kirki da wulakanci Naja
tsaki na shige gida ina guna guni .
Chapter 2 · 0% Book details