Sashe 60
Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel · about 3 min read
Yana isa cikin gida ya fita zuwa sasansu yana shiga dakinta beby yana fadowa,da sauri ya riketa beauty me yasa kika min haka?Nan ya kira Umma ta waya sannan ya dauko zaninta ya nade bebyn ciki.duk yanda zan baku labarin suna ya wuce nan,domin anyi sunan ne acikin sabon gidansu wanda suka tare ana jibi suna,washegarin sunan ne,Yrm ya shigo ya wuce Faisal babban dan anty Fatima suna hira da Asma‘u auta,ya samu Bily tana bawa Al‘amin nono wato Yarima karami kenan,Bily ce ta zaba masa sunan,ya kalleta tana murmushi tace sannu da zuwa,ya zauna kusa da ita yasa hannu ya rungumota ya kai hannun ya matsa nonon,ta dubesa zakasa ya kware fa?Yace wai me ke tsakanin auta da Faisal ne?Bily tayi dariya tare da cewa, oho.adai cikin ‘yan kwanakin nan kullum suna tare,ina zaton har free call sukayi shekaranjiya dana cemata meke tsakaninku sai tace min wai yana koya mata karatu ne,nace shine karatun har cikin dare?Sai kuma tayi shiru.Yrm yace,Faisal yana da hankali kuma ya gama karatunsa yana aiki wannan ba matsala bane,da zaran sun sasanta sai ayi magana. Bily tace,Allah yasa mu dace.yayi dan murmushi,‘yan suna sun watse azo a san yanda za‘ayi dani fa,tace Allah basu tafi ba su Sakina suna can baya suna soya nama.Mansu ma tana nan,yace don Allah kaima Mansu beby kizo ki duba wani bebyn,tace kasan kuwa kai ne asalin bebyn nawa kayi kokari kwana takwas bari nazo inma irin hikimomina kaji nawa?Bily tasan kalar mijinta wurin bukata,dole ne ta kula dashi ta samu da rokon Allah da rigima ya daina neman mata bata fatan ya koma ruwa.kai radadin da tasha na neman matan da mijinta yayi bata fata ko makiyiyarta mijinta ya nemi mata,shiyasa bata barin sa cikin sha‘awa ko wane lokaci yazo mata takan jure ko tana so ko bata so,in lokacin tana al‘ada ne zatayi amfani da hikimominta har sai ya gamsu ba tare da sun keta haddin musulunci ba,ciki ko laulayi basa hanata sauke nauyin daya rataya a wuyanta. Yarima kansa yana tausaya mata domin ya sani tana kokari, don haka sai ya koma tamkar bawanta, duk abinda take so cikin sauri zai mata,gashi yana dawainiya da duk wani mai hulda da ita bama danginta ba,amintakarsu da Mansura kuwa babu wanda ya kaisu murna da farin ciki,haka lokacin da suka ji cewa Faisal na son auta murna suka yi domin sun san duk halinsu daya da Bilkisu.haka rayuwa ta ci gaba da tafiya cikin sha‘awa,‘ya‘ya maza Bilkisu tayi ta tarawa abinda mai martaba yaso yanzun gashi Allah ya bashi ‘ya‘ya biyar maza,t tuni suka amshe uku.Son da Al‘amin,da kuma Abba (wato mai sunan malam mamman)suka barsu da Saddik da Usman,ga kuma ciki mace? Namiji? Sai dai an haifa.
Tammat Bihamdullah!
Tammat Bihamdullah!