Sashe 37
Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel · about 4 min read
Ladiyo ta dubi gefen da Mama take zaune,sannan ta kalli su Karima ta soma magana dubi matar can,sunan ‘yarta na gidan sarauta amma kullum fate da rana.Salame tace ke da kike wannan zancan an san da zamansu ne?Har shi malam din da yayi hanyar auren,itama yarinyar tunda akayi auren shiru ko irin tazo din nan.Ladiyo tace ta samu dadi yaushe zata tuna da uwarta? Ai dai ba‘ayi dacen haihuwa ba wallahi. Duk Mama tana jin su,yi tayi tamkar bataji ba,aranta tace,oh yaushe rabon ta da faten ma,yau ma malam ne yace ta masa amma da sheri harda cewa kullum fate.
Tana mamakinsu gasu da abin zagi rututu amma sun danne suna zagin wani su da girkin ranar ma sai su debe shekara basuyi ba,ita bata da matsalar abinci,dan ko yaushe ne ma ko sati ba‘ayi ba da Mansu tazo ta kawo mata buhun shinkafa,katon din taliya,harda galan man gyada gashi su Sakina da Maryam suna mata aike daidai gwargwado,kuma zancan maigado su daba sa kasar kwana biyu ma basuyi waya ba,ko lafiya?Malam ya katse mata tunani da cewa,hakimi ne ya aiko inzo Fatima,bari inje in dawo.Tace lafiya dai ko?Yace nima ban sani ba,sai dai na dawo. Tace to,ya fita ba tare da musu magana ba,suka soma kwasa dariya suna cewa kila ma ‘yar ce aka sako ta.Ladiyo tace,Allah yasa hakane,da sai na zuba ruwa akasa nasha don dadi.Karima tace,haba dani nan bari dai mu jira dawowarsa. Suka shiga ‘yan wake-wake su adole burinsu ya cika.Shiko malam yana isa gurin hakimi ya samu ‘yan aike daga Bauchi, mota ce guda shake da kayan abinci zuwa na masarufi,inji mai martaba sirikinsa,‘yarsa aka kawo ma mahaifin sirikarsa lokacin da ya iso gida murna dai ta kasa boyuwa,tun daga bakin kofa yake fadin ina Fatima,ga sako daga ‘yarki.Nan aka soma shigo da kaya ana kimewa, Mama tace ikon Allah haihuwar ‘ya mace mai dadi,yau ga uwar mata tana murna ni Fatima na gode Allah.Ai su Ladiyo sai aka shiga sirarewa ana shiga daki,zuciya fal bakin ciki,hassada ga mai rabo taki ce,haka abin yake. Mama ko cewa malam tayi,wannan kaya shi aka ba,don haka sai ya raba yaba kowace hakkinta, yace a‘a san musu za‘ayi,tace ai ba zai yiwu ba,a karshe dole ya amince ya raba musu,sai dai duk da haka sai daya kara mata,sannan ya ware mata wanda zata ba mutane,tayi rabo kam duk sauran sassan ta basu,haka kawayenta Umman Mansu ma takai mata da yawa su Ladiyo ko kunya aka amshe shinkafa har ki ga ana salo gurin dafawa ana ci ana zagin Mama da ‘yarta, mutum kenan ba‘a iya masa.Umma tana ta zaton cewa Bily tana da ciki ne,don haka duk sanda sukayi waya da Bilyn sai ta rika ce mata don Allah kada ki biye ma babana da cin zakin nan da shan sanyin nan nasa kinji ko?Bily bata gane ba sai tace,to Umma shima Yarima sai ta riga cewa babana amma gida zata dawo nan gaba ko?Shima bai gane nufinta ba,sai yace dama fa kune kuka matsa sai nazo da ita,duk Umma ta damu har takai ga sanar da mai martaba damuwarta,tace ranka ya dade ina zaton matar Modibbo cikine da ita kuma daga shi har ita babu mai hankali cikinsu kada yaje yayi ta tura mata sanyi azo a haifi dan da sanyi ayi ta fama,mai martaba yace to yanda za‘ayi tunda ga azumi yana zuwa,in salla ta kusa sai mu tafi Ummara tare dasu daga can sai mu wuto da ita.Nan Umma taji dadin haka.Abinda yayi mugun bata ran Bily, harma da azumin nan Yarima bai daina kwana da mace ba,al‘amarin yayi mugun daga mata hankali, tasan cewa duk wani shaidani yakan aje shedancinsa a cikin wata mai alfarma,wata mai daraja,watan tuba,watan yafiya,watan da Allah yake ‘yanta bayinsa,watan lada.Don haka tayi niyar zata yiwa Yarima nasiha koda zai dake tane, shiyasa ma yau tayi nufin zama a falo don yin buda baki.Ya fito dakinsa yana sanye da jallabiya fara tas,yaxo ya nufi dinning bayan ta gama mikewa taji zuciyarta tana karfafa mata gwiwa kan cewa taje ta masa magana,don haka ta isa gurin kallo daya yayi mata ya kauda kai tare da cigaba da buda bakinsa,ta zauna tana fuskantarsa.Nazo ne ina son yin magana da kai,ya dubeta sannan yace “umhum. Taci gaba da cewa nazo ne in maka tuni kan wani abu dana san ka sani kila ka manta ne,matsayinka na musulmi bai dace ace cikin watan Ramadan kana aikata alfasha ba,kana zina ka sani duk wani musul.....ke!Ya katse ta da tsawa tare da buga teburin cin abinci har kofin glass ya fado kasa ya fashe,abincin gabansa ya tarwatse,ki shiga taitayinki dani,ni sa‘anki ne? Nace ni abokin wasanki ne?Itama tayi karfin hali ta mike tsaye danna gaya maka gaskiya?Yace bana son ji, ki fita daga idanuna,inba haka ba zan nuna miki waye ne Al‘amin.
[2/19, 10:01 AM] +234 803 225 4928: 🏵MEKE FARUWA 65🏵