← Book details Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 60

Sashe 19

Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel · about 6 min read

La'asar, suka shiga ojo da har za su wuce amma magajin yace su shiga anguwar.
Kai tsaye kusa da wasu samari suka yi dayan ko sai rantsuwa yake yi. Ibrahim yayi musu sallama suka amsa. In ban da dayan da yake ta zuba bai ma san ana sallama ba. Ibrahim yace, bayin Allah muna tambaya ne ko Allah yasa kun sani? Biyu suka hada baki gurin cewa,to magaji ya matso don Allah cikin ku ko akwai Wanda yasan wata Bilkisu? Yaci gaba. Yarinyar tana da kyau na ban mamaki. Samarin suka ringa kallon magaji kamar sunga wani sauna. Dariya ma ya basu, inda dayan yace Malam, Bilkisu suna da yawa a unguwar nan, kuma akasarin su kyawawa ne.Magaji ya yi shiru, can yace ita fa kyanta dabanne, kuma ta gama makaranta. Gaba dayan su suka sa mishi dariya har ma ya ji haushi zai tafi, sai daya daga cikin masu musun kwallon nan mai surutun tsiyan yace, Aa ko dai yana nufin Bilkisun gidan marina? Nan take samarin suka ce ita ce ma, don duk unguwar nan ita ce best a kyau. Magajin Malam da jin haka sai ya dawo yana cewa, don Allah yaro zo mu muje ka gwada min gidansu.Yace,to Magaji ya saka hannu cikin aljihu ya debo kudi ‘yan naira ishirin ya mika musu ba tare da ya kirga ba,yace na gode fa,suma suna ta godiya.Ibrahim yace,bari na zauna baya shi ya shiga gaba saboda zai dinga yi maka kwatancen inda zaka bi.Magaji yaji dadin haka,don yana son ya yiwa yaron tambayoyi musamman ma da yaga yaron zaiyi surutu.Ya dubi yaron,sannan yaci gaba da tuki,yace abokina kusa kuke dasu kenan? Yaron yace,E,gida biyu ne tsakaninmu dasu.Amma gurinta zaka?Magaji yace,eh,yaron mai suna Sule,yace ai ina ganin fa bata nan tana Kaduna,aikin gidan TV takeyi,ko bauta ma kasa naji ‘yan gidanmu suna cewa, suna zuwa yace da Sule ya shiga ya tambaya ko tana nan.Bayan fitar yaron ne Ibrahim yace da Magaji abokina zaka iya samun labarinta gurin yaron nan,don naga yana da surutu.Magaji yace nima na lura.Sule ya dawo da sakon cewa tana KD.Magaji yace,amma ka tabbata nan ne gidansu?Sule yace,nan ne,ko ba wata doguwa ba?Fara mai kyau?Magaji yace,itace,nan ne gidansu nan yaro ya labarta ma magaji labarin bilkisu
Bayan sun gama magaji ya kawo kudi ya bashi suka maida shi inda suka dauko shi suka tafi yana mamakin inda take zaune dan shi in ta tashi ne diyar wani hamshaki ce dan shi a zaton sa in ba'a samu gidan su a GRA ba toh cikin dai shahararrun unguwannin masu kudi take
Magajin Malam da ya gama ba Yarima labarin Bilkisu kamar yadda yaji sai Yarima yace,ka bincika sosai ko?Magaji yace duk wanda ka saka ba zai zo maka da sama da wannan labarin ba,sannan ga number dinta nan zan turo maka,wane saurayi ke nemanta?Bata dashi.Yarima yayi wani murmushi aransa kuma fadi yake,yarinyar nan ta cuce sa data ce ta sansa har kuma ta mammaida masa da maganganu.Layinta ya soma kira,amma sai aka ce ba zai je ba,nan take ya soma kiran sabon layin da Magaji ya tura masa,wayar ta soma ringing lokacin Bily tana tsaka da yin nafila,bata kalli wayar ba sai data idar ta sallame sannan ta dauko wayar cike da mamaki tace,to wanene wannan?Domin tasan ba kowa bane yasan layin,kuma wane mahaukaci ne da kiranta cikin dare haka?Tana dauko wayar ana sake kira,bata gane number din ba don shima bada wancan layin ya kira ta ba,sannan duk da(+)din data gani batayi tunanin cewa Yarima bane,duk da tasan cewa bata da wanda zai kirata daga wata kasa.Cikin mamaki ta saka wayar akunnenta,kafin tayi magana ya soma cewa,ke!‘yar gidan masu rinin tsumma,‘yar kauyen kayau,‘yar talakawa tilis,‘yar gidan ginin kasa.Kin cuceni da kika ce kin sanni,sai na saka brush na wanke bakina sosai saboda furtawa da nayi na cewa zan aureki.Wanene kike ikrarin kina dashi wadda mahaifinki Malam Mamman ke rini,uwarki ke aikatau?.....kai jahili! Ta katsesa da zafin rai,tana huci tace,kai jakin ina ne?Da baka san talaka da mai kudi da mai sarauta duk Allah ne ya halicce su ba?Kuma babu wanda Allah yafi so face wanda yafi bauta masa,kana zaton wayonka ne yasa Allah ya sakoka cikin gidan sarauta?Je ka shiga Islamiya,kana da bukatar sanin ilmin Tauhidi.Na biyu kuma duk da talaucinmu ba muzo roko gidanku ba,sannan Ubangijina shine wanda ya tsaya min,dashi nake takama,sannan baka san hakkin dan Adam ba da zaka min waya cikin dare.....ya katseta ni kika kira jahili?Tace ,eh.Zaki ga aikin jahilci,zan baki mamaki donni na wuce da tunaninki ‘yar matsiyata kawai.Ya kashe wayarsa duk su biyun sun batawa juna rai,sun gaya ma juna maganganu masu zafi.

Yarima saboda shi namiji ne zufa ya shiga yi tare da yin jifa da wayarsa,yayinda ita kuma ta hau kan gado ta dora hannu akai ta saki kukan bakin ciki,bata iya fada ba,bata taba fada ba,don haka sai abin duk ya zamar mata sabo,don haka kwana tayi tana kuka,kafin gari ya waye fuskarta ta kumbura suntum,haka nan da ciwon kai ta farka,da kyar tayi sallah.Shirun da Mansu taji shiyasa ta fitowa,tasan babu lafiya don tasan Bily da yanzun tana kitchen.Ganinta cikin bargo yasa ta karasawa gaban gadon da sauri taga yanayin da bilyn take ciki hankali tashe tace Billy baki lfy ne ta daga kai kawai ta kamata zuwa jikinta tana mata sannu tace bari toh na kawo maki wani abu ki taba sai muje ko asibiti tace sam ita ba zata ci komai ba mansu Tai banza da ita ta tafi ta hado mata abincin amma sam billy sam taki ci sai kuka take tayi lallashin har ta rasa ya zata yi mata

Mansu ta kalli Faruk tace,baban dady na rasa yanda zanyi da Bily,dama so nake ka gama cin abinci in shaida maka yau ko fita batayi ba,bata ci komai ba sai kuka nayi tambayar duniyar nan taki ta gaya min damuwarta.Ya mike da sauri zo muje,tana zaune ta hada tagumi suka sameta,sannan duk da zafin da akeyi tasha rigar sanyi.Faruk ya jawo kujerar gaban madubi ya zauna agabanta,Mansu kuma ta zauna kusa da ita,ta dafa ta tare da cewa,Bily tunda ni kinki sanar dani damuwarki,ga yayanki nan sai ki gaya masa domin tun kafin in haihu nasan kina da matsala,boye min kawai kikeyi.Kada ki manta fa ni dake ko ‘yan biyun da suka fito ciki daya alokaci daya basu kaimu shakuwa ba,ga zatonki bansan kina da damuwa ba?Bily ta kalleta da idanunta da sukayi jajir suka kumbura,sannan ta kalli Faruk tayi wani dan guntun murmushi wanda yayi sanadiyar zubowar hawayen da take kokarin makalewa.Muryarta tana rawa tace kada ku damu,ba wani dogon abu bane ya faru.Ta saka hannu ta kama hancinta ta dan ja iska,sannan taci gaba kun san wani lokaci abu kalilan ne yake bata ma mutum rai,domin zagin da Yarima yayi min wallahi anyi min gomansa amma ban damu ba,sai nasa.Faruk suka kalli juna shida Mansu,sai suka ji zancan wani banbarakwai,Faruk ne ya soma magana,wane Yarima?Ta nuna sa Yarima naka,taci gaba saboda Yarima na canza layi,amma bansan inda ya kuma samun layina ba ya kirani jiya yayi min tatas,harda gorin talauci.Babu abinda yayi min ciwo irin yanda ya zagi uwata.Faruk har suna hada baki da Mansu gurin cewa zagi?Tace zagi dai,Faruk yace tun dama menene ya hada ku?Bata boye ba,nan ta warware masa komai game da mafarkinta da Yarima zuwa ganin data masa,ta masa magana har zuwa sa-in-sar da sukayi dare jiya.Abin yayi matukar bata ran Mansu,Faruk ko cewa yayi sai ya kirasa yaci masa mutunci,nan Bily ta jajirce kan cewa kada ya kirasa,ya kyalesa in halinsa ne zai hadu da daidai shi.Mansu ko kallon Faruk tayi sannan tace,wai shin shi Yarima wanene shi?.
[2/19, 9:57 AM] ‪+234 803 225 4928‬: 🏵MEKE FARUWA 32🏵
Chapter 19 · 0% Book details