← Book details Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 60

Sashe 20

Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel · about 6 min read

YARIMA MODIBBO cikakken sunansa shine Al‘amin Isma‘il Abdullah,shine da daya tilo namiji da iyayensa suka mallaka bayan sun haifi ‘yaya mata ishirin da biyu.Sarki Isma‘il ya gaji sarauta ne gurin Babansa Abdullah tun yana da rai ya sauka yaba dan nasa Isma‘il mulki.Modibbo shahararren Malami ne mai tarin ilmi,su aminan junane shida mai martaba sarki Abdullah,tare suka taso wannan dalili ne yasa daya baya aiwatar da komai sai da shawarar daya,don haka lokacin daya kawo masa shawarar sauka daga kan mulki,Modibbo ya amince tare kuma da bashi shawarar yayi wa dannasa aure hadi da nadin sarauta.Sarki Abdullah yace shima nufinsa kenan,kuma yana so ne ya hadasa da ‘yar wajenka Sa‘a.Modibbo yace,wannan dama tasa donna gani cikin lamarin aurensa danayi istihara.Shekara daya jal da auren hadi da nadin sarautar ta sintilo ‘yarta mai kyau inda taci sunan matar Modibbo mahaifiyarsu Sa‘a,wato Salma.A takaice sai datayi mata shida sannan ya auri ‘yar sarkin yankin Katsina,itama ‘yaya hudu duk mata.Lokacinne sarki Abdullah,Allah yayi masa rasuwa,Wazirinsa shima tsakaninsu sati daya,sai dan Wazirin mai suna Hafiz shima ya gaji mahaifinsa bayannan ya kara mata biyu jere banda sadaka ga kuma kwarkwarori bakin abinda Allah ya halatta masa,duk babu wadda tayi koda barin namiji.Al‘amarin daya daga masa hankali kenan,saboda yasan mace ba zatayi mulki ba yana son magaji,haka yake kullum cikin damuwa har girma ya fara shiga,domin da yawa ‘yayan nasa ya aurar dasu.Umma mai babban daki haka suke kiran Haj.Sa‘a,tana tausayawa mijinta kullum tana addu‘ar Allah yabawa mijinta da namiji koda ba agurinta ba,ko gurin sauran kishiyoyinta ne.Lokaci yayi nisa,haihuwa ma harta tsaitsaya musu,ba wai sun tsufa bane,Allah ne kurum ya tsaida musu ita.Kwatsam!Sai ga ciki jikin Umma mai babban daki,batayi saurin sanarda mai martaba ba saboda tasan tana sanar dashi yanzun nan zai daga hankalisa,sannan ya hana idanunsa bacci yana rokon Allah yasa da namiji ne.Cikin hakane wani dare takai ziyara gurin mahaifinta Modibbo take sanar masa cikin dake gareta.Modibbo yace,na ganki cikin mafarki kina shayarda wani yaro namiji,sai dai ba yana nufin lallai namiji zaki haifa ba,domin mafarkin Annabawane kurum yake zama gaskiya.Murna ta cika ta tace,a taya mu da addu‘a,sannan bana son mai martaba yasan da cikin nan.Modibbo ya dubeta yace,saboda me?Tace zaya damu ne,yace wannan ba dalili bane,ki sanar dashi.Sai dai kada ki sanar dashi game da mafarkina,domin karya saka rai.Umma tace,to Modibbo na gode,Allah ya kara lafiya da nisan kwana,sukayi sallama ta dawo gida.Cikin satinne matar waziri Hafiz ta haifi danta namiji,mai martaba yayi murna tamkar shine aka haifamawa.Inda waziri yayi kara yasa ma yaro sunan mahaifin mai martaba,wato Abdullah.Da yake anfi kiran mai martaba Abdullah da Malam,saboda yana da ilmi na addini,don haka sai ake kiransa Magajin Malam,wato jaririn da aka haifa.Wannan yasa mai martaba kara son yaron,Umma mai babban daki ta sanar da mai martaba cewa tana da ciki,murna sosai ya shiga yi tare kuma da rokon Allah.Gefe daya kuma zuciyarsa tana cikin damuwa inya tuna shi bashi da kwan da zai samar da namiji kamar yanda wasu Likitocin suka shaida masa lokacin daya shiga neman taimakonsu.Amma ya dai mikama Allah lamuransa,ya kan tuna kalaman Modibbo da yake cewa,lallai kada ya zama daga cikin bayi masu cire rai daga rahamar Ubangiji.Haka dai ciki yayi ta girma har zuwa lokacin da aka haife sa.Ranar wata Juma‘a an tafi masallaci,an haifesa ne awani asibitin kudi dake nan cikin garin Bauchi bayan Umma tasha wahala.Mai martaba yana Fada Jakadiya ta iso masa da albishir,zancen daya saka mai martaba farin cikin da Fadawa suka jima basu gani ba,nan take yace da Jakadiya ya bata kujerar Makka.Kafin mai jego ta dawo gida labari ya karade garin Bauchi da kewaye.Yanda asibitin ya cika shine dalilin sallamarsu zuwa gida.Tun ranar ake shagalin yanke-yanke har zuwa ranar suna,inda mai martaba ya saka sunan Modibbo yace tunda waziri yayi masa kara ya saka Magajin Malam Sai dai yana fatan inya sake samun wani namijin ya saka masa Abdullah,ko kuma in Modibbo ya girma yayi aure to yana fatan Allah ya barsa da rai yaga ya saka masa sunan Abdullah.Faruk ya dubi su Mansu yace,bazan iya sanar daku gatan da Yarima ya samu ba,duk abinda yakeso shi zaiyi shi zai ci,haka nan shi zai sa,banda yayi sa‘ar iyaye masu tarbiya da ilmi hadi da sanin yakamata,to ko daba karamar shagwaba zaiyi ba,ko ince daya lalace,tun yana karami yake zuwa Fada,mai martaba yasa ake kawosa.Wannan abin yasasa girman kai ganin yanda ake zubewa gabansu.Yarima wani yaro ne dan kwalisa mai tsananin tsafta tun yana karaminsa,ga manyance tare da son girma,yana da matukar wahala kaga y shiga harkar wani,haka nan baya son ashiga tasa,halayensa rabi na Turawa ne,ko ince na tsarin Musulunci ne,misali;yana da cika alkawari,in har yayi maka alkawarin abu tabbas ne babu go nd come,sannan ko kai waye karya ne ya zageka abayan idanunka shi dan karara ne ko kaji dadi ko kada kaji bashi da yawan hayaniya,shiyasa nayi mamakin sa- insarku.Ya dan dakata kafin yaci gaba,ya taso shi wani tauraro ne cikin kafatanin ‘yan gidansu,haka nan gurin Kakanmu Modibbo bai hadasa da kowa ba,to haka yake cikin dangi kowa yana sonsa.Yayi karatun Nursery da Primary a (C.N.I)wata makaranta ce mafi tsada a Bauchi.Secondary yayi tane akasar Spain,yanzu kuma yana Malesia yana karatun Likita ne fannin mata.Bansan yanda zan gaya muku halin Yarima ba,shi dai dabanne komai nasa dabanne,bansan yanda zanyi muku bayaninsa ba,yana da tsattsauran ra‘ayi,haka nan baya son duk wani abu da zaya zubarda mutuncin gidansu,yana da alheri.Kada kuce ina yabonsa hakane halinsa.Bily tace,niko baban dady banga haka ba,Faruk yace ni kaina nasha mamakin lamarinku,shi ba mai shiga cikin lamarin wani bane,baisan fa bacin rai ba.Bily tace,shidai ya sani.Mansu tace,kadai gaya masa ya kiyayeta,ai talaucin ba bawa yake dorama kansa ba,haka nan don kana da kudi ba yana nufin Allah yafi sonka bane ya baka,wani kudinma in mai su baiyi hankali ba sai su kaisa wuta.Yace zan kirasa.
[2/19, 9:57 AM] ‪+234 803 225 4928‬: 🏵MEKE FARUWA 33🏵

Bily tace,a‘a don son Manzon Allah(S.A.W)kada ka masa magana,bana son kace masa kala!Nifa ya wuce agurina,kada ma yaga kamar ma na damu dashi ne koda abinda ya faru,please forget about him,na bar maganar.Faruk yace shikenan.

Mai martaba ya kalli Umma mai babban daki,sannan yace,Sa‘adatu menene na damun kanki don kawai nace mun yanke shawara za‘a nemawa Yarima aure?Ranka ya dade,bawai na damu bane,ina duba karatunsa ne,sannan shekaru ashirin da hudu duka nawa yaron yake?Yayi dan murmushi.To ni banda Modibbo ya tsaidani da tuni ma anyi auren.Amma yanzun ma bazai dauki lokaci ba,Yarima yana bukatar aure.Shiru tayi domin tasan maigidan nata baya zartar da wani al‘amari sai da shawarar mahaifinta masani mai tarin ilimi,haka nan tasan suna da dalilinsu.Ta dubesa sannan tace,ina fata Yarima bawani shirmen yakama ba?Mai martaba yace,a‘a yana da kyau dai muga ‘yayansa in Allah ya nufa zamu ga hakan,tace hakane,a ina ya samu matar?Mai martaba yace,wannan yana ga Modibbo,yace shine zai zabawa takwaran nasa mata.Umma tace,to Allah yasa mu dace,mai martaba yace amin. Duk da takaicin da Yarima yakeji na yarinyar,amma yana jin gara ya yarda kwallon mangwaron ya huta da kuda,don ba zai iya auren yarinyar ba,taje taci sa‘a domin yaso ne ya aureta ya wahalsheta.Yanzu kuma baya jin auren nasu zai yiwu,tunda yaji ita wacece.Sannan ya jinjina ma karfin halinta kasancewarta mace kuma ‘yar talakawa har kuma ta iya ja dashi,tunda ya gano cewa ita din abin tausayi ce to ya barta.Haka Yarima yaci gaba da harkokinsa,ahankali har ya warware ya ma manta da batun wata Bily.
Chapter 20 · 0% Book details