← Book details Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 60

Sashe 33

Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel · about 5 min read

Jikinta yayi sanyi, zuciyarta ta
baci,duk da shakkarsa da takeji gami kuma da
yanda yake cika mata idanu,sai data ce kai ma
kasan baya ga aure mai hada namiji da mace
baka isa in zo ince maka gani ba,ka sani nima
bada son raina bane,don kawai na fita daga
hakkinka ne,kuma Allah ya sani na fita.Ta mike
tayi waje rai bace,da kallo ya bita tun daga sama
har kasa yake kallonta,har ta fita.Ya runtse
idanunsa yana kallon yanda jikinta yake
motsi,wata sha‘awarta ce ta mugun tsirga
masa,ta baya ya fada kan gadon hannu ya kai ya
jawo filo ya saka akirjinsa ya matse gam,bakinsa
yana kwadayin lebunanta yana son jin kalar miyanta,nan zuciyarsa ta shiga tuno masa ni‘imarta duk da ya kusance ta ne cikin garari ba tare da wasu wasanni ba,amma abin ya tsaya masa a rai .Ya kuma shakar kamshin data tafi ta bar masa a dakin,ya sani bawai yana sonta bane
amma sha‘awarta tun ranar daya soma ganinta
ta tsirga masa,ba kamar yau da yaga siffofinta
a fili,yace kai she is a beauty.Yayi tsaki tare da
cewa,ni gaskiya banyi ba,ta kawo kanta amma na tsaya, yayi shiru yana son ya tuno wai ma me ta
masa ne?Yasan dai ta shiga rayuwarsa tunda
tasa an masa aure da wuri,sai ya kasa manta
zagin data masa na cewa jahili.Wata zuciyar tace
kada ka manta kaima ka zageta,yayi birgima
akan gado ya koma rufda ciki,sha‘awarta na bin
duk jininsa sai kurum yaji an kwanta a bayansa,ga
zatonsa itace,don haka ya juyo da sauri tare da
rungume ta tsam a kirjinsa,sai yaji muryar chelen tana cewa,oh my prince.Nan ya sassauta mata rikon tare da bude idanu yayi ajiyar zuciya kuma duk sai yaji ransa ya baci,tana kokarin neman
bakinsa ya tsaida ita tare da nuna mata hanyar
waje.tasan wanene prince in ba yayi yana bukatar
a kyalesa,don haka sai kawai ta mike ta fita,haka
ya kwana ranar juyi kawai yakeyi. Bily tana komawa daki kofa ta kulle ta hau gado tana aikin kukan bakin ciki,ta danne xuciyarta ta zubar da ajinta na mace ta kai masa kanta shi kuma ya nuna banza wofi ma ta fita,to daga yau duk abinda zaiyi yaje yayi tayi,ganinta ma bazai kara ba, hakance kuwa ta kasance,domin tun daga ranar Bily ta shiga kulli kurciya tsakaninta da Yarima in yana gidan bata fitowa har sai ya fita,dama tasan shi dan ka‘ida ne,lokutan fitarsa dana dawowa ahaka suka kwashe sati uku bai sata a idanunsa ba,tun baya damuwa har ranar ya zauna ya yini,amma bata fito ba,ya tambayi madam dora tace tana fitowa sometimes ita ko duk ta mika lamuranta ga Allah,daga nafilfili sai addu‘o‘i sai karatun kur‘ani,sai kuma kuka don tunani wani sa‘in gashi yaushe rabon wayarta da kudi bare ma ta kira wani sai dai Mansu tana kiranta.Malam Mamman ya shigo dauke da buhun doya kofar Mamanmu,ya sauke sannan yace Fatima tana daga ciki tace na‘am.Ta fito tana cewa gani Malam,yace ga doya nan ki kasa.Tayi shiru domin duk tsawon xamanta agidannan malam bai taba kawo mata abu wai ta kasa ba,sai dai su Ladiyo su kasa,kuma bata kwasa sai wanda suka kawo mata,wata rana ma tana kallo za‘a kasa din a hanata.yace kinyi shiru Fatima,tace malam kabasu kawai su kasa kaga sune masu yara,yace nine dai maigidan ko?Tace kai ne malam.Yace to nace ki raba muku, Fatima ni tsakanina da Allah yanzun na gane kuskurena,kadaki zata zanci gaba da muzguna miki ne,nidai afuwarki nake nema.Mama tayi dan murmushi,sannan tace dama ni ban rike kaba malam,na sani duk abinda bawa keyi mara kyau dole lokacin nadama zaizo,ko yayi nadamar mara amfani ko kuma yayi ta lokaci bai kure masa ba.Yace nasan dana ke mai hakuri ce Fatima na gode don haka ki kasa kurum nina fita.Tace to sai ka dawo malam,haka ta kasa doyan su masu yara tasa musu kashi bibbiyu ita ko ta dauki daya,har kofar dakin Ladiyo taje tace Ladiyo kuzo ku kwashi doya gata da malam ya kawo ai fa nan suka fito cike da masifa baki nayi duwawu nayi,su za‘ayi ma salo da iyayi?Da itace mai rabawa? Tace malam ne nima yace in raba.Nan sukayi wata shewa,“He!!! Lallai samun sarari tusar asuba,wannan kinibibin na malam ya isa haka don bamu taba nuna masa bacin ranmu akan sauyin halin daya yi mana ba,Karima tace ai kwadayi ne ba wani abu ba,don ‘yarta ta auri dan sarki.Salame ta amshe da cewa,aikin banza da wannan auren ba gara babu ba,daga malam din har ita uwar ‘yar ai ba abasu wata daraja ba,don ko da an basu da yanzun mu gani akasa.Ladiyo tayi shewa,sannan tace fadi ki kara inda za‘a tsare angon da bindiga bazai ce ga surukansa ba.Daidai nan malam ya shigo,yana tsaye suka cigaba da fadin don haka mu yanzu babu wani salon da za‘ayi mana,munsan komai. Karima tace,tallarta fa akayi,matar cushe ko bata kwarjini.Malam yace ai tallar hoton ma hanya ce,haka nan in an tallata wani an siya wani ko kyauta aka bada babu mai amsa,in ma kuna masifa kan doya ne,nine nan nace ta kasa,in bakwa ci ku barta yanzu na dawo cikin hankalina,in ma da kun min asiri ne to ya karye,‘yan bakin ciki,da hassada,ahaka zaku gama rayuwarku a tsiyace,ita ko kuna mata bakin ciki tana kara gaba.Mama ta dubi malam tace yi hakuri malam,jeka abinka.Nan ko ya juya itama ta nufi daki,su ko sun kasa magana don mamaki. Ladiyo tace yau mun shiga uku da makirci,(ta kwaikwayi muryar Mama)tace har da cewa wai yi hakuri malam,kuji makirci.Salame tace eh tana kuma cewa ya tafi ya ko juya.Ladiyo tace yanda na tsani matar nan da in na kashe ta babu hukunci da tuni na daba ma shegiya wuka,amma duk da haka sai nasa an sabautata.Haka dai suka yi ta surutansu ta inda suke shiga bata nan suke fita ba har suka gaji suka bari. Bily tana zaune tana karyawa akitchen,sai taji anata doko sallama, mamaki taji domin ta manta rabonda taji anyi sallama.Da sauri ta fito don tasan ba Yarima bane,ga mamakinta sai taga Magaji.Murna sosai tayi da ganinsa,sannu da hanya kai kadai ne?Yace wallahi ni kadai ne na kawo ziyarar bazata,ina maigidan?Tace yana makaranta,zauna bari na kawo maka abin kari karfe biyu saura,lallai ku ‘yan gayu ne ni dai na karya acikin jirgi sai dai abani na rana mai gishiri.
[2/19, 10:00 AM] ‪+234 803 225 4928‬: 🏵MEKE FARUWA 58 🏵
Chapter 33 · 0% Book details