← Book details Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 60

Sashe 52

Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel · about 4 min read

Da dare sun gama shirin kwanciya tana jikin Yarima son na gefen su sai kawai wayar Yarima ta fara ringing kuma tafi kusa da ita sai ta dauko Wayan kan screen din taga an rubuta T.girl ta mika masa sai ya kasa dauka tun a nan ta gane bashi da gaskiya sai ga call din ya kara shigowa sai ya dake dan kar ta zaci wani abu ya dauka duk da haka tana kwance jikinshi kuma tana jiyo muryar ta kadan kadan tana lura da a darare Yarima ke amsa mata har ya kashe tace kai da wa kake waya ya dake yace abokiyar karatun sa ce tace iya matsayin ta ke nan? Yarima yace ban gane ba tace kasan abunda nake nufi ai ko ita ce wadda ka maye gurbi na da ita da ka tafi sai ya hau fada shi baya son zargi kaza kaza ba dama yayi wata hulda da mace sai kice ina neman ta sai kawai ta tsura mashi ido kawai har ya gama tace masa Yarima da duk abun da kake ba wani damuna yake ba amma yanzu kasan wannan ta canza kuma da baka boye gaskiyarka amma yanzu ka koyi karya ta tashi ta dauki dan ta ta bar masa dakin ya bita da kallo tamkar ya bita sai kuma ya fasa,ransa ya sosu, yace tayi ta tafiyarta mana don taga na damu da ita shiyasa take yi min abinda take so,ya koma yayi kwanciyarsa,duk da bawai yaji dadin kwanciyar tasa bane, kuma yana zargin kansa da cewa shine bai mata adalci ba,ita kuma data kwanta sai ta soma tunanin cewa fushinta ba mafita bane,shin dama fushin tane ya dawo mata dashi kanta?Lallai fa ba fushinta bane,hakurinta ne da kuma addu‘a dole ne taci gaba da hakuri tare da addu‘a,amma bari ta barsa sai da safe ta koma gurinsa. Da safe tayi wankanta tana sanye da riga da siket na blue jeans kanta babu dan kwali ta tufke gashinta da ribbon blue,tana zaune tsakiyar gado tana yiwa son shafa, tafi son ta shirya yaronta da kanta. Yarima ya rasa sukuni dole ya nufo dakin beauty ya iske ta tana kici-kicin saka masa pampers. tsayawa yayi ya harde hannu daga bakin kofa yana kallonsu, cikin tsananin sha‘awa, ajikinta taji da akwai mutum a bakin kofa,da sauri ta juyo tana kallonsa,murmushi ta sake tare da cewa, abban son muna sauri muzo mu kwashi gaisuwa shine ka rigamu zuwa?Ya shigo cikin jin dadin yadda ta tarbe shi,shima gadon ya hau ya zauna kallonta yakeyi sannan yace,ni da kuke fushi dani?Ta dora masa son akan cinya, kafafunsa kuma suna kan gado tana kokarin sa masa wando,tace haba nawa, wazai fushi da aljannarsa?Yasa hannu ya shafi kumatunta,dama matan duniya suyi koyi da kyawawan halayanki na hakuri da saurin yafiya,ga mazajansu,saboda ladabin da kike min yanzun ina jin kunya ki kamani da wani laifi tace ni dama ina jin kishinka bana son ka dinga rabar mata abin yana soya raina,ta zuba masa idanu gami da tagumi ya jawota zuwa jikinsa,insha Allah ba zan kuma ba,kinji?Tace to ka yafe min jiya na barka kai daya amma kasan banyi wani bacci ba,yace na yafe miki beautyna, inda kana gurin kai ko baka san so ba zaka fahimci wadannan suna cikin mayen so amma su basu gane ba.

Ranar da Yarima zai fara halartar asibiti don fara aiki a matsayin babban likitan mata,duk hankalin Bily ya dagu,gani takeyi matan zasu kwace mata miji,ya gama shirinsa tsaf cikin suit,takwas saura kwata ya kalli beauty yace duk wannan damuwar ta mecece?Tace to doctor ba ka fa karya ba zaka fita,ya tura mata kofi zuba min lipton kinsan bazan iya karyawa 8:00 ba,tace to in ten din tayi in kawo maka office?Ya girgiza kai,bance ki fita ba,tace to ni don Allah kada fa ka kalli mata,cikin sigar shagwaba tayi maganar, yace cikin dariya kema kinsan dole na kallesu tunda sana‘ata ce kallon nasu,ina nufin aiki nane duba lafiyarsu, in ta kama ma har taba jikinsu zanyi,t tace daina gaya min abin haushi,ya dubi agogo beauty barni in tafi,kinsan cikin tsarina babu African time 8 nayi alkawarin halattar office kinga saura mintuna,ta dauki jakar muje in raka ka Umma tayi maka addu‘a.yace ta min tun asubahi zan dai musu sallama a tsaitsaye, suka fita tare.goma daidai ta kirasa cikin hanzari ya daga wayar tace yaya aiki nawa?Ya lumshe idanu ya bude,aiki kam gashi nan inayi,kamar ni aikin ke jira,dama kinsan Allah beauty?Yacigaba tunda na zauna kan wannan kujerar marasa lafia suke shigowa ga kuma katunan wasu nan jibge,so ki tayani da addu‘a,tace zanyi amma break fa?Yace babu time tace haba don Allah shikenan nima bazanci komai ba,yace no,no kada kiyi min haka, me son zai sha yau?Tace duk mu hakura har dashi yace,a‘a zanci to nan da sha biyu kinji beautyna. tace zan kira sha biyun dai,ta kashe wayar.

**************************
Haka suke rayuwa mai ban sha‘awa,sai dai a boye Yarima yana amfani da wani cream lokacin saduwarsu wanda a lokacin tarayyarsa da Tina yasan wannan in ya shafa shi yana tsinka spam ba zaiyi da ba sam bata sani ba ta dai gaya daina mata zancan tsarin iyali.
[2/19, 10:08 AM] ‪+234 803 225 4928‬: 🏵MEKE FARUWA 86🏵
Chapter 52 · 0% Book details