← Book details Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 60

Sashe 25

Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel · about 5 min read

A falon suka zauna,Magaji ya dubi kuyangin dake zube gabansu suna dibar gaisuwa yace,ina Gimbiyar take?Asabe tace,tana ciki ranka ya dade.Yace shaida mata isowarmu,tunda taji shigowar matoci ta kasa sukuni,ta mike tsaye tana ta kaiwa-da-komowa, sanye take da doguwar riga mai hade da hula. Asabe ta shigo ranki ya dade ki bani goron albishir,da sauri Bily tace,Mansu ce tazo ko Mamanmu?Asabe tace,ranki ya dade Yarima ne yazo.Ta dafa kirji cike da fargaba,tare da cewa,Yarima?Asabe tace,eh ranki ya dade.Bily ta soma zufa,koma kice ina bacci don bazan ganshi ba.Saroro Asabe tayi,amma dole taje ta fada,jiki babu kwari ta sanar dasu gimbiya tana bacci.Yarima kam ko juyowa baiyi ba,Magaji ko yace,to bari mu jirata.Ya dan saci kallon Yarima don ya fada ne kawai don yaji me Yariman zai ce,nan take kuwa Yarima ya dakawa Asabe tsawa da cewa,ki taso ta mana,ita wacece da har za‘ace tana bacci? Duk Bily tana ji,nan take ta tuno da maganganun da Yarima ya gaggaya mata,don haka Asabe tana shigowa kafin tayi magana,Bily ta fita.Yarima yana zaune ne saitin dakin nata,don haka tana fitowa tayi arba dashi,yayi kyau cikin kayan da ‘yayan sarakuna suka fi sawa,sai hula mai gashi da kuma takalman sarakai.Sam Yarima bai ko kalli inda take ba,duk da yasan ta shigo yayi shiru yaji da wacce zata fara?Amma sai yaji shiru,sai Magaji ne yace,ranki ya dade karaso mana.Yarima ya juyo da nufin yaga wai shin wannan wacece ita?Zumbur ya mike yana nuna Bily da dan yatsa tare da fadin dama kece?Ya kalli Magaji ka gane ta?Bai jira amsa ba ya soma tafa hannunsa sai da yayi tafi so uku sannan ya taka a hankali ya isa gurinta.Ya dubeta sai yanzun na fahimci dama kina da wata manufa akaina,kuma kinyi Achieving shiyasa kika ce kin sanni tun randa kika fara ganina?So kinyi kokari,yanzun dama nazo miki da abu biyu ne,na farko in tayaki murna sannan in miki jaje,daga karshe kuma in baki shawara,to amma tunda kece ina nufin ba wata can da nake zato ba,wadda bata sanni ba aka tilasta ma aurena bace,to abu uku zan miki ke maimakon biyu zan fara jinjina miki sannan in miki murna in kuma miki jaje,sannan in baki shawara sai dai shawarar da zan baki tasha banban da wadda nazo da ita,taki ta dabance.Ya juya mata baya tare da harde hannuwansa a kirji, jinjinar da zan miki kuwa?Ita ce na yaba da kokarinki yanda kika shiga kika fita tun daga kakana Modibbo zuwa mahaifina kika kuma hado da sarkin zazzau kinyi kokari har zuwacin nasararki na aurena.Sannan ina miki murnar samun miji kamar ni,hakika kinyi sa‘ar samun wanda mata ke so,kuma mai burin zama da mace daya rak karin sa‘arki kuwa?Itace gidan sarauta ba‘a saki mutu ka raba matsawar ba kin zo da wata alfasha bayyyananniya ba Sai shawara da farko nazo in ba wadda za‘a aura min shawara ne akan kada ta yarda ta shigo hurumina, wato ta bijire ma aurena kafin zuwan ranar auren. Amma yanzun ke ya juyo ya nunata,bazan baki shawarar karki aureni ba,domin kece kika nema,kuma nima naso hakan don in banbance miki tsakanin aya da tsakuwa,sannan shawara sai kinyi hakuri da zama da karamin yaro kuma bugu da kari yaron jahili da kakkausar murya ya fada.Magaji ya taso yana cewa a‘a Yarima what are you thinking? Yarima ya daga masa hannu don‘t say anything baka san komai ba akan wannan yarinyar.Bily tace,kaini daina ce min yarinya domin ba sa‘arka bace ni,sannan ka daina babatun na shiga nafita don na sameka wallahi kayi kuskure,yanda kake jin an matsa maka haka ma nima har ma gara kai,nida aka tuge ni kan aikina sannan duk zaman da kake bukata na shirya sai ka sani ni ina da ilmi kuma bana fata nabar tafarkin da musulunci ya shinfida min,don haka zan bika in Allah ya sa kai ne mijin nawa(hawaye ya soma zubo mata)sai dai na cutu don ba irin ka naso in aura ba.Ta juya zata tafi Yarima ya fizgota,kinsan zaman da zamuyi?Ya zuba mata manyan idanunsa cikin nata idanun masu tsananin haske da matsakaicin girma,yace ina tambayarki?Tace sai ka fada.Mace mai shekaru da ilimi mijinta karamin yaro jahili,kuma mai tsattsauran ra‘ayi sannan miskili in kin shirya you are welcome ya saketa da karfi ya fita. Magaji ya taso kusa da ita yace kiyi hakuri insha Allah komai zaiyi daidai, murmushin bakin ciki tayi ga hawaye yana zuba ita kam yaya zatayi?Daki ta shiga ta hau gado tana kuka zuciyarta kuwa tana tambayarta sai yaushe zatayi farin ciki?A baki ta furto babu rana,don yanzun zaka shiga sabon babin bakin ciki ne gidan Yarima gashi babu saki MEKE FARUWA dani ne? Lokaci baya jira sai dai ajira sa inji ‘yan magana,wannan haka ne domin yanzun dai saura sati daya bikin Yarima da Bily,gefensu Mamanmu babu zama,duk da ance ba‘a son azo da komai Mamanmu ta dage lallai abada koda daki daya ne don azuba ma maigado kayanta,Mansu kuwa dubu dari ta zube ma Mama tana bada hakuri babu yawa,ban dana Faruk,su Sakina kowa yayi kokari sai dai su Gwaggo Ladiyo su hana kansu sukuni,sunata faman shige-shige ‘yan tsibbu suma sunyi nasu shirin.Gefen ango kuwa sam ba wanda ya zaci baya so,nan ya sake aka shiga shirya yanda biki zai kasance dangi kowa ya kosa.‘Yan kawo lefe gidan Umman Mansu aka saukesu,suna dauke da akwati doxin biyu tare da key din henesy su anty Salma sun raina ma gidan da aka nemo ma Modibbo aure duk da tsarin gidansu Umma Mansu ina to ace gidansu Bilyn ne kila ko zama bazasuyi ba.Sai dai sun dan yaba da tarbar da aka musu,na kayan lashe-lashe da kuma ciye-ciye, sannan tukuicin dubu dari sun ansa a raine don bai wuce kudin shan sweet din yaransu ba,haka suka tafi suna ta surutu.Koda suka je suka gayama Umma,cewa tayi bata son surutu,in ma ba‘a basu tukuicin ba ai ba addini bane.Ana saura kwana uku biki aka dauko Bily,wadda tasha gyara gurin tsohuwar da jakadiya ta tura,ga kuma Mansun ta tazo mata da tata tsarabar,sannan ga mai lalle tare da dilke.Nan fa Bily tayi kyau kamar aljana.Suna sa kai dakin Mamanmu dangin Mama suka kama fadin tubarkalla masha Allah, Allah yanda mutane suke ta cewa kai Bily kece kuwa?Kinyi kyau kaza- kaza,sai kawai ta boye gidansu Mansu,walima kawai suka shirya inda aka sha wa‘azi da kuma nasihohi,bayan daurin aure kenan.
[2/19, 9:58 AM] ‪+234 803 225 4928‬: 🏵MEKE FARUWA 45🏵
Chapter 25 · 0% Book details