← Book details Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 60

Sashe 5

Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilkisu tana tafe amma duk wanda yasan ta in ya ganta yanzu zai fahimci tana cikin damuwa,duk da cewa dama ita ba mai son hayaniya ba ce, ko yawan dariya akan hanya,ta tsaya kofar gidan su mansura tace Sakina shiga kice ma Mansu in ta shirya tazo mu tafi,mun yi latti. Sakina na saka kai Mansura na fitowa,tace "ashe kun iso?Nima naga shiru nace bari naje gidan na gani shin lafiya?Bilkisu ta dan yi tsaki sannan tace, to lafiya,suka soma lafiya mansu tana korin cewa. Gaskiya bily ban yarda lafiya ba,idanunki kamar kin yi kuka.Tace kawai bana jin dadi ne.Ko a islamiya bilkisu babu kwanciyar hankali duk malamin da ya shigo sai ya gane,saboda zazzakar muryarta mai kayata karatun nasu in suna yi yau adusashe take,haka nan kyakkyawar Fuskarta yau kam a daure take tam.Mansu ma duk ta damu suna tashi bata shiga gida ba sai kannanta tace ma ku shiga gida ku ce ma umma zan gaida mamanmu in dawo, Bilkisu ta dubeta mamanmu tana gidan aiki,mansura ta kada kai na sani ina so ne muyi wata magana,suka nufo gidansu bily.
Sai da suka zauna sannan mansura tace wai me yake damunki ne bily? Bilki tace ba komai Mansura. Ta daga mata hannu alamar tayi shiru, ina baza ki fada min ba to in tafi gidanmu kawai bana son dogon labari. Bilkisu tace to ni ban san ta ina zan soma ba, abinne kamar tatsuniya kin gane! Tun ina karama ne muka taba zuwa sallah bauchi,shi kenan kawuna yaje dani kallon hawan sallah, naga dan sarki, shima yayi hawan, dan yaro ne tamkar ni a wancan lokacin shi ne fa tun daga nan kullum ina cikin mafarkinshi har yanzun. Mansura tace ban gane ba? Bilki tace ai ba zaki gane din ba.donni ma da bani ce ke yi ba zan karyata ne. Mansura tace wane irin mafarki ne haka kullum kina mafarkinshi ya kara girma ko yana nan kamar da? Sannan shi ne sanadin bacin ranki yau? Bilki tace, yana girma nasan zaki sha mamaki in na gaya miki tun daga randa na ganshi, nake mafarkinshi har yau din nan ko gyangyadi ne ya dan sace ni sai nayi mafarkin shi,sunan shi Yarima modibbo, yana da kyau kuma dan kwalisa ne komai nashi da ka'idarshi Komai da lokacinshi, misali baya cin abinci a lokacin karatu,kin gane irin abun yana ce min wasan da yake zuwa muna yi lokacin wasan kenan, awa daya da rabi muke yi sai ya tafi, wai baya son shiga lokacin wani abin, kuma shi ma'abocin son girma ne, baya son raini ni fa da shi har fada muke yace ya girme ni, ni kuma in ce karya ne yanzun nan zaki ga yayi fushi ya tafi nesa dani kafin lokacin tafiyar shi yaya. Mansura taja tsaki, ni don Allah ki gaya min damuwar yau. Bilki tace kin cika garaje baza ki gane ba ne hn ban miki dalla-dalla ba. Haka muka taso tare dashi cikin mafarkina shima yanzun js3 zai je, kin gane ai jiya kuma ita ce ranar da nayi mafarki mafi muni kin aji, wai sai na isa gurin da muka saba wasa, yau ma na riga shi zuwa kamar sauran lokutan, sai dai har lokaci yayi nisa bai iso ba, na soma damuwa ga hadari har an soma yayyafi, dan tsumman riga da siket din da ke jikina suka jike dama sun sha jiki sai suka matse min a jiki iska ta shiga kada min shi, ni kadai a filin Allah,

Kamar daga sama sai naji an dafa ni ta baya ina juyowa sai nagaYarima tsaye,yana sanye ne da riga da wando na farin shara-sharan yadin shi ma din duk ya jike,nace zan tafi dubi duk na jike,ya dubi kirjina,don kirgan dangin daya soma nuna yake kallo,nace zan fa tafi fa,in gaya miski mansu sai jina nayi a jikinshi,na soma kai mishi duk ina cewa,bani son iskanci an ce maka ni yar iska ce?Yace ke wawuya ce beauty wani wasa Zan koya miki In dai takaita miki wai sai gani ni da shi muna...Mansura ta rufe mata baki ita kuma ta fashe da kuka,mansu tace shi ne to na damuwa ba a cikin mafarki ba ne?Nace bara fa kiji tashi nayi na ganni cikin jini...Jini? In ji mansura,bilkisu tace eh shiyasa narasa yanda zan yi,kuma na kasa yaya ma mamanmu tsorona daya kada ace ina da ciki mansura tace gaskiya ne kin sani yanzun muje mu samu.Ummarmu tunda ita tana aikin asibiti ne zata sani,da sauri bilki ta mike.Sun same ta tana sallah suma suka yo alwala har zasu tada salla,mansura tace kin mata malam yace,inda jini jikin mutum bazaiyi salla ba Bilkisu tace ai yace jinin haila ni ko wannan ba haila bace bana ma yin wannan, wannan fa kin ji yanda aka yi jinin fa yazo, basu ji shigowar umma ba sai suka ji tana cewa wane irin jini ne? Tsuru-tsuru suka ji tace da ku nake fa, kuka bilki ta soma yayin da mansura ta soma magana cikin in-ina, gaya mata dai. In ji mansura, cikin kuka bilkisu ta shiga bai wa umma labarinta da Yarima har zuwa jiya, a karshen lbrin ta dora da cewa ni tsorona kada ace ina da ciki. Tamkar umma ta kwashe da dariya, amma sai ta boye tace kin san haila ko? Bilkisu tace malamin fikihunmu yana mana bayani amma ban santa ba, umma tace to haila ce ta same ki, batun mafarki kuwa sai dai na kiya ya dan tsoratani, yanda ki kace tun kina karama, Allah yasa ba aljanu bane suka fake da Yariman da ki ka gani? Kin san suma shu'umai ne, amma zan yi batun da mamanku.
Sannan ta dube su tace, yanzu abin da zan ce muku shi ne dake da ki ka balaga da ita din da bata soma ba na sani tana kan hanya, ku kula. ta dai ja musu kunne.ta fita sai gata da part ta nuna mata yanda zata yi amfani da shi, umma ta samu mamanmu sun zanta kan batun mafarkin Bilkisu, mama tace bana zaton maigado tana da aijanu, kinsan in ka kallafa abu a rai dole ne kayi mafarkinshi, tun tana karama da taga dan sarkin garinmu shi kenan bata da zance sai nashi. Umma tace to bilkisu tana da nutsuwa sai dai ki kara ja mata kunne ko in ce nasiha, tunda yanzun ta girma sai da saka ido, dan yau sai Allah. Mamanmu tace Insha Allah komai zai zo da sauki,Allah dai ya shirya mana daukacin ya'yan musulmi.Umma tace.Amin,yau din ce tayi wuya,sai ki ga yarinya ta tashi da hankali da nutsuwa,ki daga ki yi mata tarbiyar kwarai daga baya sai kiga samari ko wasu kawaye sun rusa komai. Mamanmu tace kwarai dole ne mu sanya ido kan ya'yanmu, wadannan irin kawaye ne suke tare dasu,haka nan kar mu yarda da samarin banza.
[2/19, 9:56 AM] ‪+234 803 225 4928‬: 🏵MEKE FARUWA 11🏵

Da wannan hirar suka yi bankwana.Tun daga wannan lokacin take tsoran maza sam bata son wata hulda ta shiga tsakaninta da kowane namiji,balle da mamanmu ta kara nuna mata cewa kar ta yarda da 'yan kananan samarin nana masu bata yara suna kai su suna barowa.Mamanmu tace ki lura don shi da namiji duk abin da yayi ado ne, ke kam mace ce duk in ki ka yarda aka bar miki abin kunya shi kenan rayuwarki ta lalace,koda ba ai miki ciki ba da an kau miki da budurcinki shi kenan,duk mijin da kika aura baki da wata daraja ko mutunci a gunshi in me kawaici ne zai daure ya barki da Allah,in ko mai zafin kishi ko in ce wanda ba zai iya hakurin bane kisha magana gori har yaranki suta so yana miki don haka ki kula. Bilkisu yarinya ce amma akwai zurfin tunani, domin tun daga nan tasa ma kanta da nazari kan maza ana ta ganin maza sun cika son kansu musamman in tayh duba ga mazan gidansu tun daga kan yayun da kannai na mahaifinta tare da shi kanshi mahaifin nata mazan gidansu daidai gwargwado suna samun kudi da irin sana'ar da sukeyi. Amma sam ba sa biyama iyalansu bukatu, ya'yansu babu boko babu islamiyya, sai yawon talla, kusan duk matan gidan su ke ci da kansu da kuma ya'yansu,ba sutura, amma abin da yake bata mamaki yanda su kuma matan ke faman gasar haihuwa tare da fada da kishi mai tsananin a junansu, saboda mijin da bai san darajarsu ba, ita kam ta gode Allah da yasa mama ta kasance uwa agare su don ta tsaya musu da tarbiya da ganin sunyi karatu sun zama yaran kwarai, kuma insha Allah baza su bata kunya ba, sannan su zama rahama gare ta ba kamar yanda yan gida da suke cewa wahala bashi yasa ko cikin mafarkinta yanzun bata sakar ma Yarima fuska sannan ta dage da addu'a kan Allah ya yaye mata mafarkin Yariman nan. Haka nan hasashen umma na cewa, ko Bilkisu tana da aljani ne ya saka mamanmu cikin tunani don haka ta samu mijin Aminiyarta Hajara tai ma malam mudi bayani, shima da ya yi Istihara ya gano bata da aljanin kowa, don haka yace da mamanmu rudin ne kurum irin na mafarki kada ta damu don haka sai ta kwantar da hankalinta.
tare da ci gaba da neman na rufin asirinta gurin Allah

Yau da gobe asarar mai rai in ji yan' magana gashi Bilkisu har an shiga ss1 lokacin tana da shekaru sha shidda, daukacin unguwar Oja da kewayenta labarin kyawun ta ake ita har mamaki take yi idan taga mutane sun shagala da kallonta, farinta irin farin nanne fes jikinta na dauke da lafiyayyar fata me laushi sumul- sumul suma kwance jikin fatar sai ka zata cikin AC take kwana doguwa ce amma ba can ba, dirin jikinta irin mai wahalar samu din nanne danko ta keru, farin da jikin duk na mahaifiyarta ne,
Chapter 5 · 0% Book details