Sashe 15
Mi Ke Faruwa Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanzu zan ba ki wasu addu'a zaki dinga yin su a lokutan sallah da kuma bacci, duk da cewa na lura ke din mai tsayawa ce akan addininta, Allah ya yi miki albarka, tace na gode kwarai, In'sha Allah zan kiyaye, Mansura ko da ta ji labarinn da suka yi da tsohon daga bakin Bily murna ta hau yiwa aminiyarta ta kusa aure, tace da yace mijin da za ki aura dan babban gida ne sai na raya Yarima, Bilkisu ta kalle ta cikin sauri ki ka raya Yarima! Mansura ta ce sosai ma, Bilkisu taja dogon tsaki don Allah ki bar yi min mugun fata,ni fa Yarima nan ba wai ina sonshi ba be, ko cikin mafarkina aboki na dauke shi tunda shekarunmu daya, sannan ma sabonmu cikin mafarki ne tunda dibi wulakancin da yayi min gabanki Mansura ta ce Aa ba zamu shirya ba, ni fa bani da burin Auren yaro karami , Yariman nan fa na girme shi, Allah ya tsare ni da auran karamin yaro ko da Modibbo yace babba ne zan aura ina zaton yana nufin babba mai shekaru, shi ne kuma ya dace dani, Mansura ta ce ba wani ke dai kin cika ra'ayi kuma In'sha Allah shi ne mijin ki, fita Bilkisu tayi har ga Allah cikin ranta ta tsani zancan Yarima. suna cikin shiri sai gombe yau, kuma sai Kaduna, sun gama shiri tana cikin wani Jan yadi mai ratsin baki, tayi kyau sosai Mansura ta ce don Allah kiyi kwalliya ki dan yi shafe shafe zaki yi tamkar balarabiya, tace Aa bana so yar hodannan ta ishe ni tana magana tana fesa turare ta dauki karamin kum tana taje gashin ta zuwa baya farooq suka shigo shi da Yarima da kuma magajin Malam, da saure ta dauke dan kwalinta ta rufe kanta amma duk da haka Yarima ya gani, magajin Malam kam cewa yayi Masha Allah ya dubi Yarima ya mishi rada, kaga hurul inin duniya? Yi yayi tamkar bai ji ba kuma yaki kallon inda take tun da ya kalle ta sau daya, kan kujeru suka zauna Mansura ta gaishe su, suka amsa farooq yace Mansura babu rabon ku kalle hawa yau zamu tafi su kuma yau zasu fara, Mansura ta kalle Bilkisu, Bily ko mu tsaya ne? Ta yatsina fuska, A'a aikina Ku ku tsaya ni kam zani koma bakin aikina Yarima ya saci kallon ta wannan ya kula tana da gadara, shi zata ma gadara? Yaji bata iya ta gaishe shi ba don ma rainin wayo jiya har da nuna tasan shi ? Gashi yanzu ma ko ta gaida su magajin Malam yace ina kwana Malama? Ta dube shi lafiya, ya ya sallah ? Ya ce Alhamdulillah, jin muryarta ta saka magajin Malam rudewa yayin da Yarima yayi tsam da ranshi yana sauraronta, suna hira ne jefi jefi Yarima yace ma farooq mu zamu tafi dama mun zo gaida tsohon nan ne nima gobe ko jibi zan koma in ban zo yau ba maybe ba zan samu zuwa ba farooq yace to kun gaisa ne? Yarima yace kasan shi da mutane, mun zo yana da baki ya dubi magajin Malam duba mana tsohon nan ko bakin sun tafi,
A ran Bilkisu fadi take wannan dan rainin wayo ne,ban da haka mene nashi na Aiken wannan, shi kuma har da zuwa tashi tayi ta fita ta shiga gurin hajiya Fati, ta same ta tana shafa ma yarta mai,yar kyakkyawar yarta mai gashi, ta zauna tare da fadin baby zo nan in shafa miki man, dama gata da son yara. Hajiya tace kuna ta shiri ko? Tace wlh dan ma wannan Yarima ne ko wanene? Ya zo yana jiran Modibbo su gama da baki da yanzun mun dauki hanya, tace Aa Yarima yazo kenan? Tace ina jin shi din ne taci gaba da shafa ma Aisha mai tana sama yarinyar kaya sai ga Yarima ya shigo tare da sallama hajiya tace Aa mutanen wacan kasa yaushe a gari? Yace shekaran jiya nazo, gobe nake tunanin tafiya suka gaisa da yar hira Bilkisu tana jin su ta taje ma Aisha gashin ta sai nan ta dago kai ta dubi hajiya tace, hajiya ina ribbon din ta? Ta jeho mata sai ta dan kalle Yarima cikin sa'a suka hada ido ita ce ta soma kauda kai shi kuma ya mike bari naga dan takwarkwasasshen tsohon nan da ya ki mutuwa, hajiya Fati ta ce lallai haka ma zaka ce? Albarkarshi fa kake ci ya tafi.
Hajiya fati tace Yarima kenan,tsohon nan naka yana matukar ji da kai,kai ko tsiya ka ke mishi,Bilkisu kan ta duk adaure tun jiya tana son sanin wani abu da Yarima,tace shima yana da dangantaka da Dattijon nan ne?Ta dubi Bilkisu baki bude sannan tayi murimushi jikan shi ne kuma shine jika mafi soyuwa agurin shi, kenan suna da dangantaka da farooq? Cewar Bilkisu kanta bata amsa sai ga mansura ta shigo ki zo ga wayarki ta amsa ta fita tana amsa call din sa'adatu sani abokiyar aikinta ce, farooq ya cekuzo mu tafi fa,bilkisu tace to bayan ta gama amsa waya. Yarima zaune gaban kakanshi bayan sun gaisa ya dan mishi tsokana irin ta kaka da jika,sannan yace Aminu ana can ana ta shirmen ko?Ya shafa keyarshi tare da fadin a haba dai muna karatu ne ba shirme ba,yace to yaya batun aure kuma ina fata ka soma shirin yi?Ya dubi tsohon haba wane aure?Ai ba yanzu ba,sai yaushe?Sai na gama karatuna na fara aikina nahuta,yace nan da yaushe kenan? Yarima cikin jin dadi ya gyara zama domin yasan cewa in tsohon ya daure mishi
[2/19, 9:57 AM] +234 803 225 4928: 🏵 MEKE FARUWA 26🏵
In tsohon ya daure mishi gindi ba zai yi ba,to dole ne mai martaba ya hakura, ya soma lissafi, shekara 7 zan yi zuwa 8 yanzu nayi 4 ina cikin na5 , saura 3 da yan watanni, in fara aiki duk dai da komai mu barshi nan da shekara 7 ,lokacin shekaruna sun kai 31 kenan.
In soma neman Auren zuwa yin Auren kila ya kai shekara ko biyu haka in an hada tare kenan, tsohon yayi dan murmushi yace haka ne, to Allah ya taimaka, ya dauko wani Kofi ya juye ruwan zam-zam a ciki, sannan yayi wata addu'a ko nace ya tofa addu'a sannan ya mika mishi,
Yarima ya saka hannu biyu ya karba ya kafa kai ya shanye tare da addu'a nasan zaka zo kafin ka tafi ko? Yace eh to zan zo kila gobe ne fa tafiyar, yace to kayi kokari ka zo din dan zan baka wasu addu'o'i su farooq suka yi sallama suka shiga falon dan yiwa tsohon sallama, kusa da Yarima farooq ya zauna, su Mansura suna gefe Bilkisu a ranta du'a'i take yi Allah yasa kada tsohon yayi maganar matsalar ta a gaban wannan sarkin girman kan, farooq yace mu zamu tafi, tsohon ya ce to Ummarul Faruku, Allah yashi albarka, kawun ka ya yi min bayanin tsaraba, Allah ya kara budi mun gode da zumunci, to Ku tashi na sallame Ku har kai Aminu, ya nuna Bilkisu ke kuma jikata bari in dan ganki.
Ya dubi Dady dan zo nan, dady yaje gunsa ya shafa kansa Allah ya yi maka albarka, Mansura ta ce mun tafi sai wata rana, ya ce to ki kula da zumunci kada ki biye wa mijinki, suka yi dariya tare da mikewa, Yarima kam dama ranman gim kuma ya riga su fita, bayan duk sun fita ya dubi Bilkisu zaki samu dawo wa nan kusa? Tayi shiru sannan ta ce matsala ta yana yin aikina, amma da na samu dan Hutu zan zo, yace shi kenan amma ki rike addu'o'in nan da kyau, tace na gode, Ya ce zan ci gaba da addu'a nima a nan, tashi kije Allah ya yi miki albarka, ta tashi tana godiya suna sallama da Yarima Bilkisu ta fito, ya bita da kallo a ranshi yana tunanin shin KO dai yar uwarsu CE?
Menene hadin ta da. Kakanshi? Ya dan kalle ta yana jin mamakin kyan da cikar halittarta yake yi sai dai kuma kauyanci irin na matan arewa ya hanata ta nuna kyaunta, ya shiga motar bayan shima ya yi sallama da farooq.
Mansura duk murna ta cika ta son surukarta ya kara shigarta, haka nan Bilkisu ji take tamkar mahaifiyarta CE,ta zayyane mata yanda suka yi da tsohon, itama taji dadin jin hakan ta kuma yi fatan alkairi taso su biya gurin Umman Mamanmu amma suna sauri ne jiya da suka je Bauchi, zariya suka tsaya Mamanmu tasha murana jin batun da tazo dashi washe gari da sassafe suka nufi Kaduna ta koma bakin aikinta.
Yarima yana kwance a dakin shi can malesia, ya rasa dalilin da yasa zuciyar shi ta cika da son ya tuno inda ya san yarinyar wadda zuciyar tashi ta mata lakabi da beauty, amma ya kasa, ya sani bashi da saurin mantuwa da sun taba haduwa kyanta ba mai saurin gushewa a rai ba ne da zai tuna, wata zuciyar tace meyasa ka damu kanka da tunanin inda kasan wannan yar kauyen? Tsaki yaja sannan ya mike yana ayyanawa a zuciyar shi, cewa cikin lokutan da ya tsara bai cire na tunanin kowa ba,saboda bai ga macen da ta isa ya tsaya tunaninta ba, can haka ya tashi ya nufi kicin don kora wani abin mai dan sanyi.
Dattijon ya maida hankali ne kan rokon Ubangiji ya karkato hankalin jikanshi ga aure, duk addu'o'in da ya yi mishi cikin ruwa da wadanda zai dinga karanta wa duk saboda hakan ne.